A+ R A-
25 May 2020

Ali Abdallah Saleh....Karshen Alewa Kasa

Yau dai an wayi gari kasar Yemen ba tare da Ali Abdallah Saleh, mutumin da tsawon shekaru sama da arba’in ya mayar da kansa tamkar shi ne kasar Yemen, kasar da ake mata kirarin cewa: Rungumar zaki shi ya fi sauki a kan shugabancinta. To sai dai duk da cewa wasu suna ganin Ali Abdallah Saleh din ya sami nasarar jagorantar wannan kasar na tsawon lokaci, to amma a halin yanzu dai kan ya fada ‘ramin muguntar’ da ya jima yana hakawa. Allah Ya jikan marigayi Mamman Shata da ke cewa: Kai dai mai gina ramin mugunta, to ka gina daidai kwabrinka, watakila fa kai ka fada, mu gargadi mai gina ramin mugunta.

Tarihin rayuwarsa dai ba komai ba ne face dai ‘jerin gwanon’ kulla hadin gwiwa da wannan da wancan da kuma juya baya ga wannan da wancan bayan hadin gwiwan….Ya hada gwiwa da ‘Mutanen Kudancin Yemen’ daga baya ya yake su….Ya yaki ‘yan Houthi sannan daga baya ya hada kai da su….haka lamarin ya ke dangane da kasar Saudiyya wanda ya kasance mutuminta kafin daga baya alakarsu ta yi tsami, kafin cikin ‘yan kwanakin da suka gabatan nan inda suka sake kulla wata alaka don cimma wata manufa da bangarorin suke da ita: Saudiyya a kokarin da take yi na cutar da ‘yan Houthi da ci gaba da rarraba kan al’ummar Yemen da kuma share mata fagen ficewa daga cikin tsaka mai wuyan da take ciki a kasar Yemen, shi kuma a nasa bangaren don cimma burinsa na dawowa karagar mulki da kuma ci gaba da juya kasar yadda yake so.

To sai dai a wannan karon kan ruwa ya kare masa, yayi kuskuren lissafi. Yayi zaton cewa ‘sabbin abokan nasa na kasashen larabawan Tekun Fasha’ za su iya kai shi ga gaci, bai yi tunanin cewa su ma suna cikin tsaka mai wuyan ba. Haka nan kuma watakila ya dogara ne da tunanin da yake yi na cewa ya samu kan wasu daga cikin dakarun kasar (Yemen) da kuma wasu jagororin kabilun kasar, to sai dai ya mance da irin karfi da tasirin da ‘yan Houthin suke da shi hatta garin Sana’a da yake ganinta a matsayin helkwatarsa.

A takaice dai reshe ya juye da mujiya….

Babu Ali Abdallah Saleh a fage, a bangare guda kuma Saudiyya ta rasa wannan babban dama da ta kirkiro shi ta hanyar kashe biliyoyin daloli da nufin rarraba kan al’ummar Yemen da sayen lamirai.

Daga dukkan alamu wannan ‘fitina’ da Ali Abdallah Saleh ya kirkiro ta kara karfafa matsayin ‘yan Houthi din ne da kara tabbatar da irin tasirin da suke da shi cikin al’ummar kasar. Don kuwa a daidai lokacin da nake wannan rubutu dubun dubatan (in ma ba a ce miliyoyin) al’ummar kasar ne suke kan titunan birnin Sana’a, babban birnin kasar, duk kuwa da ci gaba da hare-haren da jiragen yakin Saudiyya da kawayenta suke kai wa birnin, don amsa kiran da shugaban kungiyar ‘yan Houthin, Abdulmalik Badruddeen al-Houthi yayi musu jiya na su fito don nuna murnarsu da kawo karshen wannan makirci na Saudi-UAE kan al’ummar Yemen da kuma kira zuwa ga hadin kai tsakanin al’ummar kasar, a daidai lokacin da suka yi watsi da kiran da ‘korarren’ shugaban kasar Abd Rab Mansur Hadi yayi na cewa su fito don yin Allah wadai da ‘yan Houthin.