A+ R A-
25 May 2020

Jagora: Amurka Ba Abar Yarda Ba Ce/Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Kaushi Ga Wanda Ya Kawo Mata Hari

A safiyar yau Asabar (5-10-2013) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci bikin yaye daliban jami'oin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran karo na bakwai da aka gudanar a Jami'ar Sojin Sama ta Shahid Sattari da ke birnin Tehran.

An fara gudanar da bikin ne dai da ziyarar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kai makabartar shahidan soji da ke jami'ar inda ya karanta musu Fatiha da kuma nema musu karin daraja da matsayi a wajen Allah Madaukakin Sarki.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan bikin, Ayatullah Khamenei ya bayyana shiga cikin jerin jaruman dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin wani abin alfahari ga wadannan matasa da suka gama karatun na su. Haka nan kuma yayin da ya ke jaddada musu wajibcin ci gaba da zama cikin shiri da kuma karfafa irin karfi na tsaron kasa da kuma hadin kai tsakanin al'umma da ake da shi, Jagoran cewa ya yi: mu dai muna goyon bayan tafarkin diplomasiyya da gwamnatin (Iran) take gudanarwa ciki kuwa har da ziyarar da shugaban kasa ya kai birnin New York (don halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya), don kuwa mun yarda da wannan gwamnatin ma'abociyar hidima ga al'umma kuma muna da kyakkyawan fata dangane da ita, to amma wasu abubuwan da aka yi a yayin wannan ziyarar ta New York wasu abubuwa ne da ba su dace ba. Don kuwa gwamnatin Amurka ba abar yarda ba ce, gwamnati ce maras hikima sannan kuma mai karya alkawari.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Mu dai mun yarda da jami'anmu, don haka bukatarmu a gare su ita ce su kalli dukkanin bangarori yayin da za su dau wani mataki, sannan kuma kada su mance da manufofi na kasa.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan wajibcin tabbatar da irin karfi na cikin gida da ake da shi, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Abin ya kare juyin juya halin Musulunci tun farko-farkon nasararsa da kuma al'ummar Iran, bugu da kari kan samar musu da ci gaba, shi ne irin muhimmancin da ake ba wa koyarwa da manyan manufofin tsarin Musulunci da kuma daukaka ta kasa. A saboda haka nauyin da ke wuyan dukkanin jami'an gwamnatin da sauran al'umma shi ne ba da kariya ga mutumci da kuma daukaka ta kasa.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin kallon rashin aminci da yarda da gwamnatin Musulunci ta Iran take yi wa Amurka, Jagoran ya bayyana gwamnatin Amurka a matsayin ‘yar amshin shatan sahyoniyawa yana mai cewa: Ko shakka babu siyasar gwamnatin Amurka siyasa ce ta goyon baya da tabbatar da manufofin sahyoniyawa. Amurka tana dagawa ga (kasashen) duniya, amma kuma tana mika kai ga gwamnatin sahyoniyawa.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da cewa al'ummar Iran ba su taba yin barazana ga wata kasa ba, amma karfin da sojojin kasar Iran suke da shi wani lamari ne mai muhimmancin gaske wajen kiyaye tsaro da zaman lafiyan tsarin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Wajibi ne dukkanin dakarun kasa da suka hada da sojoji, dakarun kare juyin juya halin Musulunci, dakarun sa kai na Basij da jami'an ‘yan sanda su kasance wata garkuwa mai karfi wajen tinkarar makirce-makircen makiya.

Babban kwamandan dakarun kasar ta Iran ya ja kunnen makiya al'ummar Iran da suke ci gaba da yi mata barazana da cewa: Wajibi ne dukkanin wadanda suka saba yi wa al'ummar Iran barazana su san cewa martanin da za mu mayar ga duk wani wuce gona da iri kan al'ummar Iran, wani martani ne mai kaushin gaske.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Al'ummar Iran sun tabbatar wa da duniya irin tsayin dakansu wajen kare koyarwar da suka rika da kuma manufofin da suka sa a gaba, kamar yadda kuma suka tabbatar da irin fatan da suke da shi na sulhu da zama lafiya, don kuwa wadannan wasu abubuwa ne da suke tafiya tare da junansu.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jinjinawa irin sadaukarwar da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, musamman sojojin sama, suka yi a lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas (da kasar Iraki ta kallafawa Iran), kamar yadda kuma ya jinjinawa shahidan kallafaffen yakin irin su Shahid Babayi da Sattari.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da babban hafsan hafsoshin sojin sama na Iran Admiral Hasan Shah Safi ya gabatar da jawabin barka da zuwa ga Jagoran inda ya bayyana cewar: baya ga horarwa ta soji da ake koyarwa a jami'ar sojin ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, har ila yau kuma ana karantar da daliban ilmummuka na addini.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin nasarorin da sojojin suka samu a jami'ar, babban hafsan hafsoshin sojojin saman na Iran cewa ya yi: sakamakon karfafa irin karfin da suke da shi na kariya, sojojin saman na Iran suna cikin dukkanin shirin da ya kamata wajen ba da kariya ga kan iyakokin kasar Iran ta sama.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban jami'ar sojin sama ta Shahid Sattarin Rear Admiral Bakhshande ya gabatar da rahoto kan irin ayyuka da horarwar da ake ba wa jami'an sojin a wannan jami'ar.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da lambar girma bugu da kari kan Alkur'ani mai girma ga kwamandoji, malamai, matuka jiragen sama, wasu daga cikin iyalan shahidai da kuma wasu daga cikin daliban da suka gama karatun na su. Sannan kuma sojojin sun gudanar da faretin ban girma da kuma nuna wasu daga cikin kwarewar da suka samu.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei www.khamenei.ir

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook