A+ R A-
08 December 2023

Sabon Shirin Amurka Na Nuna Damuwa Kan Shirin Makamai Masu Linzami Da Jirage Marasa Matuƙa na Iran

Jaridar World Street Journal ta Amurka ta ba da labarin cewa Amurka tana shirin sanya sabbin takunkumi wa Iran saboda irin ƙarfi da ƙwarewar da ƙasar take da ita a ɓangaren makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuƙa da ake iya kai hare-hare da su. Hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da dukkanin ƙoƙarin da Amurkan ta yi wajen shigo da wannan batu cikin tattaunawar nukiliya da ake yi da Iran a birnin Vienna ya ci tura sakamakon tsayawar da Iran ta yi ƙyam kan cewa waɗannan batutuwa guda biyu wasu lamurra ne da suka shafi tsaron ƙasarta da ba za ta taɓa tattaunawa da wata ƙasa kansu ba.

Ko shakka babu masana harkokin yau da kullum kana masu sanya ido kan abubuwan dake gudana a yankin Gabas ta tsakiya cikin shekarun baya-bayan nan sun bayyana cewar wannan mataki da Amurka ta sanar ba wani abu ne da ya zo musu da ban mamaki ba bisa la’akari da irin ci gaba da shan kashi da siyasar Amurka take fuskanta a yankin Gabas ta tsakiya wanda take ganin ko shakka babu akwai hannun Iran ɗin cikin hakan.

Ga misali sanarwar da Amurkawan suka yi a baya-bayan nan na cewa a karon farko tun bayan yaƙin Vietnam sun rasa irin ƙarfin da suke da shi na sama a yankin nan, suna masu cewa wannan rashi da suka fuskanta hakan zai amfani Iran ne, wani lamari ne da ke nuni da hakan da kuma irin damuwar da suke ciki dangane da irin ƙarfi da kuma tasirin da Iran take samu a yankin. Hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da, kamar yadda muka faɗi a baya, Iran take ci gaba da tsayawa kan matsayarta na cewa za ta ci amince da ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya ne ba tare da an shigo da wani abu da ya haɗa da ƙarfin da take da shi na makamai masu linzami da kuma tasirin da take da shi a yankin ba, wanda kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci na ƙasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da ma sauran jami’ai da cibiyoyi na ƙasar suka ce waɗannan wasu lamurra ne da ba za a tattauna da wata ƙasa kan su ba.

Ko shakka babu amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuƙa na Iran a yankuna daban-daban na yankin Gabas ta tsakiya ko dai kai tsaye ko kuma ta wasu hanyoyi misali musayen ƙwarewar hakan, yana a matsayin wata gagarumar nasara ga Iran ɗin da kuma ƙawayenta na sansanonin gwagwarmaya da suke yankin. Don kuwa harba kimanin makamai masu linzami 4000 da dakarun gwagwarmayar Falastinawa suka yi zuwa cikin ‘Isra’ila’ tsawon kwanaki 11 na yaƙin baya-bayan nan da Sahyoniyawa suka ƙaddamar kan al’ummar Gaza, haka nan da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da dakarun Yemen suke amfani da su kan masu wuce gona da iri na daga sojojin Saudiyya da ƙawayenta a ɓangarori daban-daban na Yemen ɗin kai hatta ma har zuwa cikin Saudiyyan bugu da ƙari kan makamai masu linzami da ƙungiyar gwagwarmayar ƙasa Labanon (Hizbullah) ta mallaka waɗanda a kullum suke hana ‘Isra’ila’ barci da dai sauransu, dubi cikin waɗannan lamurra ko da kuwa a gurguje ne za su iya fahimtar da mutum irin halin damuwa da tsaka mai wuya da Amurkan take ciki da kuma dalilanta na komwa da batun barazana  ta hanyar ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumi.

Yayin da muka kalli wannan barazanar ta Amurka a kan Iran tare da matsayar baya-bayan nan ta sakataren wajen Amurka Antony Blinken yayin da yake magana kan abin da ke faruwa a ƙas ɗin inda ya ce tattaunawar da ake yi da Iran ba zai ci gaba da wanzuwa har abada ba da kuma cewa a halin yanzu dai komai yana hannun Iran ne…za mu ga cewa wannan wani lamari ne wanda Iran ta jima da sanin faruwar hakan kuma tuni ta shirya wa faruwarsa.

To sai dai abin ban dariya cikin hakan shi ne irin yadda Amurkan ta ke tsayawa kan batun cewa Iran ta karya yarjejeniyar nukiliyan da kuma ƙoƙarin sanya ta ta amince da wasu sabbin sharuɗɗan da take neman gindaya mata.

A fili yake cewa Amurka ita ce wacce ta fara yin karen tsaye ga yarjejeniyar ta nukiliya da kuma take wa Iran haƙƙinta ta hanyar ficewar da ta yi daga cikin yarjejeniyar a 2018 shekaru biyu da wani abu bayan an cimma ta wato a shekara ta 2015, wannan wani lamari ne da babu kokwanto cikinsa. To amma a halin yanzu Amurkan tana ƙoƙari ne wajen mayar da wani ɗan ƙaramin ɓangare na wannan haƙƙi na Iran, shi ɗin ma bisa matsin lamba da barazana da dai sauransu wanda ko shakka babu tana yin hakan ne don cimma mafi girman abin da za ta iya cimmawa a hakan wanda ko shakka babu wannan abin kuwa shi ne manufofinta da kuma na haramtacciyar ƙasar Isra’ila a yankin.

Ala kulli halin, ko ma dai mene ne sanya sabbin takunkumi kan Iran wani lamari ne wanda da wuya ya haifar wa Amurkawan ɗa mai ido, wato ba abu ne da zai kai su ga cimma manufar da suke son cimmawa ba, don kuwa abubuwan da suka faru a baya na irin waɗannan  takunkumin da Amurkan ta sanya wa Iran ya isa ya tabbatar da hakan. Da dai Amurkawan za su ji shawara da dai sun bi lamarin a hankali ta hanyar ba wa kowa haƙƙinsa cikin yarjejeniyar ta nukiliya a wuce wajen.