A+ R A-
25 May 2020

Alkiblar Musulmi Ta Farko Kana Waje Na Uku Mafi Tsarki Na Musulmi Na Cikin Hatsari

Donald Trump, shugaban Amurka, ya cika daya daga cikin alkawurran da yayi wa sahyoniyawa yayin yakin neman zabe na mika musu birnin Qudus. A jawabin da yayi a daren jiya ya bayyana birnin Qudus din a matsayin helkwata ko kuma babban birnin 'Isra'ila' yana mai cewa ya ba da umurnin a fara shirin mayar da ofishin jakadancin Amurkan daga birnin Tel Aviv zuwa birnin na Qudus. Da haka dai Trump ya tsallake 'jan layin' da wadanda suka gabace shi, irin su Ronald Reagan da kuma George Bush 'karami', da ake ganin su a matsayin shugabannin Amurka da suka fi mika kai ga 'Isra'ilan', suka gagara tsallakewa.

Me wannan matsaya da Trump ya dauka take nufi? Tana nufin: sauya yanayin Gabas ta tsakiya, yin watsi da shirin zaman lafiya da larabawa suka gabatar, yin watsi da yarjejeniyar Oslo, wanda bisa ita ne aka gina shirin zaman lafiyan, yin watsi da batun kafa 'kasashe biyu' da za su rayu tare da juna (Isra'ila da Palastinu), share fagen ci gaba da gina matsugunan yahudawa a Yammacin Kogin Jordan da birnin Qudus da suke karkashin mamayar sahyoniyawan, share fagen korar larabawa mazauna birnin na Qudus da sauransu.

Wadannan dai su ne abubuwan da suke a fili duk kuwa da kokarin da Trump din yayi cikin jawabin nasa na rage kaifin wasu daga cikin batutuwan da muka yi ishara da su din, amma ko shakka babu dukkanin wadannan wasa ne kawai da jumloli da lafuzza.

To koma mene ne Trump dai ya aikata abin da ya aikata, wanda da man hakan ake tsammani daga wajen 'mutum maras lissafi' irin sa. To amma abin tambaya me ya rage wa su kuma 'al'umma' su yi.

A nan dai akwai abubuwa da dama da za a iya yi:

Jagorori da 'yan siyasar Palastinawa suna iya amfani da 'makami' na diplomasiyya wajen kai karar gwamnatin Amurka kwamitin tsaron MDD da shi kansa babban zauren Majalisar saboda yin kare tsaye da dokokin kasa da kasa. Haka nan gwamnatin cin gashin kan Palastinawa din, a matsayinta na memba mai sanya ido, tana iya kiran zaman kwamitin tsaron MDD na gaggawa da sake tayar da wasu batutuwa da suka shafi rikicinta da 'Isra'ila' irin su batun 'Katangar wariya' da ci gaba da gina matsugunan yahudawa a yankunan Palastinawa da suka mamaye da dai sauransu.

Su kuwa sauran kasashen larabawa, suna da abubuwa masu yawa da za su iya tinkarar wannan matsaya ta Amurka da su, matukar dai har yanzu suna ganin lamarin Palastinu a matsayin lamarinsu, sannan Qudus kuma a matsayin alkiblarsu. Da farko kasashen da suke da alaka da 'Isra'ilan' suna iya janye jami'an diplomasiyyarsu daga can da kuma dakatar da duk wata alaka da ita. Ita kuwa Amurka idan ma har ba za su iya katse alakarsu da ita ba, alal akalla za su iya dakatar da cika mata asusunta da kudadensu na sayen makamai. Idan har ya zama dole sai sun sayi makaman to suna iya sayensu daga wasu bangarorin kamar kasar Rasha ko kuma Tarayyar Turai ko China wadanda alal akalla sun nuna rashin amincewarsu da wannan matsaya ta Trump.

Hmmmmm, wai abin da kamar wuya, gurguwa da auren nesa…..

To idan har akwai shakku cikin wadannan biyun, zabi na uku shi ne rawar da al'ummomi za su iya takawa.

Ko shakka babu akwai bukatar a sake dubi cikin yadda ake fuskantar matsalar Palastinun, hakan kuwa shi ne ta hanyar dogaro da karfin da al'umma take da shi. A nan ina nufin kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa wadanda tun da jimawa su ne dai al'ummar Palastinun suka dogara da su wajen kwato musu hakkokinsu.

To tuni dai kungiyoyi da sansanin gwagwarmaya suka fadi matsayarsu kan wannan lamari:

- Imam Khamenei: Sanar da Qudus a matsayin helkwatar 'Isra'ila', alama ce ta gazawa / al'ummar musulmi za su tinkari hakan da dukkan karfinsu / lalle za a 'yanto Palastinu daga mamayar sahyoniyawa.

- Hamas: Matsayar Trump za ta kunce wa manufofin Amurka kura ne.

- Jihad Islami: Matsayar Trump na a matsayin kada kugen yaki ne.

- Zuwa an jima kuma Hizbullah ta bakin shugabanta Sayyid Nasrallah, za ta fadi nata matsayar duk da cewa kafin nan, Sheikh Na'im Qassim ya ce: Matsayar Trump ya kawo karshen batun kafa kasashe biyu, wajibi ne a karfafa tafarkin gwagwarmaya.

Abin tambaya a nan shi ne: Me hakan yake nufi? To ni dai ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai su wadanda ake maganar da su (Amurka da Sahyoniyawa) sun san inda aka kwana.