A+ R A-
25 May 2020

Hannun Amurka Cikin Fitinar Da Ke Faruwa A Kasar Iran A Halin Yanzu.

Cikin 'yan kwanakin nan wasu garuruwan kasar Iran sun fuskanci jerin gwano na nuna rashin amincewa da matsaloli na tattalin arziki, tsadar kayayyaki da kuma rashin sanya ido sosai da gwamnati take yi kan wasu cibiyoyi na kudi a kasar da mutane suke ganin sun taimaka wajen karuwar wadannan matsaloli; suna masu kiran gwamnatin da ta dau matakan da suka dace.

To sai dai wasu daga cikin wadannan jerin gwanon, wadanda daga dukkan alamu tun da jimawa an  tsara su ne, sun koma wani abu na daban inda wadansu mutane suka fara kai hare-hare da kone-kone kan wasu cibiyoyi  na gwamnati, bankuna da wajaje na al'umma bugu da kari kan rera wasu take na batanci ga juyin juya halin Musulunci da jagororinsa, lamarin da ya sanya a matakin farko ministan cikin gida na Iran din Abdurridha Rahmani Fadhli ya ja kunnen wadannan mutane da cewa gwamnatin ba za ta zuba ido tana kallon wasu 'yan tsiraru suna yin abubuwan da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar al'umma ba. Ministan ya kara da cewa: Irin goyon bayan da haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka da wasu kasashen larabawa na yankin bugu da kari kan farin cikin da suke nunawa kan abin da ke faruwar na nuni da irin hannun da suke ciki cikin wannan lamari.

Jin kadan bayan faruwar wannan lamarin, Kakakin fadar White House ta Amurkan Sarah Sanders, cikin wani sako da ta rubuta a shafinta na Twitter, ta nuna cewa Amurka tana tare da masu tada fitinar tana mai barazanar cewa: Lalle lokacin da Amurka za ta ci gaba da zuba ido kan 'zaluncin da ake yi a Iran' ya zo karshe.

Ita ma Ma'aikatar harkokin wajen Amurka cikin wata kakkausar sanarwa ta sake jaddada tuhumce-tuhumce marasa tushe da shugaban Amurka Donald Trump yake yi wa Iran na cewa babu abin da Iran ta sa a gaba in ban da 'haifar da rikici, zubar da jini da kuma tashin hankali da kuma kiran al'ummomin duniya da su goyi bayan al'ummar Iran a cewarsu.

To sai dai wannan ba shi ne karon farko da Iran ta ke fuskantar irin wannan lamari ba, don haka a fili ta san ina aka dosa. Don kuwa a fili ake iya fahimtar inda Amurkan ta sa gaba musamman idan aka yi la'akari da maganganun Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson cikin wata makala da ya rubuta a jaridar New York Times inda yace: A halin yanzu sun daura aniyar fada da da abin da ya kira 'dukkanin barazanar Iran' ne. Inda ya ci gaba da cewa: "Wani bangare na wannan siyasar ita ce hada kai da aiki tare da kawayenmu na Gabas ta tsakiya, don fada da dukkanin abubuwan da suke haifar da rikici da rashin tabbas a yankin:", wato Iran.

A takaice dai wannan siyasar ita ce aiki kafada da kafada tsakanin Amurka da 'Isra'ila' da Saudiyya da kawayenta wajen haifar da rikici da tashin hankali a Iran ta bangarori biyu: na farko rikici na cikin gida, na biyu kuma rikici a fage na yankin (Gabas ta tsakiya).

To sai dai wannan ba wani sabon abu ba ne, don kuwa tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran a shekarar 1979, Amurka ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen ganin ta kifar da jaririyar gwamnatin Musulunci ta Iran, kama daga irin goyon bayan da ta ba wa Saddam a lokacin kallafaffen yaki na shekaru 8, har zuwa ga nau'oi daban-daban na takunkumi. To sai dai kuma dukkanin wadannan makirce-makirce, cikin taimakon Allah, sun zama aikin baban giwa. Don haka, da yardar Allah, a wannan karon ma Amurka da kawayen nata ba za su ci nasara ba musamman ganin yadda shugaban Amurka, wanda ko shakka babu yana daga cikin mutanen da aka fi ki a duniya, ya sa baki cikin lamarin da bayyanar da goyon bayansa a fili kamar yadda jaridar New York Times ta Amurkan ta rubuta ne cewa: Koma dai yaya al'ummar Iran suke kallon gwamnatinsu, to amma ba za su taba amincewa shugaban Amurka, wanda cikin 'yan kwanakin nan yake ta nuna adawa da duk wani sauki da za su samu a fagen tattalin arziki da kuma shigarsu Amurka ba, ya zamanto shi ne mai magana da yawunsu da kuma tsara musu yadda za su nuna rashin amincewarsu.