A+ R A-
01 April 2020

KASHE AL-BAGHDADI….Karshen Tsararren Aiki!! 1

“A daren jiya, Amurka ta zartar da hukunci a kan shugaban kungiyar ‘yan ta’adda na daya a duniya. Abubakar al-Baghdadi ya mutu. Shi ne shugaba kuma wanda ya kirkiri kungiyar ISIS, kungiyar ta’addanci mafi tsananin rashin tausayi da kuma amfani da tashin hankali a duk fadin duniya”.

Da wadannan kalmomi ne shugaban Amurka, Donald Trump, ya bude jawabinsa na sanar da ‘nasarar da sojojin Amurkan suka samu’ na kashe Ibrahim Awad al-Badri, wanda aka fi sani da Abubakar al-Baghdadi bayan wasu hare-haren da sojojin Amurkan suka ce sun kai maboyarsa da ke yankin Idlib na kasar Siriya.

Ko shakka babu kashe al-Baghdadi wani labari ne da zai faranta ran wasu daga cikin mutanen duniya musamman na yankin Gabas ta tsakiya wadanda suka fuskanci mafi munin rashin tausayi da ayyukan ta’addancin da kungiyarsa ta ISIS ta aikata tsawon shekaru kuma take ma ci gaba da aikatawa, lamarin da ya sanya gwamnati da al’ummomin kasashen Iraki da Siriya da kawayensu mikewa tsaye wajen fada da shi da kuma daularsa da ya ce ya kafa ta Musulunci a wadannan kasashen; duk kuwa da dardar din da suke ciki na yiyuwar sake bayyanar wani irinsa na daban.

Amurka din dai ta ce ta kashe Al-Baghdadin ne bayan tattaro wasu bayanan sirri da suka yi kan mutumin bisa taimakon wasu kasashe da Trump din ya ambaci sunayensu da suka hada da Iraki, Siriya, Rasha, Turkiyya da sauransu duk kuwa da cewa wasu sun musanta ba da taimakon…ala kulli hal wannan dai ba shi ne ya ke da muhimmanci sosai don kuwa ko ba dade ko ba jima gaskiyar lamarin dai za ta fito fili kowa ya gani.

Abin da ke da muhimmanci a halin yanzu, duk kuwa da cewa ba shi ne mafi muhimmanci ba, a nan gaba za mu yi bayanin abu mafi muhimmancin. To amma kafin lokacin abin da ke da muhimmancin fahimta a halin yanzu shi ne wasu abubuwa da suka faru wadanda suke dauke da alamun tambayoyi kansu da suka hada me al-Baghdadin ya ke yi a wannan yankin da aka ce an kashe shi, me ya sa aka kashe shi a halin yanzu da ake dab da zabe a Amurkan, kada dai tarihi ne yake kokarin maimaita kansa, bangarori da dama suna zargin Amurka da kirkiro kungiyar ISIS din, kamar yadda shi kansa Trump din yayi wannan zargin yana mai kafa hujja da maganganun wasu jami’an gwamnatin da ta gabace, to me ya faru suka kashe shugaban kungiyar da suka kirkira kuma…. Dukkanin wadannan za su taimaka wajen fahimtar wane ne al-Baghdadi da ire-irensa da kuma abin da ake kitsawa wa al’umma.

Idan muka fara da inda aka kashe al-Baghdadin, Amurkawa sun ce sun kashe shi ne a garin Barisha da ke arewa maso gabashin Idlib na kasar Siriya. Wannan shi ne daya daga cikin abubuwan mamakin wannan labarin na Amurka wanda kuma yake cike da alamomin tambayoyi kansa. Saboda shi wannan yankin yana karkashin ikon kungiyoyin ta’addanci irin su kungiyar ‘Tanzim Hurras al-Din’, Ansarut Tauhid da sauransu wadanda dukkaninsu suna karkashin kungiyar Jabhatun Nusra (Al-Nusra Front) wacce take karkashin kungiyar al-Qa’ida ta duniya; wadanda suke tsananin adawa da kungiyar ISIS ta al-Baghdadi kana kuma suke ta kashe junansu a kokarin kowacce na neman tabbatar da ikonta.

Ba zai baci ba idan muka dan yi karin bayani kan abin da ya shiga tsakaninsu har ya haifar da irin wannan gabar.

Tushe ko kuma uwar dukkanin wadannan kungiyoyin dai ita ce kungiyar al-Qa’ida ta Usama Bin Ladin kuma karkashinta suke gudanar da lamurransu. To sai dai an fara samun baraka ne a tsakanin su tun daga lokacin bayyanar Abu Mus’ab al-Zarqawi, shugaban kungiyar al-Tawhid wal Jihad, wacce daga baya ta zamanto Tanzim Qaidat al-Jihad fi Bilad Rafidayn (ko kuma al-Qa’ida a Iraki kamar yadda ake fi saninsu) lokacin da ya sanar da mubaya’arsa ga kungiyar Al-Qa’ida. Barakar ta kunno kai ne a 2005 lokacin da shugaban kungiyar Al-Qa’idan na lokacin Ayman Al-Zawahiri ya nuna rashin amincewarsa da yadda ‘yan kungiyar al-Zarqawin suke kashe fararen hula ba kyakkyaftawa a Iraki lamarin da al-Zarqawin ya ki amincewa da shi. Barakar ta ci gaba har zuwa lokacin da sojojin Amurka suka kashe shi a 2006 da kuma kashe wadanda suka gaje shi wato Abu Hamza al-Muhajir da Abu Umar al-Baghdadi a shekarar 2010 har zuwa lokacin da Abubakar Al-Baghdadi ya dare karagar shugabancin kungiyar.

Darewar al-Baghdadi karagar mulkin kungiyar ta al-Zarqawi ta kara fadada irin sabanin da ke tsakaninta da al-Qa’ida musamman bayan barkewar rikicin kasar Siriya a 2011 inda Al-Baghdadin ya tura da Abu Muhammad al-Jaulani zuwa Siriyan don kafa kungiyar al-Nusra Front a can da nufin kafa abin da suka kira gwamnatin Musulunci ta Iraki da Siriya karkashin jagorancin shi al-Baghdadin, lamarin da ita kanta kungiyar Al-Qaida ta duniyar ta ki amincewa da shi. Don kuwa a ra’ayin shugaban al-Qa’idan Ayman Zawahiri, shi ne shi al-Baghdadi ya ci gaba da ayyukansa a Iraki, shi kuwa Al-Jaulani a Siriya. To sai dai al-Baghdadi ya ki amincewa da hakan inda ya sanar da kafa abin da ya kira ad-Dawlat al-Islamiyya fil Iraq wash Sham (Daesh) ko kuma a turance Islamic State of Iraq and Syria (Levant) (ISIS, ISIL), wato Gwamnatin Musulunci ta Iraki da Siriya, bayan sun kame wasu yankuna masu yawa na kasar Iraki da Siriya inda al-Baghdadin ya sanar da kafa ‘gwamnatin Musulunci’ daga masallacin al-Nuri da ke garin Mosul a shekara ta 2014.

Tun bayan wannan ‘taurin kan’ da Al-Baghdadi yayi wa Ayman al-Zawahiri aka fara samun kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar al-Nusra Front din da sauran kungiyoyin da suke tare da ita wadanda suka ci gaba da mika mubaya’arsu ga kungiyar al-Qaida ta duniyar karkashin jagorancin al-Zawahiri, sannan kuma an sha samun yake-yake da zubar da jini a tsakaninsu. Don haka kasantuwar al-Baghdadi a wannan kauye na Barisha inda nan ne cibiya da kuma helkwatar wadannan kungiyoyi da suke tsananin adawa da shi kuma suke nemansa ruwa a jallo don su kama ko kashe shi, hakan wani lamari ne da ke sanya alamu tambayoyi masu yawa kan wannan lamarin da kuma shi kansa al-Baghdadin da kungiyar tasa da sauran kungiyoyin da suke wajen.

Lamarin imma dai da man tun asali dodorido ake wa mutane, wato duk bakinsu daya ne, ko kuma akwai wani bangare da ke jujjuya dukkanin wadannan kungiyoyi da ya ba wa Al-Baghdadin lamunin kiyaye lafiyarsa a wajen don kuwa kamar yadda wasu majiyoyi suka ce tun kimanin watanni 7 da suka gabata al-Baghdadin tare da masu gadinsa su biyu da iyalansa suka iso wajen tun bayan kashi da suka sha a Iraki, a hanyar su ta zuwa kasar Turkiyya.

(Akwai ci gaba)