A+ R A-
08 December 2023

Kamfanin Twitter Ya Yi Watsi Da Buƙatar Isra’ila Na Cire Saƙonnin Jagora Imam Khamenei

Shugabannin kamfanin sada zumunta na Twitter yayi watsi da buƙatar da ‘Isra’ila’ ta gabatar masa na ya cire ko kuma ya daina wallafa saƙonnin da ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ke wallafawa a shafin, suna masu cewa saƙonnin Jagoran ba su saɓa wa ƙa’idojin kamfanin ba.

Jaridar New York Post ta ba da rahoton cewa a watan Mayun da ya wuce ne ministar dabaru na siyasa na ‘Isra’ilan’ Orit Farkash-Hacohen, cikin wata wasiƙa da ta aike wa shugaban kamfanin Twitter ɗin Jack Dorsey, ta buƙaci kamfanin da ya cire saƙonnin Jagora Imam Khamenei daga shafin nasa saboda a cewarta saƙonnin Jagoran suna ƙumshe da gaba da ƙiyayya ga yahudawa.

Sai dai yayin da ta ke mayar da martini ga buƙatar ‘Isra’ilan’, mataimakiyar shugaban kamfanin Twitter kan harkokin jama’a Sinéad McSweeney ta ce saƙonnin Ayatullah Khamenei ɗin ba su saɓa wa ƙa’idojin kamfanin ba, tana mai cewa jagorori da shugabannin duniya suna amfani da kafar sadarwar ta Twitter wajen maganganu da mayar da martini wa junansu.

Jami’ar cikin wasiƙar da ta aike wa ministar Isra’ilan ta ƙara da cewa: “Saƙonnin da kika yi ishara da su (na Jagoran) ya zuwa yanzu ba su saɓa wa ƙa’idojin mu ba”.

A lokuta da dama dai ofishin Jagora Imam Khamenei ɗin ya kan wallafa wasu kalamai na Jagoran a shafinsa na Twitter da suke bayani dangane da ɗanyen aiki da ayyukan ashsha na ‘Isra’ilan’ a kan Falasɗinawa da sauran al’ummomi da kuma kiran da a kawo ƙarshen ‘Isra’ilan’ a doron ƙasa a matsayinta na haramtacciyar ƙasa lamarin da ya ‘Isra’ilan’ da ‘yan korenta suke ci gaba da nuna rashin jin daɗin su da kuma kiran da aka rufe shafin Jagoran na Twitter.

To sai dai Jagoran a lokuta da dama ya sha faɗin cewa abin nufin da kawar da Isra’ila a doron ƙasa ba shi ne kawar da yahudawa ba, face dai haramtacciyar gwamnati da ƙasar sahyoniyawa da aka kafa ta a ƙasar Falasɗinu.