A+ R A-
08 December 2023

Ƙungiyoyin Kare Haƙƙoƙin Bil'adama Sun Buƙaci Gwamnatin Bahrain Da Ta Dakatar Da Kashe Masu Zanga-Zanga

Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bil'adama guda 16 na ƙasa da ƙasa tare da haɗin gwiwan na ƙasar Bahrain sun buƙaci sarkin ƙasar Bahrain ɗin Sarki Hamad bin Isa Al-Khalifa da soke hukuncin kisan da aka yanke wa wasu 'yan ƙasar su biyu suna masu cewa ba a yi wa mutanen biyu adalci ba yayin shari'ar da aka musu kamar yadda kuma sun fuskanci azabtarwa daga wajen waɗanda suke tsare da su.

Ƙungiyoyin 16 da suka haɗa har da kungiyar Amnesty International sun bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da suka aike wa sarkin na Bahrain inda suka bukace shi da kada ya sanya hannu kan hukuncin kisan da aka yanke wa Husain Moosa, ɗan shekaru 34 da kuma Mohammed Ramadhan, ɗan shekaru 37 da kuma yin duk abin da zai iya wajen ganin ba a zartar da hukuncin kisa a kan mutanen ba.

Jami'an tsaron ƙasar Bahrain sun kama mutane biyun ne a watan Fabrairun 2014 suna masu zarginsu da kai hari kan 'yan sanda da nufin 'aikata aikin ta'addanci' da kuma wani harin bam da aka kai da yayi sanadiyyar mutuwar wani ɗan sanda. Bayan wani lokaci wata kotun laifuffuka ta ƙasar Bahrain ɗin ta yanke wa mutanen biyun hukuncin kisa.

Mutane biyun dai sun ɗaukaka ƙara amma a nan ma dai dukkanin kotunan da aka kai maganar sun tabbatar da wannan hukuncin.

Bayanai ai sun tabbatar da cewa mutane biyun sun fuskanci tsananin azabtarwa ne lamarin da ya sanya su amincewa da laifin da ake zarginsu da shi.

A wata sabuwa kuma wasu 'yan majalisar Tarayyar Turai sun buƙaci sarkin Bahrain ɗin da ya dakatar da hukuncin kisan da aka yanke wa wasu mutane 12 a ƙasar suna masu cewa ba a yi musu adalci ba yayin shari'ar da aka musu bugu da kari kan cewa an azabtar da su ne da tilasta musu yarda da zargin da ake musu.

Tun a shekara ta 2011 ne dai ƙasar Bahrain take fuskantar zanga-zangogin al'ummar ƙasar da suke buƙatar kawar da gwamnatin gidan sarautar Al Khalifa ta ƙasar da kuma kafa gwamnatin demokraɗiyya ta haƙiƙa da za ta ba wa al'ummar ƙasar damar walwala. Tswon wannan lokacin dai gwamnatin Bahrain ta ɗau matsayar girar mikiya a kan masu zanga-zangar lamarin da yayi sanadiyyar kashe wani adadi mai yawa wasu kuma suna tsare.