A+ R A-
01 April 2020

KASHE AL-BAGHDADI….Karshen Tsararren Aiki!! 2

Kashe Abubakar al-Baghdadi da Amurka ta yi yayi kama da labarin Taras Bulba, da marubucin nan dan asalin Ukraine, Nikolai Vasilievich Gogol ya kawo cikin littafinsa inda Taras Bulba din yake ce ma dansa Andriy wanda ya ci amanarsa cewa: Ni na samar da kai (ni na rena ka), kuma ni na cancanci kashe ka” don haka sai ya bude masa wuta ya kashe shi.

Kasashen yammaci, musamman Amurka sun dau shekaru aru-aru suna amfani da ‘kungiyoyin Musulunci’ wajen cimma manufofinsu; wani lokaci don fada da akidar gurguzu kamar yadda suka yi a Afghanistan don fada da tsohuwar Tarayyar Sobiyeti, wani lokaci wajen fada da akidar ‘yan kasanci musamman a kasashen larabawa, wasu lokuta kuma don fada da farkawa ta Musulunci da wayewar kan da musulmi suke samu, a wani lokacin kuma wajen bakanta sunan Musulunci da bayyana shi a matsayin wani addini maras tausayi da bai san komai ba face zubar da jini kamar yadda yake faruwa a halin yanzu da dai sauransu.

Hakan kuwa ya biyo bayan irin yadda suke ganin Musulunci a matsayin babbar cikas ga burinsu na mulkin mallaka. Don haka suka ga babbar hanyar fada da shi ita ce shiga cikinsa da kuma amfani da wasu mabiyansa, wadanda ko dai saboda gurguwar fahimta ko kuma da gangan, suka riki wata hanya ta rashin yarda da kowa sai su. Wato ba sa ganin kowa a matsayin musulmi sai wanda ya yarda da abin da suke kai; kana kuma a shirye suke su zubar da jinin duk wani wanya saba wa abin da suke kai.

Ko shakka babu kungiyar ISIS da mabiyanta suna cikin irin wadannan kungiyoyin ko ma su ne a kan gaban masu irin wannan akida.

Duk kuwa da cewa batun kafa kungiyoyi irin su da Daesh (ISIS) da ake zargin Amurka da shi wani abu ne da yake a fili wanda hatta shi kansa shugaba Trump ya tabbatar da hakan cikin maganganunsa na yakin neman zabe inda ya zargi tsohuwar gwamnatin Obama da kafa wannan kungiyar, yana mai dogaro da kalaman wasu jami’an gwamnatin kan hakan, to ko ma ba wannan ba ayyukan irin wadannan kungiyoyi wani abu ne da ke nuni da wannan lamarin na yadda ake amfani da su don bakanta sunan Musulunci.

A matsayin misali idan muka dubi kasar Iraki, inda nan ne tushen ISIS din za mu ga cewa kasa ce wacce take karkashin mamayar Amurka, alal akalla a wadancan shekarun da aka kafa ISIS din ko kuma asalin tushen da ta samo asali. Abin da watakila za a yi tunani shi ne irin wadannan kungiyoyi na ‘jihadi’ babban abin da za su fi ba shi muhimmanci shi ne fada don fatattakar ‘yan mamaya, kamar yadda tun farko suka nuna wanda watakila hakan ne ma ya sanya aka samu tururuwar ‘masu kishin addini’ daga kasashe daban-daban na duniya zuwa Irakin da nufin yakar sojojin mamaya. To amma wai ana zaton wuta a makera sai aka same ta a masaka.

Don kuwa nan take bayan an tara wadannan ‘mujahidan’ wadanda suka fara yakar Amurka ‘bil hakki da gaskiya’ sai aka sauya fatawar da tun farko ta tara su ta: al-Aduwul ba’id aula bil qital min al-aduw al-qarib (wato makiyi na nesa (Amurka da kawayenta) shi ya fi cancanta a yaka sama da makiyi na kurkusa (musulmi ‘yan bidi’a), sai aka sauya wannan fatawar zuwa: al-Aduwul qarib aula bil qital min al-aduw al-ba’id (wato makiyi na kusa (‘yan bidi’a) shi ya fi cancanta a yaka a kan makiyi na nesa (wato Amurka da kawayenta) ko kuma abin da a takaice suke kira da “Qital al-qarib Aula min qital al-Ba’id, wato yakan na kurkusa shi ya fi a kan yakar na nesa. Me hakan yake nufi: (shi ne) maimakon yakar Amurka wacce ita ce bakuwa wacce ta zo daga nesa, sai aka juya lamarin cewa yakar na kurkusa wato al’ummar musulmi shi ne kan gaba maimakon Amurka da sauran ‘yan mamaya.

