A+ R A-
29 February 2020

Jagora Yayi Fatan Sauyin Matsayar Amurka Kan Siriya, Zai Zamanto Sauyi Na Hakika, Ba Tubar Muzuru Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da ya yi da safiyar yau Laraba (11-09-2013) da jami’an aikin hajjin bana, ya bayyana aikin Hajji a matsayin wani lamari mai karfafa al’ummar musulmi a fagagen siyasa, al’adu da kuma kusaci da Allah. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da halin da duniyar musulmi take ciki a halin yanzu da kuma kokarin da makiya suke yi wajen haifar da fitina tsakanin musulmi ta hanyar fakewa da batun mazhaba da kuma irin barazanar da ‘yan mulkin mallaka suke yi wa al’ummar musulmi, Jagoran cewa ya yi: Muna fatan sabuwar matsayar da Amurka ta dauka kan kasar Siriya, za ta zamanto da gaske ne ba yaudara ba sannan kuma za ta zamanto sauyi na hakika daga kura-kuran da ta tafka cikin ‘yan makonnin da suke gabata.

Har ila yau kuma yayin da ya ke bayanin cewa daya daga cikin wajiban aikin Hajji na hakika shi ne mu’amala ta ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi a yayin sauke wannan farali mai girma, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Ma’anar nesantar jidali a lokacin aikin Hajji da Alkur’ani mai girma ya yi magana kansa ta hada har da jidali na fatar baki tsakanin ‘yan’uwa musulmi da kuma nesantar kiyayya ta zuci a tsakaninsu.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu masu karkatacciyar fahimta, ta hanyar fassarar da take cike da kuskure, suna kokarin sanya alamun tambaya kan tarurrukan barranta daga mushrikai da ake yi a lokacin aikin hajj. Alhali kuwa jidali da fada da shirka da kafirci suna daga cikin manya kana kuma tushen koyarwar Musulunci.

Don haka sai Jagoran ya kirayi musulmin duniya da su yi taka tsantsan da makirce-makircen makiya na haifar da sabani da rikici na mazhaba a tsakaninsu yana mai cewa: Makiya al’ummar musulmi da kyau sun fahimci cewa rikicin mazhaba tsakanin musulmi wani lamari ne da zai amfani sahyoniyawa ‘yan share guri zauna. A saboda haka ne ta hanyar kirkiro kungiyoyi masu kafirta musulmi a bangare guda, sannan a bangare guda suka kirkiro wasu kafafen watsa labarai da a zahiri na Musulunci ne kai a wasu lokuta ma na Shi’a, don su rarraba kan al’ummar musulmi da haifar da fitina a tsakaninsu.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Manyan malaman Shi’a cikinsu kuwa har da marigayi Imam Khumaini (r.a) da sauransu a koda yaushe sun kasance masu jaddada wajibcin kiyaye hadin kai a tsakanin musulmi. A saboda haka Shi’anci da aka kirkiro shi saboda haifar da sabani a tsakanin musulmi sannan kuma ake watsa shi ta kafafen watsa labaran London da Amurka, to ba Shi’anci ne na hakika ba.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa daya daga cikin bangare masu muhimmanci na aikin Hajj shi ne samun damar musayen al’adu na Musulunci na hakika a tsakanin musulmi da kuma samun masaniya kan irin ci gaban da musulmi suke samu. Daga nan sai ya ce: Bisa la’akari da yawaitar kafafen watsa labarai masu adawa da gwamnatin Musulunci ta Iran, don haka wajibi ne a kan alhazan Iran su yi kokari wajen gabatar da hakikanin koyarwar Musulunci da Shi’anci da kuma irin nasarorin da gwamnatin Musulunci ta Iran ta samu cikin maganganu da halayensu.

Haka nan kuma a ci gaba da bayanyin irin wutar fitinar da makiya musulmi suke hurawa a kasashen Pakistan, Afghanistan, Iraki, Siriya da Bahrain da sunan Shi’a da Sunna lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wani adadi mai yawa na musulmi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: ‘Yan mulkin mallaka da masu tinkaho da karfi musamman Amurka, ba sa yin kasa a gwuiwa wajen lalata kasashen musulmi da kuma zubar da jinin al’ummomi don dai kawai su cimma haramtattun manufofinsu.

Yayin da ya koma kan barazanar da Amurka take ci gaba da yi wa kasar Siriya kuwa, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Don biyan bukatun yahudawan sahyoniya da manyan ‘yan jari hujja na duniya, wadannan mutanen a shirye suke su take manufofi da kuma hakkokin al’ummomin sauran kasashe na duniya.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan sassautowar da Amurka ta yi kan batun kai wa kasar Siriya hari da kuma fatan cewa hakan ba zai zamanto tubar muzuru ba, Jagoran cewa ya yi: Idan har aka sami hakan, to hakan yana nuni da cewa Amurkan ta dawo daga rakiyar kura-kuran da ta yi ne cikin makonnin da suka gabata.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai za ta ci gaba da sanya ido sosai kan abubuwan da ke gudana a yankin Gabas ta tsakiya.

Kafin jawabin Jagoran sai da Hujjatul Islam wal muslimin Qadhi Askar wakilin Jagoran kuma Amirul Hajji na Iran ya gabatar da jawabi da kuma rahoto kan abubuwan da aka shirya wa alhazan na bana.

Har ila yau shi ma ministan al’adu da shiryarwa ta Musulunci na Iran Malam Jannati ya gabatar da nata jawabin dangane da irin ayyukan da aka gudanar a fagen tabbatar da hadin kai da aiki tare tsakanin cibiyoyin da suke gudanar da aikin hajjin. Kama yadda shi ma shugaban hukumar alhazai ta Iran Malam Auhadi ya gabatar da nasa jawabin inda ya yi karin haske kan abubuwan da aka tanadar wa alhazan na Iran da adadinsu ya kai mutane 64,000 don tabbatar da sun gudanar da aikin hajjin ba tare da fuskantar matsaloli ba.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook