A+ R A-
01 July 2022

Saƙon Jagora Imam Khamenei Ga Amurkawa: 'Ido A Madadin Ido"

A bugunta na 246, mujallar "Khatte Hezbollah" ta buga wata maƙala mai sunan "Ido A Madadin Ido" (Eye For An Eye) tana mai ishara da jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi yayin ganawa da firayi ministan ƙasar Iraƙi a kwanakin baya inda ya sake jaddada aniyar Iran na ɗaukar fansar jinin Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani da Amurkawa suka zubar a ƙasar Iraƙin.

A ranar Talata 21/07/2020 ne dai Ayatullah Khamenei ya gana da firayi ministan ƙasar Iraƙi Mustafa Kazimi wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ci gaba da ziyarar da yake yi a Iran inda Jagoran ya sake jaddada aniyar Iran ta ɗaukar fansar jinin Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani (tsohon kwamandan rundunar Ƙudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran - IRGC) da Amurkawa suka zubar a ƙasar Iraƙi. A yayin wannan ganawar dai Jagoran ya isar wa Amurkawan a wani saƙo mai muhimmanci wanda shi ne cewa: "Jamhuriyar Musulunci ta Iran har abada ba za ta taɓa mantawa da wannan lamarin ba, sannan kuma ko shakka babu za ta mayar wa Amurkawa da martani daidai da wannan aiki na su."

Wannan batun dai shi ne abin da mujallar ta fi ba shi muhimmanci a wannan bugu nata. Ga abin da ake cewa:

Ranar Juma'a 13 ga watan Dey 1399 (3 ga watan Janairun 2020), ƙarfe 1:20 na safe, babban titin da ke kai wa ga filin jirgin saman Bagadaza ya shaidi faruwar wani aikin ta'addancin da ya buɗe sabon shafi na abubuwan da ke faruwa a yankin Yammacin Asiya (Gabas ta tsakiya). Ko shakka babu labarin kisan gillan da aka yi wa Janar Hajj Ƙasim Sulaimani, ba wai kawai al'ummar Iran ba, ana iya cewa hatta al'ummomin yankin da ma duniya ba ki ɗaya, sun shiga cikin damuwa nesa ba kusa ba. Saboda wani labari ne mai ban mamaki wanda kuma ba a yi tsammanin faruwarsa ba. Babu wani da ke tunanin cewa za a kai hari kan wannan mutumi mai girman matsayi a zukatan al'ummar Iran shi ɗin ma a yayin da yake a matsayin 'baƙon' wata ƙasar makwabta sannan a zubar da jininsa haka.

Bayan 'yan wasu 'yan sa'oi da aikata wannan ɗanyen aikin, sai ga ma'aikatar tsaron Amurka PENTAGON ta fitar da wata sanarwa inda ta ce shugaban ƙasar Amurka (Donald Trump) da kansa ne ya ba da umurnin aikata wannan aikin, kuma shi ma da kansa shugaban Amurkan daga baya ya sanar da ɗaukar alhakin wannan ɗanyen aiki maras tamka. A ɗaya ɓangaren kuma bayan shahadar wannan babban kwamandan Musulunci a hannun ashararan duniya, zukatan al'ummar Iran sun sosu ainun waɗanda a lokacin ba abin da suke jira face abin da zai kwantar musu da hankali.

Ba da jimawa ba kuwa wannan 'kwanciyar hankalin' ya zo cikin wani saƙon ta'azziya da Jagora Imam Khamenei ya fitar inda ya ce: "Ɗaukar fansa mai tsanani tana jiran waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki, waɗanda hannayen su ke jiƙe da jininsa da kuma jinin sauran shahidan wannan lamarin dumu-dumu.". Fitowar miliyoyin al'ummomin Iran da Iraƙi kan tituna, wata alama ce da ke nuni da irin fatan da suke da shi na ganin an ɗau wannan fansar kuma hakan shi ne abin da ke cikin zukata da tunanin masoyan Hajj Ƙasim Sulaimanin.

To sai dai wannan ɗaukar fansar ba lamari ne na lokaci guda ba, face dai wani lamari ne mai matakai waɗanda suka yi daidai da hankali kana kuma cikin tsari da har yanzu ana cikin da'irar aiwatar da su ne:

 

Matakin Farko. Wannan Wani Ɗan Ƙaramin Bugu Ne, Asalin Ɗaukar Fansar Wani Abu Ne Na Daban

 

Bayan kwanaki shida (da faruwar wannan ɗanyen aikin), tun da jijjiɓin safiyar 19 ga watan Dey (9 ga watan Janairun), ruwan makamai masu linzamin da (dakarun IRGC) suka yi a kan sansanin Ainul Asad, wanda masana harkokin soji suke gani a matsayin sansanin sojin Amurka mafi muhimmanci a yankin nan, ya zamanto kanun labaran kafafen watsa labaran duniya. 'Yan sa'oi bayan wannan harin ɗaukar fansar, Jagoran juyin juya halin Musulunci, a yayin wata ganawa da yayi da mutanen garin Ƙum da aka watsa kai tsaye ta kafafen watsa labarai, ya sanar da cewa wannan wani ɗan ƙaramin bugu ne da aka yi wa Amurkawa, amma asalin ɗaukar fansar ita ce ficewar sojojin Amurkan daga yankin.

