A+ R A-
25 May 2020

Kada Kugen Yakin Amurka Kan Iran….Reshe Na Nema Ya Juye Da Mujiya

Cikin ‘yan kwanakin nan, hasashe da bayanan da masana suke ci gaba da yi dangane da irin halin damuwa da rashin tabbas din da gwamnatin Amurka take ciki dangane da rikicin da take kokarin haifarwa tsakaninta da Iran a yankin Gabas ta tsakiya na ci gaba da kara bayyana. Hakan kuwa yana cikin wasu muhimman abubuwa da suka faru ne cikin ‘yan kwanakin nan, da suka hada da: sanarwar da gwamnatin Trump din ta yi na tura karin sojoji 1,500 zuwa yankin Gabas ta tsakiya, kalaman sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo na cewa gwamnatin Trump ba tana nufin sauya gwamnatin Iran ba ne face dai tana kokarin sauya yanayi da salonta ne, kara janye katafaren jirgin ruwan daukar jiragen saman na Abraham Lincoln da nesanta shi daga bakin ruwan Iran da kimanin kilomita 700 da dai sauransu.

Dukkanin wadannan abubuwan a mahangar masanan wasu abubuwa ne da suke nuni da halin rashin tabbas da gwamnatin Amurka take ciki dangane da batun kaddamar da yaki kan Iran.

Babu wanda yake kokwanto dangane da karfin da Amurka take da shi a fagen soji wanda ake ganin ya dara na kowace kasa a duniyar nan, ko kuma karfin da take da shi na lalata wajaje masu yawa a cikin kasar Iran, amma kuma a bangare guda shin Amurka za ta iya shiga yakin da ba ta da tabbacin samun cikakkiyar nasara a cikinta musamman idan aka yi la’akari da halin da kasar take ciki? A bangare guda kuma shin za ta iya jurewa da kuma kare kanta daga makaman Iran wadanda ake ganin za su iya haifar wa Amurkan da gagarumar hasara duk kuwa da irin ci gaban da Amurka take da shi a bangaren makaman kariya? Yakin da ke gudana tsakanin dakarun Yemen da Saudiyya dai babbar alama ce ta cewa makaman kariya na zamani kawai ba su wadatar ba musamman idan aka fuskanci al’ummomin da suka kuduri aniyar kare mutumci da kuma al’ummominsu.

Ko shakka babu irin karfin sojin da Iran take da shi yana daga cikin abubuwan da suka sanya shugaba Trump da mukarrabansa sassauta kalamansu kan Iran. Tabbatattun bayanai sun bayyana cewar:

1. Iran ta mallaki makamai masu linzami na zamani masu cin gajere da kuma dogon zango, masu karfin yin ‘layar zana’ wa na’urorin rada-rada, haka nan kuma masu saurin gaske da ‘saurinsu ya dara sauti’, wadanda kuma suke da karfin kai wa ga gaci. Wasu bayanan kuma sun ce tuni ma Iran din ta ba wa kawayenta da a kasashen Iraki, Labanon da Yemen wani adadi na irin wadannan makamai.

2. Iran ta kera wasu dubun dubatan kananan jiragen ruwan yaki masu saurin gaske wadanda za a iya amfani da su wajen kai hare-haren ‘kunar bakin wake’ kan jiragen ruwan Amurka, bugu da kari kan sabbin makamai masu linzami na cikin ruwa wadanda har ya zuwa yanzu ba a taba amfani da su ba.

3. Dakarun sa kai wadanda suka sami kwarewa ta musamman wajen kai hare-hare musamman kan wajaje da jiragen ruwa ta hanyar nitso (watakila nan gaba za mu yi bayani kan ayyukansu).

Da dama dai sun ganin batun aikawa da dubban sojojin Amurka zuwa yankin Gabas ta tsakiya, a matsayin ‘dabarar rashin dabara’ wanda maimakon hakan ya zamanto abin da zai razana Iraniyawa, hakan ma ya kara musu karfin gwiwa ne. Don kuwa makiya na nesa sun matso kusa, don kuwa za su zamanto abin farautar sojoji, makamai masu linzami da kuma jiragen marasa matukan Iran. Gwargwadon yadda adadin sojojin Amurkan ke karuwa, gwargwadon irin hasarar da za su fuskanta.

Ala kulli halin, har yanzu dai alamu suna nuni da cewa Iran dai ita ce watakila za ta sauya salon gwamnatin Amurka, ba kamar yadda Pompeo din yake fatan gani ba, don kuwa tuni Iran ta sanar da dukkanin masu kokarin shiga tsakani, na bayyane da na boye, cewa ba za ta yi wata tattaunawa da Amurka ba matukar dai ba ta sauya salo da kuma halayenta.