A+ R A-
01 April 2020

ALLAH DAI YA KIYAYE KAWAI…..Amma Dai Kan Akwai Matsala Idan Haka Ta Faru

A daidai lokacin da dukkanin idanuwa suka koma kan kasashen Labanon da Iraki da ‘al’ummomin wadannan kasashen’ suke ci gaba da zanga-zangogin ‘neman tabbatar da adalci da kyakkyawar rayuwa’ duk kuwa da ci gaba da kokarin da ‘wasu bangarori’ suke yi na juya wannan yunkuri zuwa wani abu na daban, to sai dai daga dukkan alamu ana kokarin kunna wata wutar kuma ta daban wacce….hmmm bari dai in yi shiru.

Idan ana iya tunawa a farko-farkon wannan makon ne rundunar sojin Iran ta sanar da harbo wani jirgin sama mara matuki da ya shigo sararin samaniyyar kasar. Daga ina jirgin ya fito, na wata kasa ce, me ya zo yi? Jami’an Iran din sun yi gum da bakinsu ba tare da karin bayani ba. Me ya wannan shirun, sannan me hakan yake nufi? Bakinmu dai da goro, amma tabbas akwai wani abu a kas. Haka nan a wani bangaren Iran din ta sanar da korar wata jami’ar hukumar nan ta IAEA mai kula da makamashin nukiliya ta duniya daga cikin tawagar hukumar da suke sanya ido kan ayyukan nukiliyan kasar sakamakon gano cewa tana dauke da wata na’ura ‘ta leken asiri’ a lokacin da suka kai ziyarar cibiyar nukiliyar kasar da ke Natanz. Jami’an da abin ya shafa sun gudanar da bincike sosai kan wannan matar, sai dai a nan ma sun yi gum da bakinsu kan abin da suka gano, wanda ko shakka babu sun gano din.

Dukkanin wadannan abubuwa, watakila da sake dawo da batun tace uranium a cibiyar Fordo da Iran ta fara, wasu abubuwa ne masu muhimmancin gaske da suke nuni da cewa tabbas akwai wani abu a kas da ke shirin faruwa a yanki…

A bangare guda kuma wani lamari mai matukar muhimmanci da kuma hatsarin gaske, da watakila yana da alaka da alal akalla da abubuwa biyu da suka faru a Iran da muka yi bayaninsu a sama, shi ne wani labari da tsohon jakadan ‘Isra’ila’ a Amurka, Michael Oren ya bayar dangane da wani shiri da ‘Isra’ilan’ take yi na kawo wa Iran da kawayenta hari sakamakon irin damuwa da take ciki na abin da suka kira ‘irin karfin da Iran da kawayenta suke ci gaba da samu’ a bangare guda ga irin yadda Amurka take ci gaba da yin watsi da kawayenta a yankin wanda hakan ke kara wa Iran karfi.

A cikin wata makala da ya buga a mujallar The Atlantic ta Amurka mai taken "The Coming Middle East Conflagration", Michael Oren ya ba da labarin cewa cikin ‘yan kwanakin da suka gabata majalisar manyan ministocin ‘Isra’ila’ wacce majalisa ce mai matukar muhimmanci da shawara yaki ko zaman lafiya ke hannunta ko kuma alal akalla tana taka gagarumar rawa a wannan bangaren, ta zauna har sau biyu don tattauna yiyuwar kawo wa Iran hari, yana mai karin haske kan wasu matakai da ‘Isra’ilan’ ta fara dauka kan hakan da kuma irin abubuwan da za su iya faruwa matukar ‘Isra’ilan ta kaddamar da wadannan hare-hare.

A takaice dai abin da makalar take nuni da shi, shi ne cewa:

Akwai yiyuwar Netanyahu, firayi ministan Isra’ilan yayi gaba gadi ya kawo harin, wanda kuma hakan ba abu ne da za a iya kore yiyuwarsa ba bisa la’akari da mawuyacin halin da yake ciki da suka hada da: gazawar da yayi wajen kafa gwamnati bayan kayen da ya sha a zabe, matsin lambar da yake fuskantar daga wajen jam’iyyarsa ta Likud haka nan kuma ga barazanar tafiya gidan yari da yake fuskanta sakamakon zargin rashawa da cin hanci da ake masa da dai sauransu. Dukkanin wadannan suna daga cikin abubuwan da za su iya sanya shi kaddamar da wannan hari musamman ma fara yanke kauna da ‘Isra’ila’ take yi da gwamnatin Trump ta Amurka.

