A+ R A-
25 May 2020

'Isra'ila' Da Hare-Haren 'Dakarun Gwagwarmayar' Kan Yankin Golan Na Siriya

Haramtacciyar kasar Isra'ila dai tun da jimawa, alal akalla bayan harin sojin da suka kai kan sansanin sojin sama na T-4 da ke garin Homs na kasar Siriya da yayi sanadiyyar shahadar wasu dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran IRGC guda bakwai, take jiran dakon mayar da martani daga Iran, don haka tun daga lokacin sojojinta suke cikin shirin ko ta kwana.

Rahotanni sun ce tsawon makonnin da suka gabatan jiragen yakin 'Isra'ilan' suke ta shawagi ba kyakkyaftawa a yankunan da suke arewacin Palastinu da aka mamaye (Isra'ila), kudancin Labanon da kuma kudu maso gabashin Siriya duk dai da nufin sanya ido da kuma zama cikin shiri.

To sai dai a daidai irin wannan yanayin ne a ranar Alhamis din da ta gabata (10, Mayu,2018) sansanin gwagwarmaya din suka yi musu bazata da kai musu munanan hare-hare.

Abin da aka sanar shi ne cewa sojojin Siriya ne suka kai wadannan hare-hare, ita kuma 'Isra'ila' ta ce Iran ce ta kai mata wadannan hare-hare. Dukkanin maganganun biyu dai ba abu ne da za a iya kore su ba. A takaice dai abin da babu kokwanto cikinsa shi ne cewa dakarun da ake kira da 'dakarun sansanin gwagwarmaya' (Siriya, Iran, Hizbullah) suna nan a Siriyan kuma da wuya a iya kore cewa akwai hadin gwiwa a tsakanin cikin irin wadannan hare-hare da za a kai su daga kasar Siriyan.

Bisa la'akari da takaituwar yankin da aka kaki hari, haka nan da kuma irin kayan aikin leken asiri da tattaro bayanan sirri da 'Isra'ila' ta baza a wajen, kamata yayi a ce ta gano lokaci, waje da kuma irin girma da nau'in harin sojin da za a kai musu, to amma abin da ya faru a ranar Alhamis din yana nuni da cewa 'Isra'ilan' ta gaza wajen gano lokacin harin, wajen da za a kai shi, wajajen da aka yi amfani da su wajen kai harin da kuma shirye-shiryen da aka yi wajen kai harin, wanda hakan ya sanya suka fuskanci irin wannan nau'i na hare-hare da ba su taba tsammaninsa ba.

Wadannan hare-hare dai an kai su ne wasu yankuna masu tsananin muhimmanci na sojojin Isra'ilan. Wasu bayanan suna nuni da cewa an kashe sojoji da dama baya ga wadanda aka raunana yayin harin duk da "Isra'ilan" kamar yadda ta saba ta boye hakikanin hasarar da ta yi.

Ko shakka babu wannan ba karamin gazawa ce a bangaren tattaro bayanan sirri da kuma aikin soji ba ne ga "Isra'ilan" baya ga shan kashi na siyasa, musamman bisa la'akari da irin makudan kudaden da 'Isra'ilan' ta kashe kuma take ci gaba da kashewa a bangaren leken asiri da tattaro bayanan sirri. A bisa cewar tsohon firayi ministan 'Isra'ilan' Ehud Olmert sun kashe dala biliyan 10 tsawon shekaru 15 wajen tabbatar da tsaron garin Haifa. A saboda haka ne da dama suke ganin idan har sun kashe irin wadannan kudaden saboda garin Haifa, to a dabi'ance abin da za su kashe a yankin Golan, saboda tsoron da suke da shi na yiyuwar Siriya da kawayenta za su iya kawo wa wajen hari, zai ninninka na can din. To amma duk da hakan ta gagara gano lokaci da kuma wajen da za a kai mata irin wadannan hare-hare na ranar Alhamis.

A daya bangaren kuma sansanin gwagwarmayar sun sami nasarar boye wajen da daga nan ne aka kai hari haka nan kuma da dakarun da suka kai shi daga idanuwan makiya da kuma kawar da hankulansu ta yadda tsawon sa'oi biyu da aka yi na barin wutan, Isra'ilawan sun gagara cutar da dakarun gwagwarmayar.

