
Ɗaruruwan Mutane Sun Mutu Da Kuma Jikkata Biyo Bayan Fashewar Da Ta Faru A Tashar Bakin Ruwan Beirut
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Latest
- Hits: 1445

Rahotanni daga ƙasar Labanon sun bayyana cewar ɗaruruwan mutane ne suka mutu da kuma samun raunuka sakamakon fashewar wasu sinadarori a babbar tashar ruwan birnin Beirut, babban birnin ƙasar a ranar Talatan nan (04/08/2020).
Rahotannin sun ce fashewar ta faru ne a wani wajen ajiye kayayyaki masu tsanannin fashewa da ke tashar bakin ruwan da suka hada da sinadarin nan na ammonium nitrate da ake amfani da shi wajen yin takin zamani da kuma bama-bamai.
Rahotannin sun ce fashewar, wacce ita ce mafi ƙarfi da girma cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan a birnin na Beirut yayi sanadiyyar ruwa gine-gine da daman gaske da ke wajen da kuma kewayensa kamar yadda aka ce ta haifar da girgizar ƙasa mai ƙarfin 3.5 da aka ji ta har zuwa ƙasar Cyprus da ke kimanin kilomita 200 ta Tekun Meditareniya.
Sanarwar farko-farko dai a aka fitar an ce sama da mutane 100 sun mutu kana wasu sama da 4000 sun sami raunuka, kuma ana sa ran adadin zai ci gaba da ƙaruwa.
Shugaban ƙasar Labanon ɗin Michel Aoun ya nuna tsananin damuwarsa kan yadda za a ajiye irin wannan sinadari mai tsananin fashewa na tsawon lokaci a wajen yana mai buƙatar da a gudanar da bincike don gano musabbabin lamarin. Shi ma a nasa ɓangaren firayi ministan ƙasar Hassan Diab ya buƙaci da a gudanar da binciken gaggawa don gano waɗanda suke da hannu da kuma gazawa cikin wannan lamarin don hukunta su.
Rahotanni dai sun ce a watan Satumban 2013 ne jami’an Kwastan na ƙasar Labanon ɗin suka dakatar da wani jirgin ruwan ƙasar Moldova da ya iso tashar daga ƙasar Georgia a hanyarsa ta zuwa ƙasar Mozambique ɗauke da sinadarin ‘ammonium nitrate’ da aka ce ya kai ton 2,750 kuma tun wancan lokacin ake ajiye da wannan sinadari mai hatsarin gaske a wajen duk kuwa da kiraye-kirayen da hukumar Kwastan ɗin ta yi wa hukumomin da abin ya shafa na a kwashe shi daga wajen.
Кungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon ta bayyana abin da ya farun da cewa babban abin baƙin ciki ne ga ƙasar da kuma al’ummarta, tare da bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin matsalolin da ƙasar take fuskanta a halin yanzu.
Кungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar don taya dukkanin al’ummar Labanon alhinin abin da ya faru, musamamn ma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka jikkata, gami da wadanda suka yi asarori sakamakon hakan.