A+ R A-
25 May 2020

Me Ya Rage, Bayan Kwace Kashi 95% Na Kasar Siriya Daga Hannun ISIS?

Ko shakka babu yanayi a kasar Siriya ya fara sauyawa bayan da sojojin kasar suka sami nasarar kwato sama da kashi 95% na kasar daga hannun 'yan ta'addan kungiyar ISIS da kuma kawo karshen barazanar kungiyar musamman a Gabashin kasar, da kuma ci gaba da takura kungiyar 'Jabhatun Nusra' a yankin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar, sannan kuma dukkanin karfi ya koma ga hatsari mafi girma, wanda shi ne bakar aniyar 'Isra'ila' wacce ita ce ummul aba'isin din dukkanin sharrin da ke faruwa a yankin.

Masana harkokin tsaro suna ganin irin kara kaimin hare-haren da "Isra'ilan" take kai wa kasar Siriyan cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan, wata alama ce da ke nuni da irin halin damuwa da tsaka mai wuya da take ciki sakamakon irin wadannan nasarori da "Sansanin Gwagwarmaya" yake samu.

A halin yanzu dai 'Isra'ila' ta kasance cikin firgita da kuma tsananin damuwa don kuwa ta kasance a kewaye kuma an rutsa da ita, ta arewa da gabashi, da makamai masu linzami da sojoji kwararru wadanda suka sami dukkanin horon da ake bukata wajen fada da makiyi; wato sojojin Siriya a matakin farko, haka nan da dakarun Hizbullah a mataki na biyu, da kuma Iran da dakarunta da kwararrunta a mataki na uku.

A halin yanzu din dai nesa ta zo kusa. Dukkanin kokarin da 'Isra'ila' (tare da kokarin kawayenta) suka yi wajen nesanta Iran daga 'kan iyakokinta' ya zama aikin baban giwa, don kuwa Iran dai a halin yanzu tana kan iyakan kasar Palastinu da suka mamaye.

Ko shakka babu kasashen Siriya da Labanon za su zama fagen yaki mai zuwa tsakanin bangarori biyu (Isra'ila da kawayenta da Iran da kawayenta) wanda alamu suna nuni da yiyuwar faruwarsa ko wani lokaci musamman idan aka yi la'akari da irin matakan neman tsokana da Amurka da 'Isra'ila' kai har ma da Saudiyya suke dauka kan kungiyar Hizbullah bisa zargin da suke mata da goyon bayan abin da suka kira ta'addanci sannan da kuma maganganun da jami'an Saudiyya suke ci gaba da yi kan kungiyar haka nan kuma da rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar tana zargin gwamnatin Siriya da amfani da iskar gas mai guba a yankin Khan Sheikhun duk kuwa da nuna rashin amincewar da kasar Rasha ta yi da rahoton saboda rashin adalcin da aka nuna da kuma kokarin haifar da yanayi na rikici da dardar a kasar Labanon, wanda babbar alamar hakan itace 'tilasta wa firayi ministan kasar, Sa'ad Hariri yin murabus',

Ba na zaton wadannan 'ihu bayan hari' na Amurka da 'Isra'ila' za su tsoratar da Siriya ko Hizbullah ballantana uwa-uba Iran. Ba zai zama kambamawa ba idan aka ce tun da jimawa wadannan "'yan-ukun" (Iran, Siriya da Hizbullah) sun shirya kansu wajen tinkarar Amurka da kawayenta. Ana iya ganin hakan kuwa idan aka yi la'akari da wani rahoto da wasu kwararru da janar-janar masu ritaya na sojin 'Isra'ilan' da Amurka da Faransa suka shirya suna masu jan kunne dangane da barkewar wani sabon yaki da Hizbullah wacce a halin yanzu ta mallaki karfi da makaman sojin da wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiya ma ba su da shi, baya ga dakarunta da suka ce sin kai sojoji dubu 25 wadanda suke da kwarewa ta musamman.

Ko ma dai mene ne rikicin Siriyan, wanda ya dau shekaru kusan bakwai ana yi, ya kawo karshen tsoron yaki da watakila kasashen Iran da Siriya da Hizbullah suke da shi. A halin yanzu dai dukkanin abin da yakin zai iya haifarwa na hasarorin dukiya da rayuka ba wai kawai zai shafi bangare guda ba ne, Amurka da 'Isra'ilan' ma suna ciki.