A+ R A-
28 February 2020

Imam Khamenei Yayin Ganawa Da ‘Yan Majalisar Kwararru: Lalle Amurka Za Ta Sha Kashi A Siriya

A safiyar yau Alhamis (5-9-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da sauran ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci (ta Iran). A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen wannan ganawar Jagora ya kirayi dukkanin jami’ai da sauran masu fadi a ji a bangarori daban-daban na gwamnatin Musulunci ta Iran zuwa amfani da hikima da hangen nesa cikin lamurran da suke faruwa a cikin gida da kuma duniya don daukan matsayar da ta dace inda ya ke cewa: Yayin daukar matsaya, wajibi ne jami’an su yi la’akari da abubuwa guda uku: ‘koyarwar juyi da manufofinsa’, siyasa ta gaba daya ta tsarin Musulunci da kuma hakikanin abin da ke a kas.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana dubi na gaba daya sannan kuma ta kowane bangare cikin lamurran da suke faruwa a matsayin lamarin da ya zama wajibi a yi la’akari da shi, daga nan sai ya ce: Daya daga cikin irin wadannan lamurran shi ne yadda aka kafa tsarin Jamhuriyar Musulunci a kasar Iran cikin irin mummunan yanayin da duniya take ciki da kuma yadda a lokacin aka kama hanyar riko da akidar abin duniya, wanda hakan lamari ne da ya yi kama da mu’ujiza.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin kiyayya da gabar da makiya suka nuna wa tsarin Musulunci na Iran tun daga farkon nasarar juyin har zuwa yanzun nan, Jagoran ya bayyana cewar: Babban dalilin dukkanin irin wadannan kiyayyar shi ne Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Duk da cewa shekara da shekaru kenan kasashen yammacin Asiya suke karkashin mulkin mallakan ma’abota girman kan duniya, to amma a irin wannan yanayin ne aka samu bayyanar farkawa ta Musulunci wanda hakan sabanin abin da ma’abota girman kan suke so ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Tunani da wasu suke yi na cewa an kawo karshen wannan farkawa ta Musulunci, lalle ne kuskure ne. Don kuwa wannan farkawa ta Musulunci ba wai wani lamari na siyasa kawai ba ne, ta yadda zuwa wasu mutane ko kuma kawar da su, shi kenan ya zo karshe ba ne. A’a, farkawa ta Musulunci, wani yanayi ne na fadaka, yarda da kai da kuma dogaro da Musulunci wanda yake ci gaba da yaduwa a tsakanin al’ummar musulmi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da a halin yanzu muke ganin yana faruwa a yankin nan, a hakikanin gaskiya mayar da martanin ma’abota girman kai karkashin jagorancin Amurka ne ga wannan farkawa ta Musuluncin.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da kokarin da ma’abota girman kan duniya suke yi wajen magance matsalolin da suka kunno kai a yankin Gabas ta tsakiya don amfanin kansu, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Manufar shigowar ma’abota girman kai masu wuce gona da iri yankin nan ita ce kawar da duk wata gwagwarmayar nuna rashin amincewa da kasantuwarsu. To sai dai kuma ma’abota girman kan sun gagara kawar da wannan gwagwarmayar, kuma a nan gaba ma ba za su iya ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: wannan ita ce ma dai manufarsu dangane da abin da ke faruwa a kasar Siriya na baya-bayan nan wanda suka kirkiro shi ta hanyar fakewa da batun amfani da makamai masu guba. To amma Amurkawa suna kokarin wasa da hankalin mutane da nuna cewa sun shigo cikin lamari ne saboda tausayi da kare hakkokin bil’adama.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa suna wannan ikirari na kare hakkokin bil’adama ne a daidai lokacin da tarihinsu yake da lamurra irin su gidajen yarin Guantanamo da Abu Ghuraib, shiru a lokacin da Saddam ya yi amfani da makamai masu guba a garin Halabja da wasu garuruwa na Iran da kuma kisan gillan da ake yi wa mutanen da ba su ci ba su sha ba a kasashen Afghanistan da Pakistan da Iraki. Babu wani a duniyan nan da zai yarda da cewa Amurkawa suna kare hakkokin bil’adama ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Mu dai mun yi amanna da cewa Amurkawa suna kokarin fadawa tarkon kuskure da za su tabka ne a kasar Siriya, wanda ko shakka babu za su sha kashi.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Duk da shekara da shekaru na makirci da nuna kiyayya, amma a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba wai ma ba ta yi rauni ba ne, face ma dai ta kara samun karfi da matsayi da kuma fadi a ji ne a wannan yankin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Faruwar wasu abubuwa masu bakanta rai bai kamata su zamanto Katanga a gabanmu ba, bai kamata su kawar da mu daga ci gaba da tafarkin da muka rika ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar tafarkin tarihin rayuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) babban misali ne a gare mu a wannan bangaren inda ya ce: Imam Khumaini (r.a) dai bai rufe idanuwansa daga abubuwa na hakika da suke faruwa ba, to amma bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da tafiya a kan tafarkin da ya rika.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Imam Khumaini (r.a) shi ne dai mutumin da ya kira haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin wata cutar kansa da wajibi ne a kawar da ita, babu wani lokaci da ya taba yin takiyya dangane da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Haka nan Imam Khumaini (r.a) bai taba boye matsayarsa kan Amurka da ashararancinta ba, sannan kuma shi ne ya fadi wannan shahararriya kalmar nan tasa ta cewa “Amurka, ita ce babbar shaidaniya”. Haka nan kuma shi ne dai wanda ya fadi wannan jumla ta cewa: ‘Mamaye ofishin jakadancin Amurka (a Tehran da aka yi) a matsayin juyin juya halin Musulunci na biyu, mai yiyuwa ma ya fi juyin farkon muhimmanci’.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar irin wannan tsayin daka na marigayi Imam Khumaini (r.a) shi ne abin da tabbatar da duga-dugan tsarin Musulunci na Iran.

Yayin da ya ke magana kan abin da a halin yanzu yake faruwa na irin yadda wasu mutane da wasu kasashen suka yi watsi da tafarkin da suke kai saboda kawai su dadada wa ma’abota girman kai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da abin da ke faruwa a kasar Masar inda ya ce: Idan da a ce an ci gaba da rera taken fada da Isra’ila a Masar, sannan kuma ba a rudu da alkawurran Amurka ba, da kuwa babu yadda za a yi a ce an sake dan kama karyan da wulakanta al’ummar Masar daga gidan yari ba, sannan kuma a tura shugaban da jama’a suka zaba zuwa gidan yarin da kuma hukumta shi ba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya yi ishara da siyasa da kuma kokarin da makiya Musulunci suke yi wajen haifar da rikici na kungiyanci da mazhaba a yankin Gabas ta tsakiya inda ya ce: Makiya suna amfani da wasu ‘yan amshin shatansu wajen cimma wannan manufa ta su. Daya daga cikin ‘yan amshin shatan su ne masu kafirta musulmi da sunan ‘yan Sunna, daya dan amshin shatan kuma shi ne wanda ya ke fakewa da sunan Shi’a.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Duk wani ko kuma wata gwamnatin da ta fada tarkon wannan makirci mai girma, to ko shakka babu za su cutar da kungiyoyin Musulunci. Jagoran ya kara da cewa: Wajibi ne malamai da masu fadi a ji na Shi’a da Sunna su yi taka tsantsan, don kuwa rikici tsakanin kungiyoyi da mazhabobin Musulunci, baa bin da zai haifar in ban da haifar da sabon rikici da kuma gafala daga makiyi na asali.

Tun da farko dai sai da shugaban majalisar kwararru ta jagorancin ta Iran Ayatullah Mahdawi Kani ya gabatar da jawabinsa dangane da taron kwanaki biyu da majalisar ta gudanar da kuma irin batutuwan da aka tattauna. Kamar yadda shi ma mataimakin shugaban majalisar Ayatullah Mahmud Hashemi Shahrudi shi ma ya gabatar da wani rahoto kan ayyukan majalisar.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook