A+ R A-
25 May 2020

Yarima Muhammad bn Salman, Sauyi Ko Kuma Neman Mulki

Saudiyya dai ta zamanto tamkar abin da wani dan jarida ya kira da sunan "Kurmar Kasa" wacce ba a jin muryarta, to sai dai a cikin 'yan kwanakin nan, an fara jin muryarta, muryarta cikin ayyukan Yarimanta mai jiran gado Muhammad bn Salman, muryarta cikin kame-kame da binciken da ake yi wa 'ya'yan gidan sarautar kasar da kuma barazanar da take yi wa Iran da kuma ci gaba da kai hare-hare kasar Yemen. Daga dukkan alamu dai 'Saurayin Yariman' ba shi da mafita da yawa a gabansa, ko dai yayi nasara gaba daya ko kuma ya rasa dukkan komai gaba daya. Ko ma dai mene ne abin da yake a fili shi ne cewa Saudiyyan ba za ta zamanto kamar yadda take a baya ba.

Shin abin da a halin yanzu yake faruwa a Saudiyyan share fage ne ga shirin Yariman na kawo gyara ko kuma wasa da hankali ne kawai ko kuma dai tarihi ya ke kokarin maimaita kansa na yadda wasu 'yan siyasar suke wargaza kasarsu kamar yadda 'Sarki' Nero yayi da daular Roma?

Abubuwan da Yariman yake gudanarwa na nuni da cewa yana ci gaba da bude kofofin tattaunawa da wasu bangarori, kokari wajen kawo karshe wasu tsoffin al'adu da Saudiyyan ta ginu a kai, a bangare guda kuma yana ci gaba da kada kugen yaki a nan da can. Yakin cikin gida tare da wasu 'ya'yan gidan sarautar da sunan fada da cin hanci da rashawa, bugu da kari kan 'yan jarida da 'yan kasuwa, kafin nan kuma da manyan malaman addini, haka nan da kuma yakukuwa na waje da sunan hakkin da Saudiyyan take da shi na mayar da martani ga Iran. Saudiyyan dai tana ci gaba da barazanar kaddamar da wasu yakukuwan duk kuwa da cewa ba ta riga da ta kashe wutar wasu yakukuwan da ta kunna ba musamman a kasar Yemen wanda ya shiga shekararsa ta uku kenan ba.

Abin tambayar dai shi ne a tsawon tarihi waye ko kuma wata kasa ce ta taba hura wutar yakukuwa daban-daban a lokaci guda, sannan kuma ta yi nasara a cikinsu gaba daya? Shin ko Saudiyya tana ganin za ta iya zama tilo cikin tarihi da ta yi hakan? Ko shin ta samu wani tabbas ne daga wajen Donald Trump, shugaban Amurka, na cewa zai kai wa Iran hari alhali ya gagara yin nasara a yakin da ya kaddamar kanta ta bangaren yarjejeniyar nukiliya?

Ko shakka babu yanayin Yarima Muhammad bn Salman mai ban mamaki da haifar da kace-nace zai ci gaba da haifar da abubuwan mamaki da kace nace a Saudiyyan kamar dai yadda muke gani a fina-finan sinima.

Kafafen watsa labarai da masana dai suna ci gaba da ba wa abin da ke faruwa a Saudiyya sunaye kala-kala da suka hada da 'fadan neman mulki', gwajin damtse tsakanin 'ya'yan gidan sarauta' da dai sauransu. To sai dai suna da kuma siffar da nake ganin ta fi dacewa da yanayin da ke faruwa a Saudiyya da abubuwan da Yariman yake yi shi ne sunan da sanannen dan wasan kwaikwayon nan na kasar Masar, Ahmad Zaki, ya ba wa yanayin inda siffanta abin da ke faruwa din da "Ciwon Iska".