A+ R A-
08 December 2023

Кungiyar Hamas Ta Yi Watsi Da Tayin Dala Biliyan 15 Don Ta Kwance Ɗamararta

Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci a Falasɗinu, Hamas, Malam Isma’il Haniya ya bayyana cewar ƙungiyar ta su ta yi watsi da tayin Dala biliyan 15 daga wasu manyan ƙasashe da sharaɗin za ta kwance ɗamarar da take da ita.

Malam Isma’il Haniya ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata jaridar ƙasar Кatar, al-Lusail inda ya ce: “Watanni biyun da suka gabata akwai wasu da suka zo wajen mu, waɗanda mun san wasu manyan ƙasashe ne suka turo su. Sun gabatar mna da gudanar da wasu ayyuka a Gaza da kuɗaɗen aiwatar da su suka kai Dala biliyan 15”.

Malam Haniya ya ci gaba da cewa: Mun ce musu lalle hakan yana da kyau, don kuwa muna son gina filin jirgin sama da tashar jirgin ruwa da sauran ayyukan ci gaban ƙasa a Gaza”.

Sai dai ya ce tayin da aka musu ɗin bisa sharaɗin cewa za su kwance ɗamarar da suke da ita ne da yin watsi da makamansu waɗanda suke amfani da su wajen kare kansu daga wuce gona da irin sahyoniyawa.

Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas ɗin ya ci gaba da cewa: Mun fahimci cewa a madadin waɗannan kuɗaɗen dole ne mu rusa ɓangaren sojin ƙungiyar da mai she ‘yan sanda haka nan kuma mu miƙa makamanmu musamman manyan makamai da kuma makamai masu linzami masu isa zuwa Tel Aviv da gaba da nan da kuma kawo ƙarshen ikon mulkin kai da ake da shi a Gaza”.

Malam Haniyah ya ce waɗannan maƙudan kuɗaɗen za a ba da su ne don cimma manufar shugaban Amurka cikin shirinsa na “Yarjejeniyar Кarni” da ya ƙaddamar a watan Janairun wannan shekara ta 2020 da nufin halalta mamayar Amurka da kuma sake taswirar yankin Gabas ta tsakiya.