A+ R A-
01 April 2020

Janar Salami: Ko Shakka Babu Za Mu Dau Fansar Jinin Shahid Ƙasim Sulaimani

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Manjo Janar Husain Salami ya bayyana cewar shahid Ƙasim Salami ya share hanyar da karshenta zai kai ga nasara ga musulmi da kuma shan kashin ma’abota girman kan duniya, yana mai cewa: Ko shakka babu za mu dau fansar jinin shahid Ƙasim Sulaimani.

Janar Salami ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a gaban miliyoyin al’ummar Kerman da suka taru don jana’izar shahid Janar Ƙasim Sulaimani a garin Kerman, mahaifar Janar Sulaimanin, inda yayin da yake magana kan shahadar Janar Sulaimanin ya bayyana cewar: Ko shakka babu za mu dau fansar jinin shahid Ƙasim Sulaimani.

Babban kwamandan dakarun na IRGC ya bayyana kisan gillan da Amurka ta yi wa Janar Sulaimani a matsayin daya daga cikin mafiya girman ayyukan ta’addanci da aka gudanar a tarihin dan’adam, yana mai bayyana shahid Sulaimani a matsayin wanda ya shirya da kuma jagorantar shan kashin da Amurka ta fuskanta a yankin Gabas ta tsakiya.

Janar Sulaimani ya ci gaba da cewa Shahid Sulaimani shi ne mutum da ya sake raya yunkurin neman ‘yanci na al’ummar Palastinu, kamar yadda kuma shi ne ya kawo karshen makirce-makircen da ake kulla wa duniyar musulmi.

Yayin da yake magana kan batun daukar fansar jinin Shahid Ƙasim Sulaimani da kuma mayar da martani ga barazanar da shugaban Amurka, Trump, yake yi na kawo hari kan wasu wajaje a Iran, Janar Salami ya ce dakarun Iran za su ruguza dukkanin wajajen da Amurka take so da kauna. Janar Salami ya ci gaba da cewa: Amurka ta san ma’anar wannan maganar, sannan kuma babu wani waje a duniyar nan da zai zamanto mai aminci ga Amurkawa.

Janar Salami ya ce: Muna da tsayayyiyar irada. Don haka za mu ruguza duk wani wajen da Amurka take so kuma take ci gaba da kare shi, sannan kuma ta san me muke fadi.

Babban kwamandan dakarun na IRGC ya ci gaba da cewa: Shahadar Sulaimani dai ita ce mafarin karshen kasantuwar Amurka a wannan yankin.