A+ R A-
29 February 2020

Sakon Jagora Ga Taron Tsayar Da Salla Karo Na 22 A Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar wayar da kan al’umma dangane da muhimmancin salla da kuma yadda ake yinta wani nauyi ne da ke wuyan muminai baki daya, inda ya kirayi masana da malamai da masu fadi a ji da su yi kokari wajen sauke wannan nauyi.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya aike wa mahalarta taron tsayar da salla karo na 23 da aka gudanar a lardin Lorestan a yau Laraba (4-8-2013) wanda wakilin Jagora na lardin Hujjatul Islam wal muslimin Mir Imadi ya karanta.

Abin da ke biye fassarar wannan sakon ne:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Yayin da ya ke siffanta muminai, Alkur’ani mai girma ya bayyana tsayar da salla a matsayin daya daga cikin manyan ayyuka da nauyin da ke wuyan muminai inda ya ke cewa: Wadanda suke idan Muka ba su iko a bayan kasa, sai su tsayar da salla…(Suratul Hajj 22:41).

Cikin aiki na daidaiku, wannan nauyi yana nufin yin salla yadda take ne, sannan a jama’ance kuwa yana nufin kwadaitar da yinta sannan kuma cikin jam'i.

Ma’anar hakan ita ce yin salla cikin nitsuwa da tattaro zuciya waje guda. Mai salla ya dinga kallon sallar a matsayin ‘wani wajen ganawa da Ubangiji’, inda zai dinga magana da Ubangijinsa, da kuma jin cewa lalle yana gabansa ne. Gwargwadon yadda za su iya, kamata ya yi masu salla su dinga yinta a masallaci sannan kuma cikin jam'i.

Duk wani kokari wajen tabbatar da sallar jam'i da kuma bayanin muhimmancin da ke cikin hakan da kuma saukake yiyuwar hakan, yana a matsayin kwadaitar da salla ne.

Masana da masu bakin magana, ta hanyar maganganu da kuma alkalumansu; haka nan ma’abota kafafen watsa labarai da mimbarori na jawabi; su ma ta hanyar fasahar da suke da ita; hakan kuma jami’an cibiyoyin da abin ya shafa, kowane gwargwadon yanayin aikinsa, za su iya sauke wannan nauyin.

Karancin masallatai a garuruwa da kauyuka; rashin wajajen salla a wajajen tarurruka haka nan da filayen wasanni da kasuwanni na zamani da tashoshi da makamantansu; rashin kula da lokutan salla yayin tafiya mai nisa; rashin ba da muhimmanci yadda ya kamata ga batutuwan da suka shafi salla cikin littafan darasi a makarantu; rashin kula da tsafka da kiwon lafiya cikin masallatai; rashin kula da lamurran da suka shafi al’umma da kuma kulla alaka da muminai daga wajen limaman masallatai; da dai sauran matsaloli irin wadannan, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke bukatar gagarumar himma wajen kawar da su da kuma bayyanar da alamun tsayar da salla cikin al’ummarmu. Insha Allah.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah.

Sayyid Ali Khamenei

11 ga watan Shahrivar 1392.

(2, Satumba, 2013)

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook