
An Kai Hari Kan Sansanin Sojin Amurka Da Ke Arewacin Birnin Bagadaza
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Latest
- Hits: 1141

Rahotanni daga ƙasar Iraƙi sun bayyana cewar an kai hari da makamin ‘Katusha’ kan sansanin Al-Taji da ke arewacin birnin Bagadaza, babban birnin ƙasar Iraƙi wanda kuma ya ke ɗauke da sojojin mamayar Amurka.
Rahotannin sun ce kimanin makama ‘Katsuha’ guda uku zuwa huɗu ne aka kai harin da su sai dai ba a tabbatar da irin hasarar da suka haifar wa wajen ba sakamakon tsaron da ke wajen da kuma hana manema labarai shiga wajen.
Cikin ‘yan watannin baya-bayan nan dai sansanonin sojin Amurkan da suke Iraƙi suna fuskantar irin waɗannan hare-hare sakamakon ci gaba da kiraye-kirayen da al’ummar Iraƙin suke yi na ficewar sojojin Amurkan daga ƙasar. Dakarun Amurkan dai suna zargin dakarun sa kai na Al-Hash al-Sha’abi na ƙasar Iraƙin da kai waɗannan hare-hare.
‘Yan majalisar ƙasar Iraƙin dai sun buƙaci gwamnatin ƙasar da ta tsara wani shiri na ficewar sojojin mamayar Amurka daga ƙasar suna masu cewa ba su ga abin da sojoin mamayan Amurka suke tsinana wa tsaron ƙasar Iraƙin ba, in ba da ci gaba da haifar da rashin tsaro a ƙasar.
Кungiyoyin gwagwarmaya da dama a Iraƙin dai sun buƙaci gwamnatin Amurka da ta kwashe sojojin na ta daga ƙasar ko kuma su ci gaba da kai musu hare-hare da tilasta musu ficewa daga ƙasar.