A+ R A-
01 April 2020

Janar Soleimani Da Mataimakin Kwamandan PMU Na Iraki Sun Yi Shahada Sakamakon Harin Amurka

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun tabbatar da shahadar kwamandan dakarun Quds, Janar Qassim Soleimani da mataimakin babban kwamandan dakarun sa kai na kasar Iraƙi, Abu Mahdi al-Muhandis bayan wani hari da Amurka ta kai musu a birnin Bagadaza, babban birnin kasar Iraƙi.

Dakarun kare juyin sun bayyana sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a safiyar yau Juma'a inda suka ce mutane biyun sun yi shahada ne sakamakon harin da Amurka ta kai musu ta hanyar amfani da jiragen yaki.

Ita ma a nata ɓangaren, ƙungiyar dakarun sa kan na Iraƙi da aka fi sani da al-Hashd al-Sha'abi (Popular Mobilization Units PMU), cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewar:

Mataimakin kwamandan PMU, Abu Mahdi al-Muhandis da kuma kwamandan dakarun Quds, Janar Qassem Soleimani sun yi shahada sakamakon harin da Amurka ta kai wa motar da take ɗauke da su a hanyarsu ta zuwa filin jirgin saman Baghdad.

Ma'aikatar tsaron Amurkan Pentagon ta tabbatar da kai wannan harin suna masu cewa shugaban Amurka Donald Trump ne ya ba da urmunin kai wannan harin.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da mayar da martani kan wannan ɗanyen aikin, inda da dama suke ganin Amurka ta yi kuskure da kuma sanya kanta cikin matsanancin hali don kuwa ko shakka babu Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmaya za su ɗau fansar wannan kisan gillan.

A cikin wani sakon ta'aziyyar shahadar Janar Soleimanin, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatulllah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar ko shakka babu waɗanda suka aikata wannan aika-aikan su zauna cikin shirin fuskantar mayar da martani a kuma ɗaukar fansa mai tsanani da kaushin gaske.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook