A+ R A-
01 April 2020

Dakarun IRGC Sun Yi Ƙarin Bayani Kan Harin Da Suka Kai Sansanin Sojin Amurka A Iraƙi

Kwamandan dakarun kare sararin samaniyya na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran, Birgeidya Janar Amir Ali Hajizadeh yayi ƙarin bayani dangane da harin da dakarun nasa suka kai sansanin sojin saman Amurka na Ain al-Asad da ke lardin Anbar na ƙasar Iraƙi inda ya tabbatar da cewa adadi mai yawa na sojojin Amurka sun halaka wasu kuma sun sami raunuka.

Birgediya janar Hajjizadeh ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau ɗin nan Alhamis inda yayin da yake ƙarin bayani dangane da harin ɗaukar fansar jinin shahid Janar Ƙasim Sulaimani ya bayyana cewar: Wannan hari da makamai masu linzami kan ɗaya daga cikin mafi muhimmancin sansanin sojin Amurka yayin wannan harin, mafari ne na wasu hare-hare masu girman gaske da za su haɗe dukkanin yankin nan, kuma hakan wani lamari ne da wajibi ne a yi shi.

Yayin da yake magana dangane da hasarar da Amurka ta yi yayin wannan harin da kuma kore ikirarin shugaban Amurka na cewa babu wani sojan Amurka da ya halaka yayin harin, Janar Hajizadeh ya bayyana cewar: Mu dai a yayin wannan harin manufar mu ba ita ce kashe wani ba, duk kuwa da cewa tabbas wani adadi mai yawa sun mutu ko kuma sun sami rauni waɗanda Amurkawan sun kwashe su da jirgin sama ƙirar C-130 (zuwa Jordan daga nan kuma zuwa haramtacciyar ƙasar Isra'ila).

Janar Hajizadeh ya kalubalanci shugaban Amurka, Donald Trump, da idan har da gaske yake yi babu wani sojan Amurka da ya halaka yayin harin to ya bari manema labarai su shiga sansanin da kuma nuna musu dalilan da ke tabbatar da wannan ikirari nasa.

Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa: Amurkawa suna faɗin cewa sun riga da sun kwashe sojojinsu daga sansanin kafin ma a kawo harin, alhali kuwa a lokacin da muka kai harin akwai sojoji kimanin dubu biyu zuwa dubu biyu da ɗari biyar a sansanin. Bayan harin alal aƙalla jiragen sama ƙirar C-130 guda tara ne suka kwashe waɗanda suka sami raunuka zuwa Jordan daga nan zuwa 'Isra'ila', haka nan kuma wasu jiragen sama masu saukar ungulu sun kwashe wasu da suka sami raunukan zuwa wani asibiti da ke kusa da ofishin jakadancin Amurkan da ke Bagadaza.

Kwamandan rundunar kare sararin samaniyar ta Iran ya ci gaba da cewa: "Makamai masu linzami 13 muka harba sansanin sojan, amma kuma muna cikin shirin harba wasu daruruwan makamai masu linzamin a daidai wannan lokacin". Kamar yadda ya ce dakarun nasa suna cikin shirin ci gaba da ruwan makamai masu linzami kan sansanonin Amurka idan da Amurka ta mayar da martani.

Har ila yau Janar Hajizadeh ya ce dukkanin makamai masu linzamin da dakarun IRGC din suka harba sun kai ga inda ake su su kai ba tare da Amurkawan sun iya harbor ko da guda daga cikinsu ba duk kuwa da jiragen leƙen asiri da rada-rada da Amurkawan suke da shi.

A wani bangare na jawabin nasa, Janar Hajizadeh yayi karin haske dangane da wajajen da aka kai musu hari a sansanin sojin na Ain al-Asad yana mai cewa daga wajajen da aka kai musu harinhar da wajajen ajiye jiragen sama marasa matuka da ke sansanin bugu da kari kan asalin helkwata a kuma cibiyoyin da sojojin Amurkan suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu na leƙen asiri da kai hare-hare da sauran su yana mai nuna wasu hotuna da aka dauka daga sama da suke nuni da wadannan wajajen da aka ruguza.

Hari la yau kuma yayi bayanin nasarar da dakarun nasa suka samu wajen katse duk wata alaƙa tsakanin jiragen leƙen asirin Amurka da suke yawo a saman sansanin, a daidai lokacin da aka kai hari, da asalin cibiyarsu da ke Amurka wanda hakan ba ƙaramar nasara ba ce da dakarun na Iran suka samu.

Daga ƙarshe dai Janar Hajizadeh ya kirayi Amurkawan da su ɗau darasi daga wannan harin da aka kai musu yana mai jan kunnensu da cewa duk wani hari da za su kawo wa Iran to kuwa zai fuskanci mai da martani mai kaushin gaske kamar yadda kuma ya ƙalubalanci shugaban Amurkan da ya kawo wata hujja da ke tabbatar da cewa babu wani sojan Amurka da ya halaka yayin wannan harin yana mai bayyana cewar suna da wasu dalilai da hotuna da suke tabbatar da abin da ya faɗi kuma a lokacin da ya dace za su fitar da su.

A jiya ne dai shugaba Amurkan Donald Trump cikin wani jawabi ya bayyana cewar babu wani sojan Amurka da ya mutu a yayin harin da dakarun IRGC din suka kai sansanin sojan na Ain al-Asad lamarin da da dama suka sanya shakku cikin wannan ikirari nasa.