A+ R A-
29 February 2020

Ziyarar Babban Hafsan Sojojin Iran Zuwa Siriya Da Sakonnin Dake Cikinta

Ziyarar babban jami’in sojin kasar Iran mai girman matsayi kamar Manjo Janar Muhammad Baqeri, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar zuwa kasar Siriya, hakan yana a matsayin sanarwa ce a hukumance na irin rawar da Iran take takawa kuma za ta ci gaba da takawa a fagen soji a kasar. Don kuwa tun farkon barkewar rikicin kasar Siriyan a 2011, Iran ta takaita ne kawai da tura masu ba da shawara kan harkokin soji zuwa kasar Siriyan don taimakawa sojojin kasar da shawarwari da dabarun yaki, shi din ba a fili haka karara ba. To sai dai bayan da rikici ya ki ci ya ki cinyewa sannan kuma wasu kasashe suka shigo cikin lamarin da aikawa da ‘yan ta’adda daga bangarori daban-daban na duniya, Iran din ta fara aikewa da dakaru da kwamandojinta karkashin jagorancin kwamandan ‘Quds Brigade’ na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Manjo Janar Qasim Sulaimani wanda aka sami nasarori da dama ta hnnunsa musamman a garuruwan Halab da Al-Badiyya.

Rawar da dakarun Iran suke takawa a Siriya ya fara fitowa fili ne da kuma sanar da shi a hukumance bayan da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka fitar da wasu faifan bidiyo na yadda jiragen yaki marasa matukansu suka kai hari kan sansanoni da kuma makaman kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh a yankin Al-Badiyya na kasar Siriyan haka nan da kuma wani yankin na garin Al-Mayadeen, haka da kuma wani faifan bidiyon da ke nuni da dakarun suna gumurzu kai tsaye da ‘yan ta’addan a fagen daga.

Ita ma a nata bangaren kasar Siriyan ta fara fitowa fili da bayyana rawar da dakarun Iran din suke takawa ne, ta bakin shugaban kasar Bashar al-Asad, cikin wani jawabi da yayi a watan Augustan da ya gabata inda ya bayyana cewar: “Iran dai ba ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen taimakonmu tun ranar farko na wannan rikicin ba, yayin da take aiko mana da makamai da sauran kayayyakin yaki ba tare da nuna gazawa ba. Ta aiko da masu ba da shawara kan harkokin soji da kuma kwamandoji da dakarunta don taimaka mana da ba mu shawarwari kan dabarun yaki”.

Da dama daga cikin masana dai suna ganin akwai wani sako cikin wannan sanarwa ta fili da Iran ta yi na kasantuwar sojojin na ta a kasar Siriya.

Ko shakka babu muhimmancin lokacin wannan ziyara ta Janar Baqeri bai gaza muhimmancin ziyarar ita kanta ba don kuwa ta zo ne a daidai lokacin da Amurka take ci gaba da barazanar sanya dakarun kare juyin juya halin Musuluncin, wanda shi kansa Janar Baqerin daya ne daga cikin dakarun kare juyin, cikin kungiyoyin ta’addanci da kuma kara kakaba musu takunkumi. Don haka ne ma wasu masanan suke ganin ziyarar  a matsayin wani sako ne ga Amurkawan kan irin gagarumar rawar da dakarun kare juyin juya halin suke takawa ko kuma za su taka a yankin Gabas ta tsakiyan ko Amurkawan sun so ko ba su so ba.

Haka nan kuma ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da kasashen yankin wato Iran, Iraki, Siriya da kawayensu suke fuskantar wata barazana da kuma makirci wanda da dama suke ganin akwai hannun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila ciki. Wannan barazanar kuwa ita  ce ta rarraba yankin Gabas ta tsakiyan zuwa wasu ‘yan kananan kasashe da za su dinga fada a tsakaninsu. A nan ma ko shakka babu Iran ta kawo karshen wannan makircin a Irakin, sakamakon rawar da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka taka wajen kawo karshen kungiyar Da’esh (ISIS) da kuma kokarin Kurdawan Iraki na ballewa daga kasar Irakin, kamar yadda kuma a bangare guda Iran da Siriya da Turkiyyan bakinsu ya zo guda wajen yin watsi da duk wani kokari na rarraba kasar Siriyan.

Mai yiyuwa wannan ziyarar ta Baqeri tana a matsayin wani kokari na rage kai ruwa ranar da ya kunno kai tsakanin Turkiyya da Siriya ganin cewa a watan Augusntan da ya gabata Janar Baqerin ya kai ziyara Turkiyya don ganawa da manyan jami’an kasar ciki kuwa har da shugaban kasar Rajab Tayyib Erdogan, kana kuma da ziyarar da shugaban Turkiyyan ya kawo Iran a kwanakin baya, inda wasu bayanai suka bayyana cewar shugaban Turkiyyan ya sanar da shirinsa na dakatar da kiyayyar da yake nunawa gwamnatin Siriyan musamman idan aka yi la’akari da cewa a halin yanzu ya daina maganar saukar shugaba Asad daga karagar mulki a matsayin sharadin kawo karshen rikicin Siriyan duk kuwa da cewa har ya zuwa yanzu gwamnatin Siriyan tana ci gaba da nuna dardar dinta dangane da wannan niyya ta Erdogan.

Wani babban sakon da ke cikin wannan ziyarar, a ra’ayin masana din, shi ne ga haramtacciyar kasar Isra’ila musamman biyo bayan ci ga gaba da wuce gona da iri da take yi kan Siriya da bayyana cewar ba za ta taba amincewa da kasantuwar sojojin Iran a kasar Siriya ba, bugu da kari kan ci gaba da matsin lambar da take yi wa kasar Rasha lamba kan batun kasantuwar sojojin Iran da dakarun Hizbullah a Siriyan wanda take ganin hakan a matsayin babbar barazana gare ta.

A saboda haka ana iya cewa ziyarar ta zo ne don tabbatar wa “Isra’ilan” cewa wannan barazana nata dai ihu ne bayan hari musamman idan aka yi la’akari da sabuwar siyasar da sojojin Siriyan suka fitar na cewa za su kai hari kan duk wani jirgin yakin Isra’ilan da ya shigo cikin sararin samaniyyar kasar Labanon wanda hakan shi ne karon farko da sojojin Siriyan suka fara yin hakan; kamar yadda kuma take a matsayin mayar musu da martanin cewa batun matsa wa Rasha lamba shi ma dai ba zai haifar musu da da mai ido ba; duk da cewa da man Rashawan sun bayyana wa Isra’ilawan, ciki kuwa har da firayi minista Benjamin Netanyahu wanda ya kai ziyara Mosko don wannan manufar, cewa Rasha ta shigo kasar Siriya ne don taimakawa kasar a fadar da take yi da ‘yan ta’adda, babu ruwanta da rikicin da ke tsakanin Siriya da ‘Isra’ilan’.

A jumla guda dai sakon dake cikin ziyarar Janar Baqeri shi ne: Iran za ta ci gaba da taimakon kasar Siriya a fadar da take yi da ta’addanci da kuma wuce gona da irin “Isra’ila” kamar yadda kuma barzanar Amurka da “Isra’ila” ba za su hana Iran taka rawar da ya dace da ita a yankin Gabas ta tsakiya ba.