A+ R A-
01 April 2020

Jerin Gwanon Goyon Bayan Gwamnati A Iran, Murna Ta Koma Ciki Ga Saudiyya Da Kawayenta

Daga dukkan alamu murna na shirin komawa ciki, in ma ba ta koma din ba kenan, ga Saudiyya da kawayenta na daga Amurkawa da Sahyoniyawan ‘Isra’ila’ ko kuma in mun dau sassauto mu ce ga kafafen watsa labaran da suke da alaka kai tsaye da ita, irin su tashar talabijin din nan ta Al-Arabiyya’, sakamakon jerin gwanon da ake ci gaba da yi a kasar Iran na nuna goyon bayan gwamnati da kuma yin Allah wadai da masu tada fitina da kuma kone-kone a kasar biyo bayan sanarwar kara farashin mai da gwamnatin ta yi a makon da ya wuce wanda hakan ke nuni da kawo karshen fitinar da wasu suka tayar a kasar.

Duk wanda ya kalli wadannan tashoshi musamman tashar ta Al-Arabiyya da kuma bibiyen wasu shafukan sada zumunci (social media) da suke da alaka ta kut da kut da gwamnatin Saudiyyan da kawayenta cikin kwanakin nan musamman a farko-farkon zanga-zangogin da aka yi a kasar ta Iran zai ga yadda wadannan tashoshin suka dinga kururuta abin da ke faruwa a Iran din a wasu lokutan ma har da shirya wasu fina-finai da hotuna na karya kan lamarin da kuma yin ‘busharar’ faduwar gwamnatin Musulunci ta Iran din. Kai wasu daga cikin masu musu sharhi ma har kiran mahukuntan Saudiyyan suke yi da su kawo karshen tattaunawar sulhun da suke yi da ‘yan Houthi na kasar Yemen, suna masu cewa nan da ‘yan kwanaki gwamnatin Iran za ta fadi wanda hakan na nufin karshen ‘yan Houthi din kenan tun da daman Iran din ce karfinsu.

A fili yake cewa gwamnatin Saudiyya ta jima tana fatan ganin faruwar irin wannan rikici na cikin gida a Iran wanda zai kai ga rugujewar yanayin tsaro a kasar wanda daga karshe kuma zai kai ga faduwar gwamnatin, kamar yadda Yarima mai jiran gado na Saudiyyan Muhammad Bin Salman ya bayyana hakan a fili jim kadan bayan darewarsa karagar yarimancin. Hakan ne ma ta sanya wasu suka fassara irin goyon bayan da Saudiyya take ba wa wasu kungiyoyi da suke adawa da gwamnatin Musulunci ta Iran din irin su kungiyar nan ta munafukai ta MKO da kuma wasu ‘yan tsirarru larabawa a yankin Ahwaz na Iran da dai sauransu a matsayin wannan kokari da Saudiyya take yi na cimma wannan manufar.

Mai yiyuwa irin wadancan ‘busharori’ na faduwar gwamnatin Iran da wasu suka dinga yi musamman a farko-farkon barkewar rikicin, wanda daga baya ta bayyana cewar akwai hannun wadanda mahukuntan Iran suka kira da ‘makiya’ cikin ruruta shi da daukarsa zuwa wani waje na daban, mai yiyuwa su sanya mahukuntan Saudiyyan tunanin sauya ra’ayinsu kan wannan tattaunawa da ‘yan Houthin ganin cewa ga wata dama ta samu da za su cimma manufar da suke da ita ta kaddamar da harin “Asifatul al-Hazm” (Decisive Storm) a kan al’ummar Yemen. Wasu alamu kuma suna nuni da hakan musamman idan aka yi la’akari da wasu bayanan da suke fitowa daga wajen taron tattaunawar sulhun da ke gudana tsakaninsu da ‘yan Houthin a kasar Oman karkashin kulawar Sarki Qaboosu, na irin jan kafar da Saudiyyan ta fara yi a wajen tattaunawar sabanin yadda a baya ta sanar da shirin ta na cimma sulhu da kawo karshen yakin sakamakon abin da wasu suka kira ‘shan kashin da take yi a hannun ‘yan Houthin a Yemen...

Amma abubuwan da suka faru daga baya ya zuwa yanzu, musamnma bayan jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi a safiyar Lahadin da ta gabata, ya kamata ya sanya su sake lissafi da kuma tunani kan wannan ‘busharar’ da aka yi musu.

Ko shakka babu irin fitowar da miliyoyin al’ummar Iran suka yi cikin ‘yan kwanakin nan kuma suke ci gaba da yi a garuruwa daban daban na kasar don nuna goyon bayansu ga jawabin Jagoran da kuma yin Allah wadai da masu tada fitinar da kone-konen kayayyakin gwamnati da na jama’a, wani lamari ne da za a iya cewa ya kawo karshen wannan ‘makircin’ da kuma ‘busharar’ faduwar gwamnatin ta Iran.

Tun da fari ma dai wasu ganin masu wadannan ‘busharori’ sun yi riga malam masallaci ne don kuwa wannan ba shi ne karon farko da irin wannan rikicin ke faruwa a Iran ba, don haka mahukutan kasar suna da kwarewa wajen magance irin wadannan rikice-rikice na cikin gida ta hanyar ‘rabe aya da tsakuwa’ tsakanin masu zanga-zangar neman biya musu bukatunsu na hakika da kuma masu neman tada fitina da biyan bukatun iyayengijinsu na waje. Inda mahukutan suke mu’amala ta ‘tausayawa’ da nuna damuwa ga kungiyar farko (wato masu neman biyan bukatunsu na hakika) da kuma mu’amala ta ‘ba sani ba sabo’ da kungiya ta biyu (wato masu neman tada fitina).

Abin nufi a nan shi ne mutane suna da hakkin su fito don nuna rashin amincewarsu ga duk wata matsaya da gwamnati ta dauka da suke ganin bai musu dadi ba kuma gwamnatin a shirye take ta saurare su matukar dai suka bi hanyoyin da doka ta tanadar, to amma a bangare guda kuma gwamnatin ba za ta taba amincewa ko yin sassauci ga duk wani mai kokarin tada fitina da kuma yin barazana ga tsaron kasar wanda daman shi ne abin da makiya suka jima suna hankoro ba.