A+ R A-
01 April 2020

Al'ummar Iran Sun Sake Jaddada Wajibcin Ɗaukar Fansar Jinin Janar Ƙasim Sulaimani

Gagarumar jana'izar da al'ummar birnin Tehran, babban birnin ƙasar Iran, ƙarƙashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, suka yi wa Shahid Janar Ƙasim Sulaimani da abokansa da suka yi shahada sakamakon harin 'ta'addancin' da Amurka ta kai musu a birnin Bagadaza na ƙasar Iraƙi, ya sake bayyanar da irin muhimmancin da wannan Janar ɗin yake da shi, alal aƙalla, a zukatan al'ummar Iran sannan da ma zukatan sauran al'ummomin duniyar musulmi.

Ni dai tsawon zama na a nan (wanda shekarun suna da ɗan dama – murmushi) ban taɓa ganin irin wannan jana'izar da aka yi wa wani a ƙasar Iran ba, ta ɓangarori da dama: yawan jama'a, murya guda ta nuna goyon baya ga 'Janar' da kuma neman 'ɗaukar fansa', uwa uba kuma yadda Imam Khamenei ya nuna tausayawarsa da zubar da hawaye da ke cike da saƙonni ga masoya da maƙiya….dukkanin waɗannan abubuwa ne da suke nuni da muhimmancin wannan bawan Allah a zukatan Iraniyawa.

Me ya sa Ƙasim Sulaimani?

Tun bayan yaƙin shekaru 8 da tsohuwar gwamnatin Saddam ta Iraƙi ta kallafawa Iran, shugabannin ƙasar suka ɗau wasu matakai na fuskantar irin wannan ƙalubalen da za su iya fuskanta a nan gaba, wanda hakan ya haɗa da dabaru 'na kai hari' da kuma 'na kariya'. Waɗannan dabarun kuwa ba dole a ɓangaren soji ne kawai ba, a ɓangarori daban-daban bisa la'akari da cewa ƙalubalen da take fuskanta ɗin sun haɗa da na 'soji' da kuma na tattalin arziki musamman bisa la'akari da irin takunkumin da aka dinga sanya mata. To amma da yake maganar da muke yi yanzu ta fi shafan ɓangaren soji, shi ne abin da za mu fi ba shi muhimmanci.

Bayanai sun nuna cewa a wajajen shekarar 1992, Ayatullah Khamenei, a matsayinsa na babban kwamandan dakarun ƙasar Iran, ya fito da wasu sabbin 'dabaru na yaƙi' da nufin tinƙarar ƙalubale da kuma barazanar da Iran take fuskanta. Ba don gudn tsawaitawa ba, da mun faɗaɗa bayani kan wannan shirin, to amma wani ɓangare na sa ya ƙumshi:

(1). Ƙarfafa irin ƙarfi na makamai musamman makamai masu linzami, da Iran take da shi. A wannan ɓangaren Iran ta samu nasarar ƙera makamai masu linzami masu cin matsakaici da dogon zango sannan kuma waɗanda suke da ƙarfin tarwatsa duk wani wajen da aka tura su don shi.

 (2). Samarwa ko kuma ƙarfafa ƙungiyoyin gwagwarmaya na yankin Gabas ta tsakiya da taimaka musu da dukkanin abubuwan da suke buƙata na daga makamai da dabarun yaƙi, wanda hakan ne ya samar da kuma ƙarfafa ƙungiyoyin gwagarmaya irin su Hizbullah a ƙasar Labanon, Hamas da Jihad da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa, Hashd al-Sha'abi da sauransu a Iraƙi, ta wani ɓangaren kuma dakarun Ansarullah a Yemen da dai sauransu.

Ko shakka babu Janar Sulaimani ya taka gagarumar rawa a dukkanin waɗannan ɓangarori biyu musamman ma na biyun, wanda ana iya cewa ma shi ne ma kan gaba wajen wannan aikin, wanda yake a matsayin ɗaya daga cikin tushen ƙarfin Iran a faɗar da take yi da 'ma'abota girman kan duniya' ƙarƙashin jagorancin Amurka.

Tabbas kashe mutum irin Janar Ƙasim Sulaimani ba wani lamari ne da Iran za ta rufe ido ta bar shi ya wuce haka nan ba.

