A+ R A-
22 September 2019

Kalaman Yariman Saudiyya Muhammad, Bushara Mai Kyau, Amma Fa

Ana ci gaba da maraba da kalaman Yarima mai jiran gado na Saudiyya Yarima Muhammad bin Salman na cewa: “Zan Kakkabe Tsattsauran Ra’ayin Addini A Saudiyya”. Lalle wannan bushara ce mai kyau da duniya ta jima tana jira, kana kuma yarda ce da maganganun da aka jima ana fadi na cewa Saudiyya din ita ce tushen tsaurin ra’ayi na addini da ke ci gaba da shafa wa musulunci kashin kaji a duniya.

To sai dai a daidai lokacin da a ke maraba da wadannan kalaman, da dama kuma suna ci gaba da sanya alamun tambaya da kuma dari-dari kan lamarin suna masu cewa wai shin da gaske ne wannan maganar ko kuma dai akwai wata manufa ta siyasa ta kashin kai cikinta? Sannan kuma shin wannan matashin Yariman yana da karfin yin hakan ganin irin yadda ‘malamai’ suka fara nuna dari-darinsu kan hakan?

Masu dari-darin dai suna ganin kamar akwai manufa ta siyasa ta kashin kai cikin wadannan kalamai na Yarima mai jiran gado. Suna masu cewa anya kuwa ba wani kokari ne na neman yardar Amurkawa da kawayensu don samun goyon bayansu a kokarin Yarima na darewa karagar mulkin kasar Saudiyya ba tare da wata matsala ba ganin irin kai ruwa ranar da ke faruwa tsakanin ‘ya’yan gidan sarautar Al Saud din?

Ko shakka babu wannan batu dai ba abin da za a kore shi cikin sauki ba ne bisa la’akari da matsin lambar da Saudiyya take fuskanta daga Amurka da sauran kasashen Yammaci saboda irin goyon bayan ayyukan ta’addanci da suke zarginta da shi. A fili yake cewa gwamnatocin Yammacin na fuskatar gagarumin matsin lamba daga wajen al’ummominsu kan wajibcin su taka wa Saudiyya birki kan irin goyon bayan da take ba wa kungiyoyin ta’addanci da suke ci gaba da kai musu hare-hare. Hakan ne ma ya haifar da dokar nan ta JASTA a Amurka saboda zargin da iyalan wadanda harin ta’addancin 9/11 ya ritsa da su suke yi wa Saudiyya da hannu cikin harin. A bangare guda kuma ga batun zargin take hakkokin bil’adama da ake mata da ya sanya hatta MDD sanya ta cikin jerin kasashe masu kashe kananan yara da dai sauransu.

Wadannan abubuwan na daga cikin abubuwan da suka sanya masu wannan ra’ayin sanya kalaman Yarima mai jiran gadon cikin jerin kokari na siyasa da zai ba shi damar darewa karagar mulkin Saudiyya, cikin sauki, wanda shi ne babban burinsa.

Mai yiyuwa ne masu kyakkyawan fata ga Saudiyya da kuma gaskata kalaman Yarima mai jiran gadon su ce wadannan kalamai dai hasashe ne kawai, amma shi dai Yarima da gaske yake yi cikin kalamansa.

To ni a ra’ayi na babu bukatar kace-nace sosai don kuwa kawo karshen tsattsauran ra’ayi a Saudiyya ai wata bushara ce mai kyau kuma fatan da duniya ta jima take da shi don kuwa ko ba komai dai idan aka  samu hakan duniya za ta zauna lafiya. Alal akalla wani kaso mai yawan gaske na ayyukan ta’addancin da ke faruwa a duniya zai ragu, kungiyoyin ta’addanci irin su ISIS, Jabhatun Nusra, Al-Shabab, Abu Sayyaf, Al-Qa’ida, Boko Haram da sauransu za su kawo karshe ko kuma alal akalla za su yi rauni sannan kuma ba za a sake samun bayyanar wasu sabbin irin wadannan kungiyoyi ba. Don kuwa sun rasa babbar mai goyon baya kana kuma tushen yada bakar akidar da ta gina su wacce kuma ita ce tushen ta’addanci da mai da jinin bil’adama ba komai ba, wato akidar wahibiyanci da Saudiyyan ta dau shekaru aru-aru tana yadawa.

Muna Ji, Muna Gani, Muna Kuma Sauraro.