A+ R A-
01 April 2020

Majalisar Iran Ta Ware Euro Miliyan 200 Don Goyon Bayan Ayyukan Rundunar Ƙudus

Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran, Dakta Ali Larijani, ya sanar da cewa majalisar ta amince da ware euro miliyan 200 daga asusun ajiya na ci gaban kasa don goyon bayan ayyukan rundunar Kudus a matsayin mayar da aniya ga shirin cutar da rundunar da Amurka ta shigo da shi.

A safiyar yau Talata 907/01/2020 ce Dakta Larijani ya sanar da hakan a wani jawabin da ya gabatar a zaman majalisar ta gudanar don tattauna batun daukar matsayar fuskantar makircin cutar da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin da Amurka ta kirkiro bayan ta sanya dakarun cikin kungiyar ta’addanci.

Yayin da yake bayanin cewa dukkanin al’ummar Iran suna goyon bayan tafarkin gwagwarmaya, Dakta Larijani ya bayyana cewar: Cikin watanni biyun da suka saura na wannan shekarar (shekarar hijira shamsiyya da Iran take amfani da ita), mun ware euro miliyan 200, daga asusun adana na ci gaban kasa don goyon bayan rundunar Ƙudus.

Larijani ya ci gaba da cewa: Wadannan kudaden an ware su ne don goyon bayan rundunar Ƙudus ta dakarun  kare juyin juya halin Musulunci wadanda nauyin aiwatar da ayyukan gwagwarmaya a duk fadin yankin nan yake wuyansu.

Har ila yau Dakta Larijani ya ce: Tuni Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da ware wadannan kudaden da kuma mika su ga rundunar na Ƙudus.

Dakarun na Ƙudus dai sun kasance suna karkashin jagoranci marigayi Shahid Ƙasim Sulaimani ne kafin shahadarsa.