Daga dukkan alamu wajajen da Netanyahun zai so kai musu hare-haren su ne wajaje irin su cibiyoyin nukiliya na Iran da ke Fordo ko Natanz ko kuma wasu cibiyoyi da sansanoni na soji masu muhimmanci na Iran ko kuma cibiyoyin kungiyar Hizbullah na Labanon, a matsayinta na daya daga cikin kawayen Iran masu hatsari a gare ta.

To a nan ne fa hatsarin yake a cewar Oren, don kuwa matukar hakan ta faru, to kuwa Iran za ta mayar da martani da dukkan karfinta kan wajaje masu muhimmanci a ‘Isra’ila’ kamar cibiyoyin wutar lantarki, ruwa, cibiyar kula da sinadarin ammonia da ke Haifa ko kuma na nukiliya da ke Dimona wanda kowane guda daga cikinsu zai iya zama babban bala’i ga al’ummar Isra’ilan ko kuma filin jirgin saman Ben Gurion wanda zai iya dakatar da harkokin zirga-zirga da kasuwanci da dai sauransu. Haka nan kuma mai yiyuwa ne ‘kawayen Iran’ a Labanon (Hizbullah), Siriya, Iraki da sauransu su ma su mayar da martani ta hanyar amfani da irin na su karfin da suke da shi.

A saboda haka ne ma Oren din ya ce idan hakan ta faru, to akwai yiyuwar ‘Isra’ila’ za ta fuskanci ruwan makamai masu linzami da suka kai guda 4000 a kowace rana wadanda a cewarsa ko shakka babu makamai da na’urorin garkuwa da ‘Isra’ilan’ take da su ba za su iya tarwatsa dukkansu ba.

Me hakan yake nufi?

A cewar Oren, hakan dai yana nufin ‘cikakkiyar rushewar’ Isra’ila wanda hakan shi ne abin da daman Iran take so. A cewarsa duk da cewa su ma makaman ‘Isra’ilan’ za su iya haifar da gagarumar hasara ga Iran da kawayen nata, to amma irin hasarar da Isra’ila za ta fuskanta ba karami ba ne, musamman a irin wannan yanayi na ‘jan kafa’ da gwamnatin Amurka take yi da kokarin gujewa kawayenta don tseratar da kanta haka nan kuma ga matsalar da kungiyar tsaro ta NATO take fuskanta ta rarrabuwar kan da ake samu a tsakanin membobinta da har ya sa shugaban Faransa Emmanuel Macron bayyana cewar kungiyar tana shure-shuren mutuwa, wanda a lokuta da dama Amurka da Isra’ilan su kan yi amfani da kungiyar wajen kaddamar da hare-hare kan gwamnatoci da kasashen da suke adawa da su kamar yadda ya faru a baya kan Saddam Husain.

Wani lamari mai hatsari na daban shi ne kokarin da ‘Isra’ilan’ take yi na janyo wasu kasashen larabawa jiki a kokarin da take yi na samun goyon baya don kai wa Iran hari, bisa la’akari da irin ci gaba da abin da suka kira ‘rikon sakainar kashin’ da gwamnatin Trump take yi ga ‘barazanar Iran’, wanda matukar wadannan larabawan suka amince suka biye mata to daga dukkan alamu za su iya fadawa cikin wannan fargaba da kuma damuwar da ‘Isra’ilan’ take ciki a halin yanzu.

To a irin wannan yanayi mene ne abin yi?

Mafita dai cikin dukkanin wannan matsalar ita ce abin da marubucin makalar ya ce a karshenta, a takaice ita ce cewa: Har yanzu yayi amanna da cewa Amurka za ta taimakawa Isra’ila musamman a yayin yaki, sai dai kuma ya ce: HAR YANZU INA TUNA A SHEKARAR 1973, LOKACIN DA MASAR DA SIRIYA SUKA FAHIMCI SHUGABAN (AMURKA) YANA FAMA DA MATSALAR KOKARIN TSIGE SHI DA AKE YI, DON HAKA SUKA KADDAMAR DA YAKI KAN ISRA’ILA SABODA SUNA GANIN TA RASA KARIYAR DA TAKE DA SHI. DUK DA CEWA ISRA’ILA TA YI NASARA A YAKIN, SAI DAI TA JI JIKI. DON HAKA YAKI MAI ZUWA ZA TA FI JIN JIKI SOSAI.

Me hakan yake nufi? Hakan yana nufin ‘Ina amfanin badi ba rai’. A wata kalmar ta daban ina amfanin kaddamar da yakin da babu tabbas za a yi nasara cikinsa, ina amfanin kaddamar da yakin da ‘za a ji jiki sosai’ a cikinsa, Iran dai ta zama wani karfi da a halin yanzu dai dole a saurara mata, dole a zauna teburin tattaunawa da ita don hakan ita ce kawai hanya guda da za ta amfani kowa.