A+ R A-
01 April 2020

Su Wa Ke Da Hannu Cikin Juyin Mulkin Da Aka Yi Wa Evo Morales A Kasar Bolivia?

Daya daga cikin muhimman lamurran da suka faru cikin ‘yan kwanakin nan, wanda watakila ba a ba shi hakkinsa sosai ba, shi ne batun ‘juyin mulkin’ da aka yi a kasar Bolivia wanda wasu suke kira da’ juyin mulkin Amurka’ wa shugaba Evo Morales. Ana iya kallon wannan lamarin ta bangarori daban-daban, kamar yadda ake kallon saura batutuwa da lamurra na siyasa da suke faruwa a duniya. Bisa la’akari da irin yadda abin da ya faru a Bolivian ne ya sanya da dama suke ganin akwai wasu ‘hannaye’ cikin lamarin, wadanda watakila ana iya kasa su gida biyu: dalilai na cikin gida da kuma dalilai na waje.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai zababben shugaban Bolivia Evo Morales ya sanar da murabus dinsa daga mukamin shugaban kasar sannan kuma ya ta fi gudun hijira zuwa kasar Mexico. Lamarin dai ya faro ne bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 20 ga watan Oktoban nan (2019) inda Morales ya lashe zaben a zagayen farko sai dai ‘yan adawa, musamman wadanda suke samun goyon baya daga wajen kasar, sun ki amincewa da sakamakon zaben. Bayan ja-in-ja daga karshe dai shugaba Morales din ya amince a sake zaben amma duk da haka ‘yan adawan suka ki amincewa, suna masu cewa dole ne kawai ya sauka daga karagar mulki. Daga baya kuma sojoji suka shigo cikin lamarin da tilasta masa yin murabus, inda bayan murabus din ya fice daga kasar don tseratar da ransa.

To amma yayin da ake magana dangane da wannan juyin mulkin da ma abubuwan da suka faru kafinsa, abin da ya fi daukar hankula shi ne irin rawar da ‘yan kasashen waje suka taka wanda ya dara wanda ‘yan cikin gida suka taka, musamman rawar da kungiyoyin leken asirin Amurka da wadanda suke da alaka da su suka taka wajen shirya juyin mulkin da kuma tunzura ‘mutane’ a kan zababbiyar gwamnatin Evo Morales.

Daya daga cikin abubuwan da suke tabbatar da hannun da Amurka da kungiyoyin leken asirinta suke da shi cikin wannan juyin mulkin shi ne abin da tsohon Sanatan Amurkan Mike Gravel ya fadi a shafinsa na Twitter yayin da yake magana kan batun juyin mulki a Bolivian, inda ya ce: “Karyar da kuke ji shi ne cewa kasashen ‘yan gurguzu sun fadi kasa warwas. Amma a hakikanin gaskiya (abin da ya faru) wani kokari na mulkin mallakan Amurka ne wajen dakile duk wata al’umma wacce za ta yi adawa da wannan tsari na ta (na mulkin mallaka) a kowane lokaci”.

Don haka sai ya sake rubuta cewa: “Ana taya kungiyar CIA murnar samun iko a Bolivia”.

Wanda hakan yana nuni karara da irin hannun da CIA take da shi cikin wannan juyin mulkin.

Dukkanin wadannan abubuwan kuwa sun faru ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka da kawayenta na Latin Amurka irin su Brazil, Colombia da Peru suke ta kokari wajen haifar da fitina da tashin tashina a birnin La Paz, babban birnin Bolivia da sauran garuruwa na kasar da sunan an gudanar da magudi a zaben da aka yi alhali kuwa hatta cibiyoyin kasa da kasa da suka sanya ido kan zaben sun tabbatar da ingancinsa.

Abin tambayar a nan shi ne mene ne dalilin da ya sanya gwamnatin Trump ta Amurka ta ke goyon bayan kawar da Morales daga karagar mulki? A taikaice dai ana iya cewa dalilin hakan shi ne ‘kokarin kawo karshen duk wata murya da kuma duk wani shugaban da zai yi adawa da ‘iko da kuma mulkin mallakan Amurka’ a wannan yanki na Latin Amurka. Wanda ko shakka babu Morales kuwa yana daga cikin irin wadannan shugabannin wadanda tun daga lokacin da ya hau karagar mulkin kasar Bolivia ya sanar da adawarsa ga mulkin mallakar Amurka a kasarsa da ma yankin baki daya, sannan kuma yayi kokari wajen kulla kyakkyawar alaka da wasu shugabannin yankin masu adawa da mulkin mallakar Amurkan irin su marigayi Shugaba Hugo Chavez na Venezuela da wanda ya gaje shi Nicolas Maduro, da shugabanni irin su Fidel Castro na Cuba, Rafael Corea na Ecuador da ma wasu kasashen duniya irin su Rasha, Iran da sauransu.

Wani batun kuma da ya hada Morales da Amurka shi ne batun irin goyon bayan da yake ba wa al’ummar Palastinu a kokarinsu na kafa kasarsu mai cin gashin kanta da kuma yin Allah wadai da irin danyen aikin da ‘Isra’ila’ take yi wa Palastinawa. Don kuwa shugaba Morales shi ne shugaban kasa na farko da ya katse alakar kasarsa da ‘Isra’ila’ a 2009 bayan yakin Gaza, sannan kuma daga baya ya amincewa da Palastinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Haka nan kuma ya kasance mai goyon bayan Palastinawa hatta a kan mimbarin Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda kuma yake kiran Isra’ila a matsayin ‘yar ta’addan kasa da dai sauransu.

Haka nan kuma alakarsa da Iran, don kuwa tun bayan darewarsa karagar mulki, shugaba Morales yayi kokari sosai wajen kyautata alakarsa da Iran ta bangarori daban-daban musamman a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Iran Dakta Mahmood Ahmadinejad.

Haka nan alakar da Rasha ma….

Dukkanin wadannan wasu abubuwa ne da ko shakka babu babban zunubi ne da Amurkan ba za ta taba yafe shi ba.