A+ R A-
01 April 2020

Majalisar Ƙoli Ta Tsaron Ƙasar Iran: Ko Shakka Babu Za'a Dau Fansar Jinin Janar Sulaimani A Kan Amurka

Ɗazu ɗazun nan ne majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar Iran ta fitar da wata sanarwa bayan wani taron gaggawa da ta gudanar ƙarƙashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei don tattaunawa da kuma dubi cikin batun shahadar Laftanar Janar Qasim Sulaimani, kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) wanda yayi shahada a yau ɗin biyo bayan harin da Amurka ta kai masa a ƙasar Iraƙi da kuma matakan da ya kamata a ɗauka don ɗaukar fansa.

Ga kaɗan daga cikin muhimman abubuwan da suka zo cikin sanarwar:

1). Wajibi ne Amurka ta san cewa ta tafka gagarumin kuskure ta hanyar kashe Janar Sulaimani, kuma ba za ta taɓa tsira daga wannan kuskuren cikin sauƙi ba.

2). An ɗau dukkanin matakan da suka dace (wajen ɗaukar fansa) sannan kuma nauyin dukkanin abin da zai biyo baya yana wuyan Amurka ne.

3). Ko shakka babu za a ɗau fansa mai tsanani a kan waɗanda suka aikata wannan aika-aika a lokaci da kuma wajen da ya dace.

4). Ko shakka babu tafarkin jihadi da gwagwarmaya za su ci gaba, sannan kuma bishiyar gwagwarmaya za ta ci gaba da kafuwa da kuma ƙara ƙarfi.

5). Cakuɗuwar jinin jagororin Iran da Iraƙi a wannan tafarki na gwagwarmaya za ta zamanto wata hanya ta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin waɗannan al'ummomi biyu a nan gaba.

 

Abin Lura:

a). Yadda Jagora Imam Khamenei ya jagoranci wannan zaman wanda ke nuni da tsananin muhimmancin da wannan lamari yake da shi da kuma cewa duk wani mataki da za a ɗauka a wajen wani mataki ne mai muhimmancin gaske, don kuwa ba kasafai Jagora ɗin yake halartar irin wannan taro na majalisar ba.

b). Iran ta riga da ta ɗau matsaya kan wannan lamarin wanda shi ne ko shakka babu za a mayar da martani da kuma ɗaukar fansa jinin Janar Sulaimani a kan Amurka, lokaci da kuma wajen da za ta aiwatar da hakan kuwa ita ce za ta zaɓa.