Hamas ta fidda hotuna na wasu sojojin Isra’ila biyu da ta kama
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Latest
- Hits: 690
Bangaren soje na kungiyar Hamas a yankin Gaza ta kasar Falasdinu, wato dakarun izzuddin Kassam sun nuna hotunan sojojin HKI 2 da suke tsare a hannunsu tun bayan fafatawa ta karshe da suka shiga da sojojin yahudawan.
Majiyar kungiyar Hamsa daga yankin Gaza ta bayyana cewa wadannan sojoji yahudawan suna tsare a hannunsu, kuma karaya ce gwamnatin yahudawan take fadawa mutanensu kan cewa babu wani sojan Isra’ila dake tsare a hannun kungiyar Hamsa.
Kamfanin dillancin labaran ‘Shihab news’ ya bayyana cewa a yau Lahadi ne dakarun izzuddin Kassam suka nuna hotunan “Hadar Guland” da kuma ‘Shaa’ul Oroon sojojin HKI biyu da suke tsare a hannun su a yankin Gaza.
Dakarun sun watsa wannan hoton ne don karyata labaran karya wadanda gwamnatin yahudawan take fadawa sauran yahudawan dangane da wadannan sojojin da suke tsare a yankin Gaza.