A+ R A-
25 May 2020

Shin Akwai Alaka Tsakanin Abubuwan Da Ke Faruwa A Labanon Da Saudiyya?

Ko shakka babu daga cikin tambayoyin da suke yawo a yankin Gabas ta tsakiya cikin kwanakin nan shi ne: Shin akwai alaka tsakanin abin da ke faruwa a Labanon da abubuwan da ke faruwa a Saudiyya? Shin akwai alaka tsakanin murabus din Sa'ad Hariri, firayi ministan Labanon da 'dirar mikiyar' da ake yi wa yarimomi, ministoci, janar-janar da 'yan kasuwa a Saudiyya?

Mun san cewa Saudiyyar tana cikin tsaka mai wuya: tattalin arzikin kasar yayi rauni sosai sakamakon faduwar farashin man fetur; yakin Yemen ya zamanto tamkar 'girgizar kasa' ga kasar (Saudiyya); takunkumin da aka sanya wa Qatar ya gagara cimma manufarsa; Iran tana ci gaba da tabbatar da tasirinta a Lebanon, Siriya da Iraki; batun tabbatar da yarima a kan karagar mulki na ci gaba da fuskantar matsaloli; a takaice dai Saudiyyan tana cikin tsaka mai wuya da watakila ba ta taba shiga cikinsa ba tsawon tarihinta na sama da rabin karni.

Har ila yau kuma mun san cewa a baya-bayan nan kasar Amurka ta sanya wa kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon gagarumin takunkumi wanda ke bukatar hadin kai da taimakon gwamnatin kasar wajen aiwatar ta shi. Amurkan ta yi hakan don cimma manufar 'Isra'ila' kan kungiyar. A bangare guda kuma 'Isra'ilan' tana ci gaba da fatan Amurkan za ta kai wa Iran harin soji, to sai dai Amurkan karkashin jagorancin Obama kai hatta ma lokacin wannan Trump din ta ki amincewa da hakan, maimakon hakan gwamnatin Trump din shigo da wasu sabbin siyasa; ta ki yarda ta tabbatar da yarjejeniyar nukiliyan Iran, ta kara sanya wasu sabbin takunkumin ko kara kaimin wasu a kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar (IRGC) da kuma tsarin banki na kasar da dai sauransu. A daya bangaren kuma 'Isra'ilan' ta hanyar kulla alaka ta fili da ta boye da Saudiyyan, a halin yanzu tana fatan Saudiyyan za ta taimaka mata wajen cimma wannan manufa da take da shi kan Hizbullah mai yiyuwa ta hanyar share mata fagen kai hari kan kungiyar a cikin kasar Labanon.

A saboda haka ne wasu suke ganin 'dirar mikiya' da 'kisan gillan' da aka yi wa wasu yarimomi a daren Asabar, ciki kuwa har da korar da aka yi wa daya daga cikin yarimomi kasar, dan tsohon sarkin Abdullah kuma ministan dakarun 'National Guards' na kasar, Yarima Mutaib Bin Abdullah da kuma kamawa da tsare hamshakin attajiri yarima Alwaleed Bin Talal a matsayin wani mataki na bude kofar darewa karagar mulkin kasar ga Yarima Muhammad Bin Salman, saurayi dan shekaru 32 a duniya, don ya gaji mahaifinsa da ke fama da ciwo; wanda hakan yana a matsayin share fagen cimma wannan manufa da muka yi bayani a sama.

To sai dai kuma da dama daga cikin masana suna ganin wannan 'makircin' tamkar sauran 'makirce-makircen' da aka kulla a baya a matsayin wani yanan gizo; babu inda zai je. Maimakon ya kara tabbatar da ikon Yarima Muhammad bn Salman din, kaikayi ne kawai zai koma kan mashekiya.