A+ R A-
13 July 2020

Jagora Yayin Ganawa Da Limaman Juma’a: Wajibi Ne Musulmi Su Karfafa Kansu Don Tinkarar Makircin Kasashen Yammaci

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar wajibi ne jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, jami’an diplomasiyya da sauran al’umma su sanya ido sosai kan yaudarar da kasashen yammaci da Amurka suke kokarin yi ta hanyar fakewa da batun kare hakkokin bil’adama da kuma fahimtar inda aka sa gaba, idan kuwa bah aka ba, su suna iya yin kuskure wajen bambance tsakanin dabaru da ayyukan abokan gaba.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi yayin ganawarsa da limaman masallatan Juma’a na garuruwa daban-daban na Iran a yau din nan Litinin (9-9-2013) inda ya bayyana sallar Juma’a a matsayin wata ibada mai muhimmanci da kima ta addini da kuma zamantakewa.

Haka nan kuma yayin da ya ke karin haske kan dalilan sanya ido da kallo na hakika ga abubuwan da ke faruwa a duniya da kuma irin fada da tushen Musulunci da kasashen yammaci suke yi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A zamanin mulkin mallaka lokacin da kasashen yammaci suka fadada irin iko na tattalin arziki da siyasa da al’adu da suke da shi a duniyar musulmi, sun yi kokarin nuna wa duniya cewa kasashen yammacin su ne kawai abin koyi saboda irin ci gaba na ilimi da fasaha da suka samu.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A irin wannan yanayin ne da dukkanin kasashen yankin nan ciki kuwa har da Iran suka kasance karkashin ikon kasashen yammaci, kwatsam sai juyin juya halin Musulunci na Iran wanda ya ginu bisa ‘yanci da kuma riko da Musulunci da koyarwa ta Alkur’ani ya yi nasara wanda hakan ba karamar koma baya ba ne ga kasashen yammacin.

Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da tasirin juyin juya halin Musulunci na Iran a duniyar musulmi da kuma irin yadda ya dawo wa al’ummar musulmin mutumcin da suke da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Irin yadda wannan juyi na Musulunci na Iran ya dawo da tunani da koyarwa ta Musulunci a hankali a hankali cikin al’umma, hakan ya daga wa kasashen yammaci hankali. Don haka ne suka kara irin kokari da makirce-makircen da suke kullawa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A halin yanzu yanayin yankin Gabas ta tsakiya da duniyar musulmi ya sauya ta yadda kasashen yammacin suke jin cewa lalle koyarwa da tunani na Musulunci ya sha gabansu, don haka suke yin duk abin da za su iya wajen ganin su cike wannan koma bayan da suka samu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A irin wannan yanayin ne farkawa ta Musulunci ta kunno kai a yankin nan; don haka suka fito da dukkan karfinsu wajen ganin sun yi fada da irin wannan farkawa ta Musulunci da aka samu.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wajibi ne a tsaya kyam wajen tinkarar kasashen yammacin, don kuwa sun tabbatar da cewa babu tausayi cikin zuciyarsu. Sabanin ikirarin kare hakkokin bil’adama da suke yi, zubar da jinin miliyoyin mutane ba wani abin damuwa ba ne a wajensu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana karya da nuna kai a matsayin wasu siffofi da ‘yan siyasan kasashen yammaci suka siffantu da su yana mai cewa: Gaskiyar lamarin dai shi ne cewa kisan kiyashin da ya faru a Hiroshima ko kuma miliyoyin mutanen da suka rasa rayukansu a yakukuwan duniya na daya da na biyu, haka nan da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba a kasashen Pakistan da Afghanistan da Iraki ba wani abu ne da zai daga wa kasashen yammaci hankali ba. A nan gaba ma a duk inda manufarsu ta keta ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aikata irin wannan kisan kiyashin ba. A saboda haka wajibi ne mu kara irin karfin da muke da shi a fagage daban-daban na siyasa, gwamnati, zamantakewa da al’umma.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Nan

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook