A+ R A-
08 December 2023

Rouhani: Mun Yi Watsi Da Buƙatar Amurka Na Tattaunawa Sama Da Sau 20

Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar tsawon shekaru biyun da suka gabata sau 23 Amurka tana gabatar wa Iran da buƙatar tattaunawa da ita amma aka watsi da wannan buƙatar.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a ranar Litinin 27/07/2020 a wata ganawa da yayi da wasu ƙwararru da masu aiki a ma’aikatar sinadaran man fetur inda ya ce sau 8 Amurkawa suke buƙaci tattaunawa da shi a ziyarar da ya kai Majalisar Ɗinkin Duniya don halartar taron babban zauren majalisar amma ya ƙi amincewa da hakan.

Shugaban na Iran ya ƙara da cewa: Amurkawa sun yi zaton tattalin arzikin Iran zai wargaje gaba ɗaya cikin watanni uku sakamakon takunkumin tattalin arziki mai tsanana da ta sanya wa Iran, sai dai sun yi kuskure. Yana mai cewa a maimakon hakan Iran ta samu ci gaba da fagage daban-daban ciki kuwa har da wannan fage na sinadarorin man fetur da sauransu.

Shugaban na Iran ya ce Iran ba tana ƙiyayya da tatatunawa da Amurka ba ne, face dai abin take ƙiyayya da shi shi ne siyasar Amurka ta neman mulkin mallaka a kan ƙasashe tare da mayar da su ‘yan amshin shata, waɗanda ba su da ‘yanci na siyasa, yana mai cewa Iran ba za ta taɓa amincewa da hakan ba.

Dakta Rouhani ya ci gaba da cewa, kowace alaƙa dole ne ta zama bisa girmama juna tare da amincewa da haƙƙoƙin da kowane ɓangare ya ke da su, kuma ya zama mai ‘yanci a cikin lamuransa na siyasar ƙasarsa.

Ya ce a kan wannan matsaya ce Amurkan ta ƙaƙaba wa Iran takunkumi, bisa zaton cewa za ta miƙa kai, abin da bai faru ba, kuma ba zai taɓa faruwa ba.