A+ R A-
01 April 2020

Dalilan Kara Farashin Man Fetur Ga Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi

Daga dukkan alamu idanuwa sun sake komawa kan kasar Iran saboda abubuwan da suka faru ko kuma suke ci gaba da faruwa a kasar tun daga jiya zuwa yau sakamakon karin farashin man fetur da gwamnati ta yi, inda wasu daga cikin al’ummomin kasar suka fito kan tituna don nuna rashin amincewarsu. Tun daga jiya zuwa yau din dai mutane, kwararru da sauransu, suke ta tofa albarkacin bakinsu kan lamari. A daidai lokacin da wasu suke ganin matsayar da aka dauka din a matsayin wata matsaya da ta dace amma kuma an dauke ta ba a lokacin da ya dace ba. Wasu kuma wadanda da man ‘ungulu ne mai jiran tsammani’ sai suka fito da maitarsu fili, su da kafafen watsa labaransu babu abin da suka sa a gaba sai kirkiro labarurruka da yada hotuna na karya wasu kuma na wasu shekarun da suka gabata don kambama abin da ke faruwa.

Ala kulli hal, wannan da man shi ne abin da ake zaton gani daga wajen irin wadannan mutanen wadanda suka gaza wajen cutar da Iran din ta hanyar takunkumi da sauran….

To amma dai idan har abin a bayyana abin da ke faruwa din a takaice ne, to ana iya cewa gwamnatin Iran, a kokarinta na magance wasu matsalolin da ake fuskanta a kasar da kuma magance irin yadda wasu suke amfani da man fetur a kasar ba ta hanyar da ta dace ba saboda arahar da yake da shi, ya sanya gwamnatin janye wani bangare na tallafin da take ba wa bangaren mai don ta samu wasu karin kudaden shiga daga rarar mai din da nufin taimakon iyalai marasa abin hannu a kasar wadanda kuma su ne suka fi cancantar irin wadannan kulawar sama da kowa.

A bisa tsarin da gwamnatin ta sanar dai shi ne cewa an amince wa duk wani mai mota a kasar da ya sayi lita 60 na man fetur a kowane wata a kan farashin toman 1500 (kudin Iran) wato kimanin Naira 46 (centi 13 kenan). Idan kuwa har yana bukatar sama da hakan ne, to zai sayi kowane lita a kan toman 3000 wato kimanin Naira 93 (centi 26) kenan.

Ana kirga Iran a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da suka fi sayar da man fetur wa al’ummominsu a bisa farashi mai rahusa ainun sakamakon tallafin gwamnati, lamarin da ya kara irin yawan man da ake amfani da shi a cikin gida ya kai lita miliyan 90 a kowace rana, sakamakon yadda wasu suke ‘almubazzaranci’ da mai din saboda araharsa, wasu kuma suke fasa kwabrinsa zuwa kasashen makwabta inda man yake tsada. Don kuwa wasu bayanai sun ce kusan rabin wannan adadin wasu ‘bata gari’ ne suke fasa kwabrinsa zuwa kasashen makwabta, wanda hakan ba karamar hasara ce gwamnatin take yi ba. Maimakon tallafin da ta bayar ya amfani talakawan kasar sai wasu ne kawai suke amfanuwa da wannan tallafin.

Ala kulli hal, akwai bukatar mahukuntan Iran su yi kokari tukuru, kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fadi, wajen ganin sun sanya ido kan wannan shiri da suke da shi na tallafa wa marasa abin hannu na daga cikin al’ummarsu, kada su bari wasu su yi amfani da hakan wajen arzurta kansu kamar yadda yake faruwa a wasu kasashen. Don ta hakan ne shi talaka zai ga lalle don shi ake yi wanda hakan zai ba shi karfin gwiwan tsayawa kyam wajen goyon bayan gwamnati da kuma fada da makirce-makircen makiya wadanda alamu a bayyane suna nuni da cewa tuni sun fara shigowa cikin fage. Kafafen watsa labaransu suna nan suna aiki ba dare ba rana wajen yada labarurrukan karya da tunzura mutane.

Iran dai ba ita ce kasar farko da ta kara farashin mai ba, akwai kasashen yankin da suke makwabtaka da ita da suka kara farashin mai din irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) wasu ma har kashi dari bisa dari da ma janye wasu tallafin da gwamnati take bayarwa kan wasu abubuwa irin su ruwa da wutar lantarki to sai dai ba a samu irin wadannan zanga-zangogi ba. Watakila saboda dalilai irin na karancin mutane kamar a UAE ko kuma saboda gwamnatin tana dauka matakin ba sani ba sabo kan duk wani wanda yayi kokarin nuna rashin amincewarsa kan wani mataki na gwamnati kamar yadda lamarin ya ke a Saudiyya, ko kuma watakila kasashen yammaci ba sa kokarin tunzura al’ummominsu da kuma yi musu bakar farfaganda ta karya kamar yadda suke yi a Iran a kokarin da suke yi na kifar da gwamnatin kasar.

To sai dai bisa dukkanin alamu a wannan karon ma makiyan Iran din ba za su yi nasara ba, don kuwa tun daga jiya zuwa yau da dama daga cikin al’ummomin Iran din sun fara rarrabe kansu daga masu kone-kone da neman tada fitina, wanda hakan babban ci gaba ne, kana kuma wata cikas ne ga makiyan wajen cimma manufarsu. Kamar yadda kuma tuni jami’an tsaron kasar suka sanar da daukan matakan da suka dace wajen ganin wannan makircin bai yi nasara ba, kamar yadda kuma suka sanar da gano wasu da suke da hannu cikin kone-konen da aka yi wadanda suke da alaka da wasu kasashe na waje.

Wani abu kuma shi ne bayanin da Jagora Imam Khamenei yayi a safiyar yau din nan wajen darashin Bahasul Kharij da yake bayarwa inda yayi karin haske kan matakin da gwamnatin ta dauka da kuma kiran al’ummar kasar da su yi taka tsantsan da makircin makiya. Ko shakka babu wannan jawabi na sa zai taka ko kuma ma ya taka gagarumar rawa rage kaifin wannan fitina da ake kokarin kunnawa.