A+ R A-
01 April 2020

A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro

A ɗan gajeren jawabin da ya gabatar 'yan awowin da suka gabata, shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa sakamakon harin mayar da martani da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran suka kai wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar Iraƙi a daidai lokacin da wasu majiyoyin labarai na iran da Iraƙin suke nuni da cewa wani adadi mai yawa na sojojin Amurkan sun halaka sakamakon wannan harin.

Ala kulli hal ba abu ne mai sauƙi cikin ɗan wannan ƙaramin lokaci a iya tabbatar da irin hasarar da sojojin Amurkan suka fuskanta yayin wannan harin da aka kai sansanin sojin saman Amurkan na Ain al-Asad musamman idan aka yi la'akari da irin yadda Amurkawan suka kulle wajen da hana kowa shiga wajen ballantana a tabbatar da abin da ya faru. To amma akwai wasu abubuwa da za su iya sanya mu sanya shakku da kuma sanya alamun tambaya kan wannan ikirari na shugaban Amurkan wanda yayi ƙaurin suna wajen 'ƙarya' da faɗin abubuwan da ba haka suke ba, sai daga baya su tabbata lalle ba hakan su ke ba. Ɗaya daga cikin misalan hakan kuwa shi ne abin da ya fadi a 'yan watannin baya na cewa Amurkan ta harbo wani jirgin sama mara matuƙi na Iran a matsayin mayar da martani ga kakkaɓo jirgin sama mara matuƙi mai matuƙar muhimmanci na Amurka 'RQ-4A Global Hawk BAMS-D' da dakarun kare juyin juya halin Musulunci IRGC suka yi inda yayi alƙawarin nuna jirgin amma shiru kake yi kamar an shuka dusa. Daga baya dai Iran ta nuna wannan jirgin da Trump yake cewa sun kakkaɗo ɗin yana nan ƙalau ɗinsa.

To ko ma dai harin na Iran bai kashe wani sojan Amurka ba, kamar yadda Trump ɗin yace, amma dai shi da kansa ya tabbatar da cewa lalle an kai harin kuma ya lalata wasu ɓangarori na sansani shi kansa hakan wata gagarumar nasara ce da Iran ta samu wanda kuma ke tabbatar da cewa jagororin Iran suna da ƙarfi da jaruntakar ɗaukar irin wannan mataki na kai hari kan mafi girman sansanin sojin Amurka a Iraƙi saɓanin abin da wataƙila wasu suke faɗi kuma suka nuna wa Trump ɗin na cewa Iran ba za ta taɓa yin wannan tarar aradu da ka ɗin ba.

Abu na biyu kuma shi ne wannan harin ya tabbatar da ƙarfin da Iran take da shi na kai hari duk wani sansani na Amurka, matuƙar dai za ta iya kai hari wannan sansanin wanda Amurkan ta kashe maƙudan kudaden wajen gina shi da kuma sanya mafiya kyawu da ƙarfin na'urorin kariya a gare shi (insha Allah a nan gaba za mu yi bayani kan wannan sansanin da kuma irin makaman da Iran ta yi amfani da su wajen kai harin).

Abu na uku kuma shi ne Iran ta sanya Trump ma'abocin girman kai rusunawa, duk wanda ya kalli jawabin da yayi ɗin da yanayinsa zai iya tabbatar da wannan batu.

Wannan dai mafari ne na mayar da martanin Iran, Amurkan ta saurari abubuwan da za su biyo baya, wataƙila ma hakan ne ta sanya Trump ɗin ja da baya daga barazanarsa ta mayar da martani ba tare da ɓata lokaci ba a kan Iran matuƙar ta kai hari kan sojojinsa. Don kuwa a fili yake cewa da Amurka ta mayar da martanin, wanda da man shi ne abin da Iraniyawa ɗin suke fatan gani, to da kuwa hare-haren da za su fuskanta nesa ba kusa ba za su fi wanda aka kai musu daren jiyan.

Ala kulli hal, Iran da kawayenta dai sun shata layi, abin da suke so shi ne Amurka ta fice daga yankin, wanda shi ne kawai abin da zai yi daidai da fansar jinin shahid Ƙasim Sulaimani. Idan ba haka ba kuwa to ta shirya fuskantar mayar da martani daga Iran da kawayen na ta.