Don haka ne ma batun ɗaukar fansa jininsa ya zamanto wani abu da al'ummar Iran, shugabanni da talakawansu, suka tabbatar da shi, kai ana ma iya cewa wani lamari ne da babu kokwanto cikinsa, musamman ma idan aka yi la'akari da abin da ya zo cikin saƙon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya faɗi cikin saƙon ta'aziyyar shahadar Janar Sulaimanin da abokansa cewa: "ɗaukar fansa mai tsanani tana jiran waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki". Magana ta ƙare. Waɗanda suka san shi sun tabbatar da cewa ba mutum ne mai magana haka kawai ba, amma idan ya faɗi to lalle zai aiwatar. Wataƙila ma hakan ne ya sanya shi jagorantar zaman majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar ta Iran da aka gudanar a ranar Juma'ar da ta gabata don yanke irin martanin da ya kamata a mayar wa wannan ɗanyen aikin. Wasu dai sun ce wannan shi ne karon farko da ya taɓa jagorantar zaman wannan majalisar, wacce take a matsayin mai yanke shawarar 'yaƙi ko zaman lafiya' a ƙasar Iran.

Bayan wannan zaman, majalisar ta fitar da sanarwa, daga cikin abin da sanarwar ta ƙumsa akwai cewa:

1). Wajibi ne Amurka ta san cewa ta tafka gagarumin kuskure ta hanyar kashe Janar Sulaimani, kuma ba za ta taɓa tsira daga wannan kuskuren cikin sauƙi ba.

2). An ɗau dukkanin matakan da suka dace (wajen ɗaukar fansa) sannan kuma nauyin dukkanin abin da zai biyo baya yana wuyan Amurka ne.

3). Ko shakka babu za a ɗau fansa mai tsanani a kan waɗanda suka aikata wannan aika-aika a lokaci da kuma wajen da ya dace.

Don haka babu kokwanto, komai kashinsa, cikin batun ɗaukar fansar jinin 'Sardar' (kamar yadda Iraniyawa suke kiransa). Abin tambayar kawai shi ne yaushe, ta yaya kuma a ina, za'a ɗau wannan fansa?

Amsar waɗannan tambayoyi kuwa suna da sauƙi kuma za a iya ganinsu a taƙaice cikin wannan saƙon ta'aziyyar Jagora Imam Khamenei da kuma sanarwar majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar ta Iran.

A cikin saƙon na sa, Jagoran ya bayyana cewar: "Shahid Sulaimani ɗan gwagwarmaya ne na ƙasa da ƙasa, don haka dukkanin masoya gwagwarmaya za su buƙaci ɗaukar fansar jininsa".

Me hakan yake nufi: Yana nufin, bayan kasantuwar Janar Sulaimani ɗan ƙasar Iran, wanda Iraniyawa za su ɗau fansar jininsa a matsayinsa na ɗan ƙasar su kana kuma Janar ɗin soji na ƙasar, wanda maganganun kwamandojin soji da na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) na Iran duk sun tabbatar da hakan. Har ila yau kuma ƙungiyoyin gwagwarmaya, waɗanda Janar Sulaimanin ya taka gagarumar rawa wajen karfafa su, su ma za su ɗau fansar jininsa a matsayinsa na ɗaya daga cikinsu. Maganganun, Sayyid Hasan Nasrullah na ƙungiyar Hizbullah da sauran jagorori da kwamandojin ƙungiyoyi irin su Hashd al-Sha'abi, Hamas, Jihad Islami, Ansarullah da sauransu abubuwa ne da suke tabbatar da hakan.

Yaushe za a ɗau wannan fansar: Da yake yaƙi, wai an ce, ɗan yaudara ne, mutum ba zai faɗi ranar da zai kai hari kan maƙiyinsa ba, amma dai dukkanin alamu suna nuni da cewa lamarin ba zai ɗau lokaci ba.

Ina za a kai harin: wannan kuwa wani lamari ne da yake a fili shi ma. Amurka tana da sansanoni soji 'bila adadin' a wannan yankin, tana da ofisoshi da cibiyoyi watsa manufofinta na fili da na ɓoye su ma 'bila adadin', tana da…., tana da….., dukkanin waɗannan wajajen suna da alaƙa da sojojin Amurka da kuma siyasarta ta mamaya. Don haka ko shakka babu ba za su tsira daga wannan 'shiri na ɗaukar fansar' ba.

Yaƙi dai ba abin so ba ne, babu wani mai hankalin da zai ƙirƙiri yaƙi ko kuma fatan faruwarsa, wannan kuma wani lamari ne da jami'an Iran suka sha bayyana shi, to amma fa kashe mutum kamar Ƙasim Sulaimani, shi ma a irin wannan yanayi sannan kuma cikin nuna girman kai irin wanda shugaban Amurka, Trump, ya nuna, ba abu ne da za a iya amincewa da shi ba.

Ko shakka babu wanda yake bibiyan lamurran da suke gudana a Iran ya san cewa irin wannan ranar da kuma wannan lokacin wani lamari ne da Iran ta jima tana shiri don tinƙararsa….ko shakka babu nasara kuwa tana tare da mai gaskiya.