A+ R A-
07 August 2020

Shin Lokacin Tattaunawa Ta Diplomasiyya Tsakanin Iran Da Amurka Ya Zo Karshe?

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sake jaddada matsayar kasar Iran ta kin amincewa da duk wata tattaunawa kan karfin kariya da take da shi. Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da yayi a jiya Laraba (25/10/2017) wajen bikin yaye daliban jami’ar jami’an soji ta Imam Ali (a.s) da ke birnin Tehran inda ya ce: Kamar yadda a baya na sha fadi, a yanzu ma zan sake fadi, karfin kariyar kasar mu ba abu ne da za mu tattauna (da yin sulhu) a kansa ba. Babu wata tattaunawa da za mu yi da makiya kan duk wani abu (wanda yake a matsayin) karfin kariyar kasar mu da kuma duk wani abin da zai lamunce mana hakan”. Daga karshe Jagoran ya ce Iran za ta ci gaba da wannan shiri na ta ba tare da la’akari da maganganun da makiya suke yi ba.

Daga dukkan alamu Ayatullah Khamenei yana mayar da martani ne ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump da kuma ‘yan majalisar kasar wadanda suke barazanar kara kakaba wa Iran takunkumi matukar ba ta kawo karshen makamanta masu linzami, musamman masu cin dogon zango ba.

Wadannan kalamai da suka fito daga bangarorin biyu ne ya sanya wasu suke ganin lokacin tattaunawa ta diplomasiyya tsakanin Iran da Amurka ta zo karshe, ko kuma alal akalla ana iya cewa da wuya ta yiyu karkashin sabuwar siyasar shugaban Amurka Donald Trump wanda yayi bayaninta cikin jawabin da ya yi a ranar 13 ga watan Oktoban nan; wanda a takaice dai take nuni da shirinsa na yin fito na fito da kasar Iran.

Abin tambaya a nan shi ne wani fito na fito din ne Trump yake son yi da Iran? Shin yana da karfin yin fito na fito da Iran kai tsaye a wannan yanki na Gabas ta tsakiya wanda ya sauya ba kamar yadda yake a da ba? Idan ba zai iya yi kai tsaye ba, shin kawayen Amurka da suke yankin za su iya yin fito na fito da Iran a madadin Amurka kuwa?

Alal akalla Iran dai tana ganin Amurka ba ta da irin karfin da take da shi a da a yankin Gabas ta tsakiya. Tana ganin gibin da Amurkan ta haifar a yankin, tuni an riga da an cike shi, don haka Amurkan ba wani abin da za ta iya yi ko kuma hana faruwarsa. A fili yake cewa Amurka ta gaza wajen cimma manufofinta na mamaya a Iraki da Siriya. Ta gaza wajen hana dakarun Iran da kawayenta kai wa ga iyakokin da suke son kai wa a yankin. Ta gaza wajen hana kwato garin Musil na kasar Iraki ko kuma Dayr al-Zawr na kasar Siriya daga hannun ‘yan ta’adda duk kuwa da goyon bayansu da take yi, ta gaza wajen kifar da gwamnatin Bashar al-Asad duk kuwa da kokari babu dare ba rana da ta yi, ta gaza wajen ba da kariya ga ‘Isra’ila’, wacce a fili take fadin irin damuwar da take ciki sakamakon yadda “Iran da kawayenta suke ci gaba da yi mata kawanya”, ta gaza...ta gaza... Ko shakka babu Iran tana da hannu cikin dukkanin wadannan gazawa da Amurka ta fuskanta.

Iran dai tana ganin sakamakon gazawar da Trump ya yi wajen daukar fansa kanta ta kofar yarjejeniyar nukiliya, saboda yadda duniya ta ki amincewa da maganganun gwamnatinsa na cewa Iran tana ci gaba da karen tsaye ga yarjejeniyar, to yanzu kuma ya fito ne ta bangaren makamanta masu linzami musamman masu cin dogon zango. Wato wajibi ne Iran tayi watsi da wannan shiri nata ko kuma a dau mataki kanta.

Iran dai tana ganin wadannan makamai masu linzami wani bangare ne na tsaron kasarta wanda ba za ta taba yin wasa da shi ba; wannan kuwa shi ne abin da Jagora Imam Khamenei ya fadi cikin wannan jawabi nasa. Me hakan yake nufi? Fitowar irin wannan maganar daga bakin Jagoran, a matsayinsa na babban kwamandan dakarun kasar Iran, a bangare guda kuma jagoran addini da siyasa na kasar wanda maganarsa, a fagen siyasar waje da kuma tsaron kasar Iran, ita ce maganar karshe, hakan yana nufin Iran ta yi watsi da wadannan kalamai da barazana na shugaban Amurka da majalisar kasar.

A takaice dai idan har Amurka, ta hanyar wadannan kalamai na Trump da majalisar, ta dau matsayar da babu ja da baya kan Iran ko da kuwa hakan yana nufin kawo karshen yarjejeniyar nukiliyan ne; to ita ma Iran a nata bangaren ta dau matsaya.

A irin wannan yanayi wanda ke nuni da cewa daga dukkan alamu bangarorin biyu sun “sa zare”, mene ne abin yi?

Iran dai tun a baya ta sanar da duniya musamman Turawa wadanda suka sanya hannu da ita kan yarjejeniyar cewa, ita dai za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya matukar za ta kiyaye mata manufarta wadanda a dalilinsu ne ta amince da yarjejeniyar. Don haka matukar suna so yarjejeniyar ta ci gaba da wanzuwa, to dole ne su yi abin da zai tabbatar da ci gaba da wanzuwar ta. A bangare guda kuma ita dai ba ta son yaki, amma fa ba za ta taba yarda a wuce gona da iri a kanta ba.

Da dama daga cikin ‘yan siyasa da jami’an sojin Amurka sun fahimci wannan sakon na Iran, mai yiyuwa shugaba Trump bai fahimci hakan ba ko kuma ya fahimta amma yana son ya ‘gwada sa’a’a kan Iran ko zai iya cimma abin da magabatansa suka gaza cimmawa.

A daidai lokacin da amfani da karfin soji a kan Iran zai yi wahala, abin da ya rage wa Amurkawan shi ne amfani da makami na takunkumi wanda shi ma tarihi ya nuna rashin amfaninsa a kan Iran don kuwa tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, Iran take karkashin takunkumin Amurka da kawayenta; hakan bai hana ta samun irin ci gaba da a halin yanzu ta samu ba wanda shi ne abin da ke tsole wa Amurka da kawayen nata ido.

Don haka dabara dai ta rage wa mai shiga rijiya.

 

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook