A+ R A-
01 April 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Nada Wanda Zai Gaji Janar Qasim Sulaimani

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, Jagoran juyin halin Musulunci na Iran ya nada Birgediya Janar Ismail Gha'ani a matsayin kwamandan dakarun Quds na kasar don maye gurbin tsohon kwamandan dakarun Laftanar Janar Qassim Soleimani wanda yayi shahada a yau sakamakon harin da Amurka ta kai masa.

Kafin hakan dai Janar Ghaani ya kasance shi ne mataimakin Janar Qassim Soleimanin.

Jagoran ya kirayi sabon kwamandan da ya ci gaba da aikin da shahid Qassim Soleimani ya sa a gaba.

Masanan suna ganin irin wannan gaggawa da Jagoran yayi wajen nada sabon kwvamandan yana nuni ne da kudurin da Iran ta dauka na daukar fansar jinin Janar Soleimanin kamar yadda Jagoran yayi alkawari.

A safiyar yau Juma'a ne dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun tabbatar da shahadar kwamandan dakarun Quds, Janar Qassim Soleimani da mataimakin babban kwamandan dakarun sa kai na kasar Iraƙi, Abu Mahdi al-Muhandis bayan wani hari da Amurka ta kai musu a birnin Bagadaza, babban birnin kasar Iraƙi.

Dakarun kare juyin sun bayyana sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a safiyar yau Juma'a inda suka ce mutane biyun sun yi shahada ne sakamakon harin da Amurka ta kai musu ta hanyar amfani da jiragen yaki.