A+ R A-
29 February 2020

Allah Ya Yi Wa Ayatullah Hashimi Rafsanjani Rasuwa

Da yammacin yau Lahadi (8-01-2017) ne Allah ya yi shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci ta Iran Ayatullah Akbar Hashimi Rafsanjani rasuwa.

Ayatullah Rafsanjani ya rasu ne a wani asibiti da ke nan birnin Tehran a yammacin yau lahadi, sakamakon matsalar zuciya.

Sheikh Rafsanjani ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yi gwagwarmayar kafa juyin juya halin Musulunci a Iran a karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini, haka nan kuma ya fuskanci azabtarwa a gidan kurkukun sarki Shah.

Bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979 a kasar Iran, Sheikh Rafsanjani ya rike mukamai da dama, daga ciki kuwa har mukamin shugaban kasa, shugaban majalisar dokoki ta kasa, shugaban majalisar kwararru masu zaben jagora, ya kuma rasu yana rike da mukamin shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci.