A+ R A-
09 December 2019

Kame Jirgin Dakon Man Iran Da Birtaniyya Ta Yi Da Hatsarin Da Ke Cikin Hakan

Bayanai na kara fitowa dangane da dalilan da suka sanya Birtaniyya kame jirgin ruwan dakon man kasar Iran (Grace 1) a mashigar ruwan yankin Gibraltar (Jabal Tariq) a ranar Alhamis din da ta gabata.

Birtaniyya din dai ta ce an kame jirgin ne a yankin Gibraltar dake karkashin ikon Birtaniyyan saboda jirgin yana kan hanyar kai wa kasar Siriya mai ne lamarin da ya saba wa takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sanya wa gwamnatin Siriya.

Wannan dai shi ne abin da Birtaniyya ta ce kan dalilinta na kame jirgin. To sai dai a bangare guda shi kuma ministan harkokin wajen Spain da ke makwabtaka da yankin na Gibraltar, Josep Borrell, ya ce Birtaniyya ta kame jirgin ne bisa umarnin da kasar Amurka ta ba ta na ta kame jirgin.

Wannan dai su ne maganganu biyu kan batun kame jirgin, wanda da dama daga cikin masana dai sun fi gaskiya riwaya ta biyun  wato maganar ministan harkokin wajen Spain din saboda wasu dalilai kamar haka:

1). Abin da takunkumin EU din, wanda ta sanya wa Siriya a 2011, ya kumsa shi ne cewa kasashen kungiyar EU din ba za su sake sayen mai daga Siriya ba, amma ba wai za su hana Siriya sayar da mai dinta ko kuma shigowa da mai daga waje ba. Don haka ne mece ce alakar kame jirgin da batun takunkumin EU kamar yadda Birtaniyya ta ce?

2). Wannan dai ba shi ne karon farko da Iran take tura irin wadannan jirage dauke da mai zuwa Siriya ba, kuma ba a boye ba, a gaban idanuwan turawan EU din take yin haka, amma ba su taba wani kokari na dakatar da jiragen ba, me ya sa sai a wannan karon ne Birtaniyyan ta yi hakan?

A saboda haka ne da dama suka fi fifita magana ta biyu ta cewa Amurka ce ta bukaci Birtaniyya da ta kame jirgin, a matsayin wata sabuwar hanya ta matsin lambar da take ci gaba da yi wa Iran don karya tattalin arzikin kasar.

To idan har magana ta biyu din ita ce gaskiya, me hakan yake nufi? Sannan kuma wani hatsari yake cikin irin wannan matakin?

1). Shi ne cewa Turawa din sun bude wani sabon shafi na sanya kan su cikin tsaka mai wuyar fada da Iran a daidai lokacin da suke kokarin yin sulhu da Iran da kuma ceto yarjejeniyar nukiliyan da suka cimma da Iran.

2). Hakan zai kara sanya yankin Tekun Fashan cikin mawuyacin halin da yake ciki a halin yanzu musamman kan batun fitar da mai zuwa kasuwannin duniya da kasashen yankin suke yi. Saboda tun ba yau ba Iraniyawa sun fadi a fili cewa duk wani kokari na hana su sayar da man fetur din su, hakan zai sanya su rufe Mashigar Hormuz inda kasashen yankin suke wucewa da mafiya yawa daga cikin man fetur din da suke fitarwa zuwa kasuwar duniya.

3). Ita ma a nata bangaren Amurka ta yi barazanar mayar da martani kan Iran matukar ta dauki wannan mataki na rufe mashigar ta Hormuz, me hakan zai haifar idan har ta yi hakan? Kalma guda: Yaki (Allah Ya kiyaye). Don kuwa Iran ma ta sanar da cewa za ta mayar da martani ga duk wani harin da Amurka za ta kawo mata.

 

Daga karshe, koma dai mene ne abin da da dama daga cikin masana suke gani shi ne cewa kama wannan jirgin wani sako ne da Amurka take isarwa ga Iran cewa ‘za mu ci gaba da takura muku ta hanyoyi daban-daban don sanya ku mika wuya’. Ko za su cimma nasarar yin hakan, Allahu A’alam, amma dai dukkanin alamu suna nuni da cewa ba za su yi nasara ba, don Iraniyawa sun tabbatar, a kas, cewa lalle matsin lambar ba zai sanya su mika wuya ba.

To sai dai kuma a daidai lokacin da Amurkawan suke son aikewa da wannan sakon, a daidai lokacin da kuma gazawarsu a gaban Iran take kara bayyana don kuwa matakin kame wannan jirgin wata alama ce da ke nuni da cewa Amurkan ta gaza wajen yin fito na fito kai tsaye (amfani da karfin soji) da Iran; duk kuwa da barazanar da suke yi na yin hakan.