A+ R A-
25 May 2020

Daya Daga Cikin Bala'oin Da Suka Fada Wa Duniyar Musulmi

Daya daga cikin manyan matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta shi ne kokarin samar da halacci ga wani lamari, wanda rashin dacewarsa ya fito fili karara, don kawai a kare matsayi da mutumcin wani ko kuma wasu.

Ba da jimawan nan ba, cikin ‘yan bincike-binciken da nake yi, na karanta wasu bayanai da wasu ‘malamai’ suka yi a matsayin mayar da martani ga kalaman da Dr. Ahmad Gumi yayi kan Annabi (s.a.w.a) da Halifa Umar, inda duk da sun nuna rashin dacewar kalaman na Dr. Gumi wadanda suke a matsayin batanci ne karara ga Annabi (s.a.w.a), to sai dai su ma ta wani bangaren sun fada wannan tarko da Gumin ya fada na ‘kokarin samar da halalci ga wani abu mai muni don kare mutumcin wani ko wasu’.

Abin da ya sa na ce sun fada wannan tarkon shi ne cewa dukkanin wadannan malaman wadanda ta wani bangaren sun yi tarayya da Dr. Gumin cikin akidar wahabiyanci/salafanci sun tabbatar da faruwar wannan lamari na hana Annabi (s.a.w.a) abin da ya bukata don ya rubuta wa al’ummarsa abin da ba za su taba bata bayansa ba, da halifa Umar ya jagoranci yi, to amma sai suka ta kokarin wajen shafa ‘farin fenti’ ga wannan abu mai muni da halifa Umar yayi, suna masu nuna cewa yayi hakan ne saboda irin tausayi da kuma kaunar da yake yi wa Annabi (s.a.w.a) sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi da dai sauransu. Wanda hakan ya sanya nake ganin ta wani bangaren kamar ba su da bambanci da shi Dr. Gumin, sai dai kawai shi ya tsananta da kuma munana kalamai ne su kuma sun dan tausasa amma dai duk mahangar daya ce: halalta abu don kare matsayin wani.

In kuwa ba haka ba ni dai ban ga ta yadda za a wanke wannan mummunan abu da ya faru ba.

Idan ma abin mu yi watsi da abin da ‘yan Shi’a suke fadi na cewa ‘Annabi (s.a.w.a) ya so ne ya rubuta sunan Ali ne a matsayin halifa bayansa, shi ya sa halifa Umar da mukarrabansa suka hana; to amma yaya za mu fassara wannan aiki na halifan wanda har ya fusata Annabi (s.a.w.a) har ya ce musu su tashi su ba shi waje, sannan kuma har hakan ya sanya babban sahabin nan Ibn Abbas (r.a) kuka mai tsanani har ma ya kira wannan lamarin da ‘Musiba ko bala’in Ranar Alhamis’.

Sannan idan da har halifa Umar yayi hakan ne don tausayawa Annabi (s.a.w.a) saboda halin da yake ciki, ashe wa ya fi cancanta ya fahimci hakan, Annabin ko kuma wadannan malamai masu kokarin halalta mummunan abin da ya farun? Ni dai a tunani na Annabin ne ya fi kamata ya fahimci hakan, saboda kuma an shaide shi da hazaka, fahimci da kuma hangen nesa. Sannan kuma yadda aka san shi da karimci da ya gode wa halifa Umar saboda wannan ‘kauna’ da ya nuna masa, amma dai abin da muka gani shi ne fushi mai tsanani da yayi da kuma korarsa da yayi.

Ita dai gaskiya gaskiya ce, kuma bayanta sai bata.