A+ R A-
29 February 2020

Jagora Yayin Ganawa Da Dakarun Kare Juyi: Makiya Suna Fada Da Iran Ne Saboda Riko Da Tsarin Musulunci

A safiyar yau Talata (17-09-2013) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan kwamandoji da sauran jami’an dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran inda ya bayyana cewar: asalin sako da abubuwan masu jan hankula tattare da juyin juya halin Musulunci shi ne nesantar zalunci da rashin yarda da zalunci. A saboda haka wajibi ne a kalli dabi’u da maganganun ‘yan mulkin mallaka karkashin wannan sakon da kuma yin mu’amala da su bisa hakan.

Yayin da yake isar da sakon taya murnarsa ga dakarun kare juyin da kuma sauran al’ummar musulmi dangane da ranar haihuwar Imam Ridha, Imami na takwas (amincin Allah ya tabbata a gare shi), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk da cewa matsayin Imaman shiriya (a.s) ya dara fahimta ta dan’adam da kuma siffantawa ta fatar baki, to amma rayuwar wadannan manyan bayin Allah, darasi ne dawwamamme.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da shekaru 55 na rayuwar Imam Ridha (a.s) da kuma imamancinsa na kimanin shekaru ashirin, Jagoran cewa ya yi: Cikin dan wannan karamin lokacin sannan kuma cikin irin gagarumin takuri na Haruna (Rashid), amma haka Imam Ridha (a.s) ya samu damar yada hakikanin koyarwar Musulunci da tunani na wilayah da koyarwar Ahlulbaiti (a.s) ta yadda gwamnatin kama-karya ta wancan lokacin ta gagara yin fada da hakan, lamarin da ya sanya su kashe shi.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jinjinawa dakarun kare juyin juya halin Musuluncin kan irin gagaruman ayyukan da suka yi inda ya ce: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun shigo fagen gwagwarmaya ne tare da gagarumin imani da kuma akida, inda suka sami damar gudanar da ayyuka hatta a fagagen da ba na aikin soji ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa dakarun kare juyin juya halin Musulunci ba su taba kaucewa daga tafarkin da suka rika ba saboda sauyin da wasu suke maganar an samu a duniya. Jagoran ya ce maganar cewa a halin yanzu duniya ta sauya ba dalili ne da zai sanya a yi watsi da koyarwa da kuma tafarkin da aka rika ba. Don haka ne ya ce: Don kare juyin juya halin Musulunci, wajibi ne a fahimci abubuwan da suke gudana a bangarori daban-daban na duniya.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan tsarin da ma’abota girman kai suka shigo da shi duniya a halin yanzu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: ‘Yan mulkin mallakan duniya sun raba duniya zuwa gida biyu; wato azzalumai da wadanda ake zalunta. To amma juyin juya halin Musulunci ya zo ne da koyarwar kyamar zalunci da kuma nesantar zaluntar sauran mutane. Hakan ne ya sanya sakon juyin bai takaita kawai ga cikin gidan Iran ba, sannan kuma al’ummomin duniya sun yi maraba da shi.

Jagoran ya bayyana cewar azzalumai da hukumomin da suke da alaka da su da kuma masu wadanta da dukiyar duniya suna daga cikin masu adawa da sakon wannan juyi na Musulunci na al’ummar Iran inda ya ce: ‘Yan mulkin mallaka suna gudanar da siyasar ‘rura wutar yaki’, yada talauci a tsakanin al’umma da kuma fasadi, wanda Musulunci yana adawa da dukkanin wadannan siyasar. Wannan adawar ita ce tushen rikicin da ke tsakanin su da juyin juya halin Musulunci.

Yayin da ya ke magana kan makaman kare dangi da kuma adawa da hakan da Iran take yi, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Mu dai ba wai saboda Amurka ko wanin Amurka ne ya sanya muke kyamar makaman kare dangi ba, face dai sai don saboda imani da akidar da muka rika. A yayin da muke cewa bai kamata wani ya mallaki makaman kare dangi ba, ko shakka babu mu kanmu ba za mu yi kokarin mallaka ba. Don haka ne manufar masu adawa da Iran, wata manufa ce ta daban.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wadannan ‘yan tsirarun kasashe da suke tada jijiyoyin wuya, ba wai saboda wannan lamari ne suke tada jijiyoyin wuyan ba. A saboda haka wajibi ne a kalli ihu bayan harin da Amurka da kasashen yammaci da ‘yan amshin shatansu suke yi dangane da batun shirin nukiliyan (Iran) karkashin wannan rikici mai girma da ke tsayin juyin juya halin Musulunci da ‘yan mulkin mallakan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Irin girman da marigayi Imam Khumaini (r.a) yake da ita, ta  sanya hatta makiya suna girmama shi. To amma a fagen kiyayya kan babu wani mutum da suke kiyayya da shi kamar Imam, don kuwa Imam ya fahimci hakikanin manufar da suka sa a gaba, sannan kuma haka ya tsaya kyam tamkar wani dutse a gabansu wajen hana su cimma wadannan manufofin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yau ma haka lamarin yake. Duk wanda ya yi riko da asalin koyarwar juyin nan sannan kuma yake ganin makirce-makirce da halayen makiya karkashin wannan rikicin da ke tsakanin ‘yan mulkin mallaka da wannan juyi na Musulunci, to kuwa ma’abota girman kai za su yi adawa da shi.

Yayin da yake magana kan tsarin diplomasiyya da ke gudana a duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Fagen diplomasiyya dai wani fage ne na sakin fuska da bukatar tattaunawa. To amma wajibi ne a kalli wannan fagen da irin wannan kallo na kalubale na asali. Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai ya bayyana cewar shi ba ya adawa da yunkuri na diplomasiyya da kuma tattaunawa, to amma wajibi ne hakan ya zamanto karkashin koyarwar da aka rika.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin gagarumin ci gaban da Iran ta samu a fagage na ilimi, ayyukan soji, gudanarwa, tattalin arziki da sauransu wanda ya ce Iran ta samu hakan ne kuwa duk da irin takunkumi da matsin lambar da makiya suke mata. Jagoran ya ce hakan wani lamari ne da ke nuni da cewa babu wani da ya isa ya hana al’ummar Iran ci gaba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Irin matsaloli da hasarorin da duniyar musulmi ta fuskanta sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a yankin nan, ya samo asali ne daga jahilcin wasu da kuma kin amincewa da hakan, duk kuwa da cewa hakan ba abu ne da zai ci gaba da wanzuwa ba. Ko shakka babu farkawa ta Musulunci da aka samu za ta yi nata aikin.

Tun da fari dai sai da Hujjatul Islam wal muslimin Sa’idi, wakilin Jagoran a hukumar dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da jawabi da kuma rahoto kan irin ayyukan da cibiyar Jagoran take gudanarwa a tsakanin dakarun kare juyin.

Har ila yau babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Ali Ja’afari shi ma ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyuka da nasarorin da dakarun kare juyin suka samu. Janar Ja’afari ya ce a halin yanzu dai dakarun kare juyin suna cikin dukkanin shirin da ya kamata wajen kare juyin juya halin Musulunci, koyarwar marigayi Imam Khumaini da tafarkin shahidai daga duk wata barazana ta makiya.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook