
Yadda ‘Isra’ila’ Ta Faɗa “Tarkon Tsaka Mai Wuyar Iran Da Hizbullah”
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Sharhi
- Hits: 3839

Sakamakon ci gaba da zaman ɗar-ɗar ɗin da ke faruwa a Isra’ila musamman kan iyakanta da ƙasar Labanon, sanannen shafin watsa labaran nan na Amurka, Business Insider yayi ƙarin haske kan irin tsaka mai wuyan da sahyoniyawan suke ciki sakamakon irin ƙarfin da ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon take ci gaba da yi.
A cewar shafin, Hizbullah ɗin ta kafa wata tunga ta tsaron kai a kudancin Labanon inda take da ‘rokoki da makamai masu linzami sama da 150,000 da suke fuskantar Isra’ilan. Shafin ya ci gaba da cewa a wannan makon Isra’ilan ta tura zaratan sojojinta zuwa arewacin ‘ƙasar’ (kan iyakar ‘Isra’ilan’ da Labanon) don ƙara ƙarfafa wannan yanki da ke cikin yanayin zaman ɗar-ɗar. Jami’an Isra’ilan dai sun bayyana wannan mataki a matsayin mafi girma da muhimmancin ƙarfafa sansaninsu da suka yi cikin shekarun baya-bayan nan biyo bayan tsoron da suke ciki na yiyuwar Hizbullah za ta ƙaddamar da wasu hare-haren (ɗaukar fansar kashe mata wani sojanta da Isra’ilan ta yi a ƙasar Siriya).
Shafin ya ƙara da cewa wannan yanayin yana nuni da irin tsaka mai wuyan da Isra’ila take ciki ne sakamakon irin wannan ƙarfi da Hizbullah ɗin ta yi a yankin, inda ta ce: “A wajen Isra’ila dai wannan ƙarin ƙarfin (na Hizbullah) wata barazana ce da ba za a iya amincewa da ita ba, amma kuma wacce ba za a iya kawar da ita ba face sai an yi hasarar rayuka da dukiya, wacce kuma (‘Isra’ilan) ba a shirye take ta yi hakan ba”.
Isra’ila dai ta kai hare-hare da dama a sansanonin Hizbullah a Siriya da Labanon tun bayan ɓarkewar yaƙin ƙasar Siriya shekaru takwas ɗin da suka gabata. Kasantuwar Hizbullah a Siriya don taimakawa gwamnatin ƙasar faɗa da ta’addanci, hakan ya sanya kan iyakan Labanon (da Isra’ila) ya yi shiru, to sai dai kuma in ji shafin akwai yiyuwar kawo ƙarshen wannan shirun cikin kwanakin nan.
Shafin ya jiyo wani tsohon jami’in gwamnatin Isra’ilan wanda ba ya so a ambaci sunansa yana cewa ba abu ne da za a iya amincewa da shi ba a ce Hizbullah ta mallaki sama da rokoki da makamai masu linzami 150,000 da suke fuskantar Isra’ila. Jami’in ya ci gaba da cewa: “Hizbullah ta ɗana mana mummunan tarko a arewaci, sannan ni kuma ban ga yadda za a magance wannan matsalar ta fuskar soji ba tare da an samu gagarumar hasara ba”.
Har ila yau jami’in ya ci gaba da magana dangane da “shekaru talatin na ɓoyayyen shirin (Hizbullah) na samar da sansanonin harba rokoki da makamai masu linzami a dukkanin kudanci da gabashin ƙasar Labanon da ana iya cewa ba za a iya kawo ƙarshensu ta hanyar hare-haren jiragen sama ba”. Jami’in ya ci gaba da cewa: “Кungiyar za ta iya ruwan gomomi ko kuma ma ɗaruruwan rokoki cikin Isra’ila ba tare da an iya tare su ba.
Har ila yau jami’in ya ce: ‘Sojojin Isra’ila ba za su iya shiga Labanon don kawo ƙarshen harba waɗannan rokoki da makamai masu linzamin ba tare da sun fuskanci hasara ta siyasa da tattalin arziki ba”. Don kuwa a cewarsa: “Aiwatar da irin wannan kutsen tana buƙatar mamaye Labanon da tura sojoji cikin ‘tungar’ Hizbullah don tarwatsa cibiyoyin harba waɗannan rokoki da makamai masu linzami a daidai lokacin da kuma suke gumurzu da dakarun ƙungiyar, wanda ya ce: “Hakan zai haifar da gagarumar hasarar rayukan (sojojin Isra’ilan) da suke fagen dagan sannan kuma da wuya a ma yi tunanin za a iya dakatar da su cikin makonni”.
Shi kuwa a nasa ɓangaren wani tsohon jami’in leƙen asirin sojin Isra’ila da shafin ya ji ra’ayinsa ya bayyana cewar: Hizbullah ta shafe shekaru 30 tana shirya wata ƙarfafaffiyar tungar kariya wacce Isra’ila ba za ta taba tunanin hakan a shekarun 1970 ba.
Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙuƙuwa biyu a kan Labanon a shekarun 2000 da 2006, inda a dukkanin biyu ta ɗanɗana kuɗarta a hannun dakarun Hizbullah ɗin da kuma tilasta mata ja da baya. Shafin ya ƙara da cewa: A shekara ta 2006 Isra’ila ta fahimci cewa Hizbullah ta mayar da mafi yawan yankunan Kudancin Labanon zuwa wasu sansanonin soji da ba za a iya ganinsu ta sama ba.
Jami’in leƙen asirin sojin na Isra’ila ya ci gaba da cewa: Hizbullah sun tsara yanayin ƙarfinsu na soji da mahanga guda: matuƙar dai rokoki suna ci gaba da sauka a Isra’ila sannan kuma Isra’ilawan suna ci gaba da ɓuya a cikin mafakar ƙarƙashin ƙasa, to kuwa Hizbullah ta yi nasara”. Jami’in wanda Business Insider ɗin ta ce ya taɓa aiki a kudancin Labanon a lokacin mamayar da Isra’ila ta yi wa kudancin Labanon a shekarun 1978 da 2000 ya ci gaba da cewa: “Shugabannin Hizbullah suna ganin za su iya jurewa wahalhalun yaƙin sama da na Isra’ila, kuma mai yiyuwa suna da gaskiya”.
Jami’in ya ci gaba da cewa: “Wani tarko ne da Iraniyawa suka ɗana mana, sannan kuma ina tsoron haka shugabanninmu suka shafe waɗannan shekaru talatin ɗin suna yawo cikin wannan tarkon ido rufe”.
Waɗannan bayanai na tsoffin jami’an soji da leƙen asirin Isra’ilan dai suna nuni da irin tsaka mai wuyan da sahyoniyawan suke ciki ne wanda suke ganin babu wani abin da zai iya fitar da su daga wannan halin da suke ciki face ‘tattaunawa da Iran’, wanda a ɓangaren Iran wannan ba mafita ba ce don kuwa babu wani batun tattaunawa tsakanin su Sahyoniyawa, mafita ɗaya a cewar Iraniyawan ita ce su fice daga yankunan da suka mamaye su koma inda suka fito.