A saboda haka yakinsu ya kasance kan musulmin da suka ki bin su, musulmin da suka saba da su a fagen akida, musulmin da suka ki yi musu mubaya’a…... Don haka tsawon lokacin nan sun kashe dubun dubatan musulmi da lalata musu duk wasu abubuwan da suke da alaka da tarihi da ci gabansu a Iraki, Siriya, Mali da duk sauran wajajen da karfinsu ya kai.

To wani zai yi mamakin idan har haka ne me ya sa a halin yanzu kuma Amurka ta kashe al-Baghdadi? Amsar wannan tambayar dai a fili yake kuma za mu iya ganinsa cikin kissar da na bude wannan rubutu da shi na Taras Bulba da dansa Andriy wato: Ni na samar da kai, kuma ni na cancanci in kashe ka.

Lamarin dai biyu ne: Imma dai aikin da ake so yayi ya gama shi don haka a halin yanzu ba shi da amfani a wajensu ko kuma ya gaza wajen yin wannan aikin, don haka za a kawar da shi a kawo wani na daban. Ni dai a gani na biyun ma shi ne: Don kuwa duk da bata sunan Musulunci da yayi, duk da zubar da jinin musulmi da yayi, duk da lalata abubuwan tarihi da ci gaban Musulunci da yayi, to amma ya gaza wajen fada da tushen farkawa ta Musulunci da ake samu, ya gaza wajen kawo karshen kungiyoyi da kasashen da suke fada na hakika da ‘yan mamaya da akidarsu da mulkin mallaka, ya sha kashi a Siriya da Iraki da Labanon, ya gaza wajen raunana Iran da tabbatar da rashin tsaro a cikinta, ya gaza wajen fada da kungiyoyi na jihadi da fada da ‘yan mamaya na hakika irin su Hizbullah da Hash al-Sha’abi da sauransu. Don haka ba shi da wani amfani face a yi ‘waje rod’ da shi.

To amma ko shakka babu Amurka da kawayenta ba za su hakura ba, nan gaba kadan za mu sake ganin wani al-Baghdadin na daban: imma dai a siffa ta mutum ko kuma wata siffar ta daban (wato ta hanyar shigo da wani salo) da nufin ci gaba da dagula lamurra a kasashen musulmi.

Mai yiyuwa tarihin kashe Usama Bin Ladin da Amurka ta yi a shekara ta 2011 da kuma rikicin da suka kunna a lokacin a kasashen larabawa da ake kira da ‘Arab Spring’, yana kokarin sake faruwa ne sakamakon kashe al-Baghdadi da Amurkan ta yi da kuma zanga-zangogin da a halin yanzu aka fara ganin sun kunno kai a wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiya, musamman inda ISIS din ta sha kashi, musamman idan aka yi la’akari da yadda wadannan kasashe suka shigo cikin lamarin da kau da shi daga asalin abin da mutane suka kai. Mai yiyuwa hakan wani kokari ne na Amurkan wajen daukar fansa kan kasashe da kungiyoyin da ake kira da ‘Mihwar al-Muqawamah (Axis of Resistance) wadanda suka hana Amurkan cimma manufofinta a yankin.

A takaice dai, batun kashe al-Baghdadi da Amurka ta yi bai wuce abin da ministan sadarwa na Iran, Muhammad Jawad Azari Jahromi, ya rubuta a shafinsa na Twitter ba ne a matsayin mayar da martani ga kalaman Trump da ke kokarin bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara inda ya ce: “Not a big deal. You just killed your creature” (Wannan ba wani abu ba ne. Kun kashe halittar da kuka kirkira ce kawai).