Duk da cewa shugaban ƙasar Amurkan, a ƙōƙarinsa na ƙasƙantar da muhimmancin harin, ya bayyana cewar babu wata hasara mai yawa da waɗannan hare-hare suka haifar wa sansanin sannan kuma babu wani daga cikin sojojin da suke wajen da ya sami rauni, amma a hankali a hankali sai labarurruka suka dinga fitowa dangane da hasarar da sojojin Amurkan suka yi a yayin hari, don kuwa babu yadda za su iya ɓoye haƙiƙanin abin da ya farun.

Har ila yau a jawabin da ya gabatar yayin huɗubar sallar Juma'a a birnin Tehran, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ƙarin haske dangane da wannan hari da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka kai inda ya ke cewa: "Harin soji ne mai tasirin gaske, to amma abin da ya fi haka muhimmanci shi ne cewa hakan wani hari ne kan haiba da kuma tinƙahon Amurka….wani hari ne ga girman kan Amurka, wanda babu wani abin da zai iya cike giɓin da hakan ya haifar.

 

Mataki Na Biyu: Ɗaukar Fansar Tana Zuwa

 

A wannan karon a ranakun ƙarshe-ƙarshe na watan Tir na 1399 (July 2020) wani 'baƙo' ya iso Iran. Wannan baƙon kuwa shi ne Mustafa Kazimi, wanda bayan rikice-rikice na tsawon lokaci aka zaɓe shi a matsayin firayi ministan ƙasar Iraƙi, wanda ya kawo ziyarar aiki Iran da kuma ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci. A yayin wannan ganawar Jagoran yayi amfani da kalmar "Ɗaukar Fansa" yayin da yake magana kan kisan gillan da sojojin Amurka suka yi wa Janar Sulaimani a Iraƙin inda ya ce: "Sun kashe baƙonku a cikin ƙasar ku sannan kuma a fili suka ɗauki alhakin hakan…. Jamhuriyar Musulunci ta Iran har abada ba za ta taɓa mantawa da wannan lamarin ba, sannan kuma ko shakka babu za ta mayar wa Amurkawa da martani daidai da irin irin wannan aiki da ta aikata (ɗaukar fansa)."

Masana harkokin soji suna bayyana kalmar 'ɗaukar fansa' a matsayin mafi girman alama da ke nuni da matsayin ƙarfin (da wata ƙasa za ta kai) da ke sanya masu ƙoƙarin wuce gona da iri (kanta) sake tunani sosai wajen aikata abin da suka aikata da ya sa aka ɗau wannan fansa a kansu. Tabbas ɗaukar fansa ko kuma mayar da irin wannan martanin ba wani baƙōn abu ba ne a wajen Iran, kuma tsawon waɗannan shekaru arba'in na nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar Iran Jagoran ya sha amfani da irin wannan kalmar da kuma aiwatar da hakan a aikace. Ga wasu daga cikin misalan hakan:

Mayar da martanin da ɗaliban jami'a mabiya tafarkin marigayi Imam Khumaini suka yi na kame ofishin jakadancin (ofishin leƙen asirin) Amurka a Tehran shekara guda bayan kisan gillan da 'yan amshin shatan Amurka na tsohuwar gwamnatin Shah suka yi wa ɗaliban makarantu da jami'oi na Iran a ranar 13 ga watan Aban 1357 (4, Nuwamban 1978), shirin gwamnatin Iran na mayar wa Saudiyya da kakkausan martani sakamakon hatsari mai sosa rai da ya faru a Mina a yayin aikin hajji na shekarar 2015, kamewa da tsare jirgin ruwan Birtaniyya biyo bayan tsare jirgin ruwan Iran da ta yi, kakkaɓo jirgin saman yaƙin Amurka maras matuƙi biyo bayan keta hurumin sararin samaniyyar ƙasar Iran da yayi, waɗannan kaɗan ne daga cikin irin mayar da martani da ɗaukar fansar da Iran ta yi a kan waɗanda suka wuce gona da iri a kanta wanda ko shakka babu hakan ya ƙara ƙarfafa yanayin tsaron ƙasar (da kuma jan kunnen masu son wuce gona da iri).

Kamar yadda aka sha bayyanawa, a dukkanin fito-na-fiton da ta yi hatta da Amurka da Saddam, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taɓa zama mai fara kai hari kan kowa ba, ta kan kare kanta ne bayan harin da aka kawo mata, duk kuwa da cewa tana mayar wa maƙiya da kakkausan martani. Toh a wannan karon ma dai mayar da irin wannan martanin da kuma ɗaukar fansa tana nan zuwa, wanda ko shakka babu irin wannan martani da ɗaukar fansa za su zamanto sun yi daidai da irin ɗanyen aikin da maƙiya ɗin suka aikata ne, wato 'Ido A Madadin Ido' haka nan 'Rai A Madadin Rai'. Sai dai bai kamata a mance da cewa irin wannan mayar da martanin, wani ɓangare ne na 'ɗaukar fansa' kan Amurka da (Jagoran ya faɗi cikin saƙōnsa da muka kawo a sama) wanda manufarta ta ƙarshe ita ce fatattakar Amurka daga yankin Gabas ta tsakiya.