
Iran Ta Kama Shugaban Wata Кungiyar Ta’addanci Mai Hatsarin Gaske Da Ke Da Helkwata A Amurka
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Latest
- Hits: 2061

Ma’aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da samun gagarumar nasara a kan wata ƙungiyar ta’addanci mai helkwata a Amurka wacce kuma cikin ‘yan shekarun nan ta yi ta ƙoƙari wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci a cikin ƙasar Iran.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar dazu-dazun a yau Asabar (01/08/2020) ta bayyana cewar jami’anta sun sami nasarar kame shugaban ƙungiyar ta’addanci da ake kira da Tondar (Thunder).
Sanarwar ta ƙara da cewa: A halin yanzu dai Jamshid Sharmahd, shugaban ƙungiyar ta’addancin ta ‘Thunder’ wanda yake jagorantar ayyukan ta’addancin da ƙungiyar take yi a cikin ƙasar Iran daga Amurka, a halin yanzu dai yana hannun jami’an tsaron na Iran biyo bayan wasu ayyukan sirri masu sarƙaƙiya da aka gudanar.
Shi dai wannan mutumin shi ya tsara da kuma jagorantar harin ta’addancin da aka kai Husainiyar Sayyid al-Shuhada’ da ke garin Shiraz na ƙasar Iran a shekarar 1387 (2008) inda mutane 14 suka yi shahada kana wasu 215 kuma suka sami raunuka.
A shekarun baya-bayan ma dai ƙungiyar ta’addancin ta Thunder ta shirya aiwatar da wasu hare-haren ta’addanci a cikin Iran da suka haɗa da tarwatsa wata madatsar ruwa a Shiraz, tayar da bam a wajen baje kolin littafa na Tehran da kuma tada bam a haramin marigayi Imam Khumaini (r.a) a lokacin da ake gudanar da wani babban taro, to sai dai ba su sami nasarar aiwatar da koda guda daga cikin waɗannan ayyuka na ta’addanci ba sakamakon ƙwarewa da kuma ayyukan jami’an tsaron na Iran.
Ma’aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta ce a nan gaba za ta yi ƙarin bayani kan wannan lamari na kame shugaban ƙungiyar ta’addanci.