A bangaren soji, 'Isra'ila' tana ikirarin cewa ita ce take da sojoji mafi girma da karfi a yankin Gabas ta tsakiya, kamar yadda kuma ta yi ikirarin cewa tsawon wannan lokacin ta yi amfani da jiragen sama samfurin F-15 da F-16 guda 28, to amma duk da hakan ta gagara dakatar da wadannan ruwan rokoki da sauransu da aka yi mata ko kuma ta haifar da wata hasara ta a zo a gani ga dakarun gwagwarmayar.

A daya bangaren kuma rashin tabuka wani abin a zo a gani da na'urorin kariya na 'Isra'ilan' da ake kira da 'Iron Dome', shi ma wani shan kashi da rashin nasara ce daga bangaren sojojin 'Isra'ilan' wanda hakan na kara kore kasuwar wadannan makamai na kariya da 'Isra'ilan' take alfahari da su da kuma kokarin sayar da su ga sauran kasashen duniya.

A bangaren siyasa kuma masana harkokin siyasa suna kirga hakan a matsayin wani rashin nasara a wannan fagen ga 'Isra'ilan'. A koda yaushe Amurka tana fadin cewa tsaron 'Isra'ila' tamkar tsaron Amurka ne, kamar yadda da dama daga cikin gwamnatocin Turai ma suna fadin cewa ba za su taba amincewa da duk wani abin da zai zama barazana ga tsaron 'Isra'ila' ba. Haka nan kuma bisa la'akari da tsohuwar alaka da take tsakanin 'Isra'ilan' da kasar Rasha, dukkanin hakan ya sanya 'Isra'ilan' fatan samun taimako daga wajensu don dakatar da wadannan hare-hare, to amma daga dukkan alamu babu wani taimakon da ta samu face dai kawai 'yan wasu sanarwa nan da can wadanda babu wani abin da za su iya haifarwa.

Rashawa dai sun zabi su yi gum da bakunansu dangane da wannan lamarin. Alhali kuwa kwanaki uku kafin hakan Benjamin Netanyahu, yana kasar Rasha don ganawa da manyan jami'an kasar Rasha ciki kuwa har da shugaba Putin don neman daukin yadda za a tseratar da 'Isra'ilan' daga abin da suka kira 'barazanar da Iran take yi mata'. Wasu majiyoyi sun bayyana cewar a yayin ganawar Netanyahu da Putin, Netanyahun ya bukaci Putin da ya shiga tsakani wajen ganin hana Iran mayar da martani kan 'Isra'ila' ita kuma a nata bangaren 'Isra'ilar' ba za ta sake kai wa dakarun Iran hari a Siriya ba.

Ko shakka babu hakan yana a matsayin wani shan kashi biyu a lokaci guda. Shan kashi na farko shi ne kokarin da Netanyahu yayi a lokacin da ake cikin rikicin da kuma wayar (tarhon) da ya dinga bugawa jami'an kasar Rasha da ma na Turai da Amurka don dai a dakatar da hare-haren amma bai ci nasara ba. Na biyu shi ne wadannan buge-bugen wayan dai ba su haifar masa da wani abu ba.

Masana harkokin tsaro da na soji dai suna ganin abin da ya faru a ranar Alhamis din a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci da ke nuni da irin karfin da bangaren 'yan gwagwarmayar suke da shi wajen tinkarar duk wata barazana ta makiya. A daya bangaren kuma yana nuni da gazawar 'Isra'ilan', wacce duk da tana sane da cewa wannan mayar da martani babu makawa za a kai shi, amma ta gagara yin wani abu wajen kare kanta da sojojinta da suke wajen.

To wannan dai lamari ne da ke nuni da wani abu da babu wanda ya isa yayi kokwanto cikinsa shi ne cewa "Lokacin shan kashin sojojin yankin Gabas ta tsakiya a gaban Isra'ila' ya kawo karshe, kamar yadda kuma lokacin da 'Isra'ila' za ta yi dukkanin abin da ta ga dama ta sha ba tare da an mayar mata da martani ba ya kawo karshe, idan ma har ba mu kara da cewa lokacin da 'bakin haure za su bar yankunan da ba na na su ba' ya karato.