A+ R A-
25 May 2020

Kada Kugen Yakin Trump Kan Iran: Dan Da Ya Hana Uwarsa Barci…..

Alamu dai suna kara tabbatar da cewa kugen yakin da shugaban Amurka Donald Trump ya fara kadawa a kan Iran da wuya ya kai labari, don kuwa a halin yanzu dai da dama daga cikin al’ummomin duniya musamman ma na Gabas ta tsakiya sun daina daukar maganar Trump din da wani muhimmancin gaske musamman in ya zo ga batun yaki kan Iran; hakan kuwa ya biyo bayan abin da ya tabbata masa a fili cewa Iran din da yake kada kugen yaki a kanta ba kanwar lasa ba ce.

A bangare guda Iran, ta bakin da dama daga cikin jami’anta, na addini, na siyasa, ko na soji, duk sun bayyyana cewar lalle su dai ba sa don yaki, amma fa ba wai suna tsoronsa ba ne, kuma a shirye suke su kare kasarsu da dukkan karfinsu. Don haka ne ma tattaro makaman yakin da Trump yayi da jibge su a Tekun Fasha ko da wasa bai razana Iraniyawan ba face ma dai hakan lamari ne da ya hada kansu waje guda wajen goyon bayan shugabanninsu, sabanin abin da ‘makiyan’ suka so, a daidai lokacin da Trump din kuma ya rasa da dama daga cikin ‘kawayensa’ na kasashen Turai wadanda suka bayyana rashin aniyarsu ta shiga cikin wannan yakin sabanin yadda suka yi a baya yayin yakin Afghanistan ko Iraki ko kuma kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh.

Bayanai suna nuni da cewa a halin yanzu dai shi kansa Trump din ba ya son wannan yakin don kuwa a halin yanzu ya fahimci cewa yakin zai janyo masa da kuma gwamnatinsa hasara mai girmar gaske, ta dukiya da kuma rayuka. Mai yiyuwa ‘kawayensa’ na kasashen larabawa su iya daukar nauyin hasarar dukiyar da za a yi din amma ba za su iya cike gibin hasarar rayukan na daga sojojin Amurkan da suke jibge a yankin Gabas ta tsakiyan, kama daga wadanda suke kan ‘Katafaren jirgin ruwa mai daukan jiragen saman nan da aka ajiye cikin teku, ko kuma a sansanonin sojin Amurkan da suke Iraki, Siriya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da dai sauransu, wanda Amurkawa ba za su taba yarda da hakan ba.

Duk da cewa yaki dai dan yaudara ne amma dai daga dukkan alamu Trump ya sha kaye a wannan zangon na share fagen yakin, sakamakon wasu abubuwa masu muhimmanci alal akalla guda uku da aka yi wa kawayensa wadanda suke goya masa baya da karfafa shi wajen fara kada wannan kugen yakin, ba tare da ya iya kare su ko kuma mayar da martani ba duk kuwa da ikirarin da suke yi na cewa sun san Iran tana da hannu cikin wadannan abubuwan:

 

1. Harin da aka kai wa wasu jiragen daukan mai guda hudu na kasar Saudiyya a tashar ruwa na Fujairah na Hadaddiyar Daular Larabawa.

2. Harin da dakarun Houthi na kasar Yemen suka kai cikin Saudiyya da jiragen sama marasa matuka guda bakwai kan matata da kuma bututun mai na Saudiyya da kuma barazanar cewa akwai wasu wajaje da suka kai 300 a cikin Saudiyyan da za su iya kai musu harin.

3. Harba makami mai linzami kan ofishin jakadancin Amurka da ke yankin “Green Zone’ mai tsananin tsaro a birnin Bagadaza na kasar Iraki.

