
Mece Ce Manufar Tarzomar Da Ke Faruwa A Labanon?
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Sharhi
- Hits: 3085

A daidai lokacin da hankulan yawancin al’ummar ƙasar Labanon suka koma ga batun fashewar da ta faru a tashar bakin ruwan Beirut da kuma gano musabbabin hakan da kuma hukunta waɗanda suke da hannu ciki, sai dai kuma tarzoma da ƙone-ƙonen da wasu suka tayar kuma ya ke ci gaba da faruwa a birnin na Beirut, na nuni da ƙoƙarin da wasu mutanen suke yi ne na jirkitar da tafarkin binciken da ake gudanarwa don kar a kai ga gano haƙiƙa. A ɓangare guda kuma a daidai lokacin da mafi yawan al’ummar ƙasar suke buƙatar a gudanar da bincike na cikin gida ƙarƙashin jagorancin gwamnatin ƙasar dangane da wannan lamarin, wasu kuma, waɗanda daga dukkan alamu su ne masu ruwa da tsaki cikin waɗannan zanga-zangogi da suke faruwa, dukkanin ƙoƙarinsu shi ne shigo da ƙasashen waje cikin lamarin binciken da kira zuwa ga gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa. Masu adawa da gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa ɗin dai suna cewa ne babu wani abin da hakan zai haifar in ban da jirkitar da haƙiƙa da kuma hana gano da kuma hukumta waɗanda suke da hannu cikin lamari, kamar yadda ya faru a baya a ƙasar cikin lamurra daban-daban musamman batun kisan gillan da aka yi wa tsohon firayi ministan ƙasar Rafiq Hariri wanda har yanzu, bayan shekaru sha biyar, babu wani abin a zo a gani na haƙiƙa da aka cimma.
Abubuwan da masu zanga-zangar suka dinga gudanarwa, wanda daga dukkan alamu an tsara su ne da nufin tabbatar da rashin tsaro a birnin, da suka haɗa da kai hare-hare kan ma’aikatun gwamnati, da mai yiyuwa suna ɗauke da wasu bayanai ko takardun da za su iya sanya a gano waɗanda suke da hannu cikin wannan ɗanyen aikin, suna nuni ne da ƙoƙarin waɗannan mutanen na haifar da yanayin da zai hana isa ga haƙiƙanin waɗanda suke da hannu cikin wannan ɗanyen aikin da ya faru na fashewar waɗannan sinadarai a tashar bakin ruwan na Beirut.
A ɓangare guda kuma ana iya sanya waɗannan zanga-zangogin da suke ci gaba da faruwa da kuma ayyukan lalata dukiyar gwamnati da ta al’umma cikin jerin zanga-zangogi da zaman ɗar-ɗar ɗin da ke faruwa a Beirut ɗin tsawon watannin da suka gabata da kuma taken da wasu suke ta rerawa irin su wajibcin kwance ɗamarar ƙungiyar Hizbullah da kuma rashin tsoma baki cikin harkokin da suke gudana a yankin musamman a ƙasar Siriya (duk dai Hizbullah ɗin ake nufi) da kuma batun da a halin yanzu wasu suke ta yi na miƙa binciken fashewar da ta faru ɗin zuwa ga bincike na ƙasa da ƙasa, daga ƙarshe kuma su cimma burinsu na kifar da gwamnatin Hassan Diab ta ƙasar wacce daga dukkan alamu hakan na daga cikin manyan manufofin dukkanin waɗannan tashin tashina da ke faruwa a ƙasar cikin waɗannan watanni.