A+ R A-
25 May 2020

Dakarun Yemen Sun kai Hare-Haren Mayar Da Martani Kan Sansanin Makaman Saudiyya A Najran

Sojojin kasar Yemen, karkashin jagorancin dakarun kungiyar Ansarullah ta ‘yan Houthi, sun kaddamar da wani hari da jirgin sama mara matuki kan wani sansanin adana makamai na kasar Saudiyya da ke filin jirgin saman Najran da ke kudancin kasar a matsayin mayar da martani ga hare-hare wuce gona da iri na baya-bayan nan da sojojin Saudiyyan suka kai kan al’ummar Yemen.

Tashar talabijin din al-Masirah ta ‘yan Houthin ta ba da rahoton cewa an kai harin na yau Talata (21-05-2019) ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuki samfurin Qasef-2K lamarin da yayi sanadiyyar tashin gobara mai girman gaske a filin jirgin saman.

Ko a jiya ma dai, makaman kariyar sararin samaniyyar kasar Yemen din sun sami nasarar harbor wani jirgin sama mara matuki na leken asiri na kasar Saudiyyan a yankin Hais da ke lardin Hudaydah a lokacin da ya shigo yankin da nufin gudanar da ayyukan leken asiri.

Dakarun hadin gwiwan da suke kai hare-hare kasar ta Yemen karkashin jagorancin kasar Saudiyya sun tabbatar da kai harin na yau.

A wata sanarwa da Kamfanin dillancin labaran SPA na kasar Saudiyya ya watsa, kakakin dakarun hadakar Kanar Turki al-Maliki ya bayyana cewar dakarun Houthin sun zamanto babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin, sai dai bai yi Karin bayani dangane da irin hasarar da harin ya haifar musu ba.

Harin na yau dai yana zuwa ne mako guda bayan wani harin da dakaru na Yemen suka kai da jiragen sama marasa matuka kan wasu cibiyoyin man fetur na Saudiyyan lamarin da ya tilasta wa Saudiyya dakatar da ayyukan mai din a wannan waje na wani lokaci.

Dakarun kasar Yemen din dai sun sha alwashin kare kasarsu da kuma al’ummominsu daga hare-haren wuce gona da iri da dakarun hadin gwiwan Saudiyya suke kai wa kasar da suka yi sanadiyyar mutuwar dubun dubatan mutanen kasar tun daga shekara ta 2015 zuwa yau din nan.