Duk da cewa Iran ta nesanta kanta daga dukkanin wadannan abubuwan, to amma da dama daga cikin masana suna ganin wadannan abubuwan a matsayin wani sako ne daga wajen Iran ko dai kai tsaye ko kuma ta hannun kawayenta na cewa ‘matukar dai ba mu zauna lafiya ba, to ku ma ba za ku zauna lafiya ba, matukar ba ku bar mu mun sayar da man fetur din mu, to ku ma kuwa ba za ku sayar da na ku ba, musamman bisa la’akari da yadda Saudiyya take ci gaba da goyon bayan takunkumin sayar da mai da Amurka ta sanya wa Iran, da kuma cewa za ta iya cike gibin da za a samu a kasuwar mai din, musamman bayan barazanar da Iran ta yi na rufe ‘Mashigar Hormuz’, inda Saudiyya ta fara kokarin karfafa tashar bakin ruwa nan Fujairah don ci gaba da fitar da manta ta wajen.

Ko ma dai mene ne ko shakka babu wadannan abubuwa wani sako ne ga Amurka da kawayenta na kasashen Larabawa musamman Saudiyya cewa ‘dan da ya hana uwarsa barci, to shi ma fa ba zai rumtsa ba’.

A bangare guda kuma wani abin da shugaba Trump din ya so cimmawa ta hanyar wannan barazana tasa ta fatar baki da kuma jibge kayan yaki shi ne razana al’umma Iran da kuma kashe musu gwiwa, wato a takaice dai a samu wani yanayi na zaman dar-dar na cikin gida. To sai dai a wannan karon ma Amurkan ta gagara cimma wannan manufa. Don kuwa wannan barazanar ba abin da ta haifar face kara samun hadin kai tsakanin kungiyoyi da jam’iyyu na siyasa daban-daban na Iran wadanda a baya ma wasu an kai matsayin ba sa ga maciji da juna, amma a halin yanzu bakinsu ya zo daya wajen tsayin daka don kare mutumcin kasarsu. A bangaren al’umma kuma wannan ‘kada kugen yakin’ ya kara sanya su kusantar jami’ai da shugabanninsu da kuma goya musu baya wajen ci gaba da tsayin dakan da suke yi na tinkarar Amurkan, kamar yadda kuma sun kara samun kwanciyar hankali da irin karfin da sojojin kasar suke da shi na kare su daga duk wata barazana ta makiya.

Watakila abin da da dama ba su sani ba shi ne cewa tun ranar farko da tsohon shugaban Amurka, Bush, ya mamaye Iraki, tun daga wancan lokacin Iran da kawayenta suka fara shirin kare kansu daga duk wata barazanar Amurka. Tun a wancan lokacin dakarun Iran, kama daga sojoji, Dakarun kare juyi (IRGC), Basij da sauransu, suka fara karfafa irin makaman da suke da su musamman a bangaren makamai masu linzami bugu da kari kan irin dabarun yaki da suke da su, kamar yadda kuma suka ci gaba da karfafa kawayensu na kungiyoyin gwagwarmaya a kasashen Labanon, Iraki, Yemen da kuma Zirin Gaza bugu da kari kan sojojin kasar Siriya, dukkanin wadannan don fuskantar irin wannan lokaci da gigi zai diba Amurkan ta kaddamar da yakin.

Watakila irin wadannan tanadin suna daga cikin abubuwan da ya sanya Iraniyawa ta bakin Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, fitowa fili ya bayyana cewar babu wani yakin da za zai faru a yankin, dukkanin wadannan barazanar da Trump yake yi buguzum ne kawai, amma lalle ya san cewa lalle ba zai sha ba matukar ya kaddamar da yakin.

Ala kulli hal alamu dai suna nuni da cewa da wuya dai yakin ya faru a wannan zangon, sai dai kuma a yi wani shirin na daban a wani zangon na daban. A wannan zangon dai Iran ta fadi nata, kawayenta a Iraki da Yemen ma sun ce wani abu, Hizbullah, Hamas, Jihad da Siriya kan ma ba su ce komai ba tukun.