A+ R A-
08 December 2023

Saudiyya Da Кawayenta Sun Sace Gangan Man Кasar Yemen Miliyan 48 – Ministan Man Yemen

Ministan man fetur da albarkatun ƙasar Yemen, Ahmed Dares, ya ce Saudiyya da sojojin haya da ‘yan amshin shatanta sun sace kimanin gangan mai miliyan 48 na ƙasar ta Yemen cikin ‘yan shekarun da suka gabata.

Tashar talabijin ɗin al-Masirah ta ƙasar Yemen ɗin ta naƙalto Ahmed Daress yana cewa cikin shekarar 2018 kawai Saudiyya da ƙawayen na ta sun sace gangan man ƙasar Yemen ɗin miliyan 18 sannan da wasu ganguna miliyan 29.5 a shekara ta 2019.

Ministan ya ci gaba da cewa Saudiyya da ƙawayen nata suna ci gaba da sace dukiyar ƙasar Yemen ɗin alhali al’ummar ƙasar na ci gaba da zama cikin mawuyacin hali na tsanani da rashi sakamakon ci gaba da yaƙi da kuma killace ƙasar da Saudiyyan da ƙawayenta suke ci gaba da yi.

Ministan ya ce kudin man da Saudiyya da ƙawayen na ta suka sace a shekara ta 2018 ɗin ya kai dalar Amurka biliyan 1.25, yana mai cewa akwai wasu ‘yan ƙasar Yemen ɗin da suke haɗa kai da Saudiyyan wajen wannan ɗanyen aikin.

Tun a shekara ta 2015 ne dai Saudiyya da ƙawayenta musamman UAE suka ƙaddamar da yaƙi kan ƙasar Yemen da suna ƙoƙarin dawo da korarren shugaban ƙasar Abd Rabbuh Hadi Mansur kan karagar mulki.