A+ R A-
31 October 2020

Iran Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Ɗan Leƙen Asirin CIA Da MOSSAD Da Ke Tattaro Musu Bayanai Kan Janar Sulaimani

Rahotanni daga Iran sun bayyana cewar a safiyar yau Litinin (20/07/2020) an zartar da hukuncin kisan da aka yanke wa Mahmud Musawi Majd, da aka samu da laifin leƙen asiri da tattaro bayanan sirri na ƙasar  da miƙa su ga ƙungiyoyin leƙen asirin Amurka (CIA) da kuma na Isra’ila (MOSSAD).

A kwanakin baya ne dai ma’aikatar shari’ar ƙasar Iran ta sanar da kama Mahmud Musawi Majd ɗin bisa zargin leƙen asiri sannan bayan shari’ar da aka gudanar kansa, aka yanke masa da hukuncin kisa saboda wannan aikin da yayi. A wancan lokacin dai mahukuntan na Iran sun ce za a zartar da hukuncin da aka yanke masa don ya zama darasi ga masu irin wannan aiki na cin amanar ƙasa.

Rahotanni sun bayyana cewar jami’an tsaron Iran sun gano cewa Mahmud Musawi Majd yana aiki wa wasu ƙungiyoyin leƙen asiri ne bayan da suka gano wayar da ɗaya daga cikin jami’an ƙungiyar CIA da ke Yammacin Asiya ya bugo masa, don haka tun daga lokacin sai aka sa masa ido sosai, inda daga ƙarshe dai aka gano yana da alaƙa ta ƙut da ƙut da ƙungiyar CIA ɗin.

Rahotannin sun bayyana cewar babban aikin da aka ba wa wannan ɗan leƙen asirin shi ne tattaro bayanan sirri kana kuma masu muhimmancin gaske dangane da sansanonin jami’an sojin Iran da suke Siriyan, hanyoyi sadarwar da suke amfani da su, kwamandojin sojin Iran da kuma shige da ficensu a Siriya musamman marigayi Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani da dai sauran bayanai na sirri.

A ranar 23 ga watan Satumban 2018 ne jami’an tsaron Iran suka kama Mahmud Musawi Majd, sannan bayan shari’ar da aka masa a ranar 23 ga watan Augustan 2019 aka yanke masa hukuncin kisa. To sai dai kuma bayan ɗaukaka ƙarar da lauyoyinsa suka yi aka miƙa lamarin ga kotun ƙoli ta ƙasar ta Iran inda bayan sake duba shari’ar ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke masa.

Shi dai wannan ɗan leƙen asiri wanda ɗan asalin ƙasar Iran ne amma kuma yana zaune ne a ƙasar Siriya tare da iyayensa waɗanda tun a shekarun 1970 suka tafi Siriya don ci gaba da harkokin kasuwancin da suke yi. A can Siriyan yayi karatunsa, sannan kuma yana aiki da wasu kamfanonin ƙasar da suke alaƙa da Iran a matsayin mai tarjama tsakanin ɓangarori biyu saboda kwarewar da yake da ita cikin harsunan larabci da Turanci. Bayan barkewar rikicin ƙasar Siriyan ya ci gaba da zama a can duk kuwa da cewa iyayen na sa sun dawo gida Iran.

Kwarewar da yake da ita cikin harsunan Larabci da Turanci bugu da ƙari kan masaniyar da yake da ita kan yankuna daban-daban na Siriyan ya sanya ya sami kusanci da jami’an sojin Iran da suke Siriyan a matsayin masu taimako da kuma ba da shawara ga sojojin Siriya kan faɗa da ta’addanci da ake yi a ƙasar. Duk da cewa shi ɗin nan ba ɗan ƙungiyar IRGC ɗin ba ne amma dai a matsayinsa na mai tarjama ya sami damar shiga ɓangarori masu muhimmanci na ƙasar Siriyan da kuma ayyukan dakarun IRGC ɗin a can.